Page 53

4.5K 238 17
                                    

Zuhraa❤❤
        (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
         ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 53

Suna isa ya yanka mata kati ba mutane sossai so direct suka wuce office d'in doctor da larabci Aliyu ya fara mishi bayanin abunda ke damunta tambayoyi ya fara mata cikin harshen turanci tana bashi amsa kwalba ya bata wai tayi fitsari a ciki Aliyu ya taimaka mata tayo suka dawo suka bashi sossai take rawan d'ari a haka doctorn ya d'ibi jininta ya kira nurse ya bata tare da mata bayanin abunda zatayi da shi........

Amsa tayi ta fita, shi kuma ya tsaya kallon soyayyar wa'yannan ma'aurata yana murmushi se lalla'ba ta yake yi ita kuma tana kara shagwa'bewa har da hawaye shima Aliyu ma ji yake kamar ya cire ciwon ya dawo jikinsa.......

Chan nurse d'in ta dawo da result d'in test d'in doctorn ya kar'ba tare da mata godiya tayi ficewarta bud'ewa yayi ya karanta murmushi kwance a fuskanshi ya dubi Aliyu yace cikin harshen larabci "congratulations you are gonna be a father" waro ido Aliyu yayi in shock he was like what!!!......

A take ya zube a kasa yayi sujudu shukuru ya kai minti biyu a haka yana kwararawa Allah godiya tukun ya mike ya d'auke ta chak yana juyi da ita cikin tsantsan farin ciki ajiye ta yayi tare da rungume ta kam kam a jikinshi yana furta "thank yhu baby, thank you, thank you fateemah I love you so much"........

Da tsantsar mamaki zuhraa ke kallonshi ta san yana son yara amma bata zata son yaran nashi ya kai haka ba zata iya cewa bata ta'ba ganin shi cikin farin ciki ba sam ya rasa inda ze sa kanshi tsabar farin ciki kafin tayi aune ya had'a bakinta da nashi passionate kiss yake bata irin wadda be ta'ba mata ba a rayuwa, ajiyan zuciya kawai take saukewa don ma Allah ya taimaka doctorn baya office d'in....

Tun da yaga Aliyu yayi sama da ita yana murna ya zame ya shige wani kofa a gefenshi tana zaton toilet ne, se da ya gama murnanshi tukun ya kyale ta suka zauna hannunshi na cikin nata bakinshi kuwa yaki rufuwa, se da doctorn yaji shiru tukun ya fito yana murmushi Aliyu ma murmushi ya mayar mishi yace "na gode kwarai da wannan Albishir naka" da larabci yayi maganan........

Murmushi kawai doctorn yayi ya zauna tare da yima Aliyu bayanin yadda ze kula da ita natsuwa kuwa yayi yana ji bayan nan doctorn ya fad'a mishi cikin na wata uku ne tunda bata amai baze bata magani ba in sun je gida se su samu specific asibiti su ringa zuwa awo.......

Kyauta me tsoka Aliyu ya mishi ya ki kar'ba se da Aliyu ya ce mishi "ihsani ne wlh da niyar kyauta ya bashi ba don wani abu ba ne" godiya sossai ya mishi suka fice a cikin taxi se tamabayn ta yake me zata ci? Me take so? Se de ta girgiza mishi kai.....

She's out of word bata san me zata ce ba bata san wani irin farin ciki zatayi ba har suka isa bata ce komai ba suna shiga ta wuce toilet ta sake ruwa tare da fashe wa da kuka, Shikuwa ya d'auka uzurinta ta shiga yi se ya d'auki waya ya kira maami ya mata Albishir hk Ammie ma su kuma suna tare da mazensu suka fad'a musu abin farin cikin da ya same su........

Maami kam mamaki yaki sake ta a fili tace "ikon Allah habeebi kaga iko na ubangiji ko? Shekaru dayawa da aure na ban samu haihuwa ba amma kaga 'yata wata biyar kacal amma ta samu karuwa" murmushi Abba yayi tare da jawo ta jikinshi yace "haka Allah ke abunshi Allah ya sauke ta lafiya" ta amsa da Ameen........

*****

ta kai 30mins kafin ta fito ido ya zuba mata be ce komai ba har tazo ta zauna kusa da shi mikewa yayi ya tsugunna a gabanta yace cikin sanyin murya "zuhraaa!!!" Zata iya rantsewa bata ta'ba ji ya kira ta da suna Zuhraa ba se yau kuma sunan ya mata daad'i sossai da ya fito daga bakinshi kallonshi tayi da jajayen idanunta ba tare da tace komai ba...... 

Zuhraa❤❤Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt