Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 26
Tana fita ta tsaya nesa da shi tana kuka shi kuwa baki ya washe yana dariya tare da cewa "amaryata, ran juma'a war haka kin zama nawa, kin san kuwa me zan miki ranan?" Tsaki taja tukun tace "ibi me yasa baza ka gane ba, bana sonka kuma in shaa Allahu bazan aure ka ba" wani irin d'an iskan dariya ya sake yace "ko baki aure ni ba se na lashi zumanki, kai ma don kutu..... Innar ki se na aure ki, ke koda tsohon ki ne ya dawo daga lahira... Kan ya karasa ta wanka mishi mari...
"Karamin d'an iska kawai wlh kayi karya ka ta'ba baffa na in kyale ka, kayi kad'an shashasha" dariya yayi yace "hmm zuhraa kina cin bashin da yafi karfin ki, mari na uku kenan kike min kuma wallahi se kin biya marukanan" yaja tsaki ya juya ya fice, kukanta taci ta koshi kafin ta shiga gidansu shatu da gidado suka ci karo ya ce "ya de lafiya kuwa?" Tace "na shiga uku hamma inna zata aura wa ibi ni, wai kuma ranan juma'a"..
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci gidado yace "dan Allah da gaske kike?" Tace "wallahi kuwa" yace "zo mu karasa ciki baba na nan, bama ze yiwu ba ne waye be san ibi d'an iska bane" gidan suka karasa shiga hawaye na ci gaba da gangara a idonta "Salamu aliakum" inji fad'ar gidado, chubado ce ta amsa "wa'alaikassalam a'a har kaje aikan baban naka ne"...
Yace "a'a inna wani matsala ne ya taso mana" zatayi magana kenan taga zuhraa a bayanshi tana kuka "subhanallah zuhraa me ya same ki? Me ya faru" shatu da baba ne suka fito suna cewa me ya faru, gidado ya ce cikin takaici "wai hanse ce zata aura wa ibi ita ranan juma'a" a tare suka ce "innalillahi wa'innailaihi raji'un" baba ya kara da "baze yiwu ba, malam buba amini na ne shakiki, bamu yi wani maganan auren zuhraa da shi ba kafin rasuwar shi, kuma ko da munyi bazan taba yadda ya aura mata ibi ba, ballantana nasan ko shi ne baze amince ba"..
Chubado tace "wannan wani irin masifa ne? Ko fa kwana goma ba'a rufa da rasuwar shi ba" shatu kam kawarta take taya kuka gidado yace "baba toh yanxu me abun yi?" Baba yace "muje wurin mai gari, muji shi me ze iya cewa"...
Zuhraa a zuciyar ta tana adu'an Allah yasa a dace don tasan halin inna idan tana son Abu ko ta wani hali se ta same shi. Ficewa sukayi ita kuma tace "bari in shiga gida chubado kar ta neme ni bata ganni ba abun ya zama matsala" chubado tace "toh amma fa ki kwantar da hankalinki ba abunda ze faru in shaa Allahu" tace "Allah yasa" tare da ficewa daga gidan...
A chan gurin mai gari kuwa bayan sun kwashi gaisuwa suka fad'a mishi abunda ya kawosu mai gari yayi gyaran murya tare da cewa "toh ita zuhraan ce tace auren dole za'ayi mata?" Gidado yace "eh" mai gari yace "kar ku damu in har bata so baza a mata dole ba, zan aika a kira min Hansen inji daga bakinta" suka ce "toh godiya muke ranka shi dade" tare da mikewa su fice"..
Wani daga cikin 'yan fada ne ya sulale yaje ya kai ma ibi rahoto shi kuma ya samu mahaifinshi da maganar dama mahaifinshi ke daure mishi gindi yake abunda yake so a garin, ai kuwa duhu nayi Alhaji manga mahaifin ibi ya d'ibi shanukai guda uku ya nufi gidan mai gari dashi, iso aka yi mishi har ciki, ni kuwa hanani shiga sukayi...
Ban san me suka tattauna ba, naga de mai gari na ta godiya kaman yayi wa Alhaji mangan sujada, ya kuma bada umarnin a shige mishi da shanukan, Alhaji manga kuwa ya wuce yana murmushin samun nasara..
%%%%%%%%%%%%%%%
Wata hamshakiyar mata, doguwa sam bata da kiba se de kuma baza'a kira ta siririya ba, chocolate color ce fatan nan a murje sbd hutu da ya zauna mata, saukowa take daga stairs a natse tana waya...
![](https://img.wattpad.com/cover/197479788-288-k522853.jpg)