Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 23
Kid'a ne ke tashi a club d'in, maza da mata ko wacce tayi shigar banza, wasu na shaye shaye wasu na rawa, wasu kuma suna iskancinsu a cikin jama'a, khaih duniya ina zaki damu?..
Ayush ce da click d'inta suka shigo gurin cikin iyayi da yanga ihu aka dauka, ana kiran sunanta, ita kuma yatsina fuska kawai take tana d'aga musu hannu, wakar data fi so aka sa mata, haweya stage tayi ta fara wani irin rawa kamar mazari...
Se da tayi rawa ta gaji tukun ta koma wurin zaman su na mussaman da ba wadda ya isa ya zauna a gurin rukky kawai ta samu a gurin zama tayi rukky ta zuba mata wine ta dauka ta kurba tukun tace..
"Rukks ina su Afrey ne?" Rukks tace "lubcy da zee sun shige daga ciki da new catch d'in da sukayi, Afrey kuma ta fita karbo sabbin kayan harkar da tayi order yanzu zaki ganta" kai kawai Ayush ta d'aga ta d'an kishingid'a..
Hamzy ne saurayin Ayush ya karaso gurin ya d'an duka yayi pecking d'in forehead d'inta yace "yane babe na d'ibo zafi d'an zo mana mu shige daga ciki" kwa'be fuska tayi tare da zuba mishi harara tace "ka san Allah daga yau har wani satin ban jin yin komai, in kana so kaje ka samu wata ehe"..
Da mamaki yake kallon ta da kyar ya bud'i baki yace "yanxu ke bakya kishi na?" Tace "tab wai in tambaye ka sonka nakeyi ne da zanyi kishin ka? Ka jimin d'an rainin hankali" a zuciye yace "wato don ina biye miki ne kike min wulakanci ko? Wai tukkuna ma me kike ji dashi ne? Banza, shashasha, karuwa kawai, bari ni hamza daga yau na fita har karki, kar ki kuskura ki kara nema na 'yar iska k....
Kafin ya karasa abunda yake son fad'a yaji saukan kwalba a goshinshi da sauri ya dafe goshin yana kallonta yana huci jini har ya fara wanke mishi fuska yaji tana cewa "wlh kayi karya ka zage ni in barka, ubanka ma yayi kad'an bare kai, wato don na baka jiki na shine raini ya shigo tsakanin mu ko? Toh bari ka ji in gayamaka idan har ka sake had'a hanya dani sena jawa ubanka zaman gidan yari, bare ka kalle ni har mu had'a ido, d'an iska kawai" ta tofar mishi da yau a fuska tare da jan tsaki ta koma tayi zamanta...
Yunkuri yayi ya nufi kanta da sauri abokanshi suka jashi suka fice dashi daga gurin yana ta zage zage, d'an dafe kanta tayi Afrey da ta shigo gurin tun fara fad'ar su tace "babe Anya lafiyanki kuwa?" Rukky tace "tayani tambaya ni wlh duk kwanan nan ban san me ke damunta ba"..
A hankali hawaye ya gangaro a fuskan ta, da mugun mamaki suke kallonta don zasu ce basu ta'ba ganin hawayenta ba karasawa kujeranta sukayi ko wacce ta zauna a hannun kujerar a tare suka ce "Ayush me ya faru?" A hankali tace "babes son Aliyu ze yi ajalina, ban san ya zanyi ba, ku taimake ni plz" ta fashe musu da kuka..
Kamata sukayi suka fice daga gurin a motar ta suka saka ta rukky taja yayin da Afrey ta shiga baya da ita mintuna 10 ya kawo su gidanta, a chan cikin bedroom d'inta suka yada zango hayewa gadonta gabad'aya sukayi Afrey ta kwantar da kanta akan cinyar ta har zuwa lokacin kuma bata dena hawaye ba..
Rukky ce tace cikin takaici tace "wai Aisha wannan wani irin soyayya ne?" Afrey ce ta katse ta "haba rukks ya za'ayi tana cikin tension you didn't find her a solution se kokarin kara mata kike?" Rukky tace "ba haka bne ai tun farko na bata shawara tazo muje gun boka na kan dutse a jos tace ba hk ba, so ya take son inyi da ita?"
Da sauri Ayush ta mike ta zauna tace "rukky wallahi yanzu kam na yarda, zan iya yin komai dan in mallaki Aliyu, wai baku ga wulakancin dayake min bane wlh yana kona min zuciya, rukky yaushe zamuje in yi mana booking flight" rukky tace kiyi mana booking din na monday, ran Tuesday se muje gurin shi kiga aiki da cikawa"...
%%%%%%%%%%%%%%%%%
"Salamu alaikum" Abba da baffa suka fad'a a tare suna shiga parlorn maami, ita da Aliyu ne suka amsa a tare Abba murmushi yayi tare da cewa "A'a major maami ta ji sauki an fara makale mata kenan"? Murmushi kawai Aliyu yayi, yanzu base yayi magana ba me kar'ba mishi zance ta samu lfy...
Aikuwa maami tayi charab tace "haba Alhaji yaro da mahaifiyarshi se a hana shi sakewa" yana dariya yace "Toh fah me kar'bawa sadaukinta fad'a ta dawo" ita ma dariya tayi tana shafa kan Aliyu dake zaune a kasan kujeran datake tace "Uhmm fad'a da ihu" duk dariya sukayi har baffa banda Aliyu da murmushi kawai yake yi...
"Aaa malam ashe kaine tafe ja'bbama lale sannu e warugo"(maraba sannu da zuwa) inji fad'an maami, baffa na murmushi yace "yauwa mi ja'bi, ya karfin jiki?" Tace "Alhamdulillah Kaga baki ya bud'e hannun ma yanzu da yammanan naga ya fara functioning"..
Abba ya yi murmushin farin ciki yace "masha Allah, Allah mun gode ma" baffa ma murmushin yayi yace "masha Allah tabbas Allah shine abun godiya, so se ku kira Maman Aliyu in mata bayanin wa'yannan magani don gobe in shaa Allahu zan wuce da safe"..
Abba yace "toh" tare da fitar da wayarshi ya kira Abbie yace "yaya ku karaso part d'in maamin Aliyu, malam ya zo" amsa mishi akai a d'ayan bangaren, basu fi 5mins ba suka shigo da sallama, aka d'an gaggaisa tukun Baffa yayi wa Ammie baya nan magungunan...
Yana gama mata suka mike suka fice gabad'aya mazan sbd kiran isha da akayi a massallaci suka bar Ammi da maami suna hiran su na kawaye, salma, salma daga d'aki tace "na'am Adda ina zuwa" ta fito ta zauna a kan one siter tace "gani" maami tace "wai me ke damunki ne kwanan nan kullum kina d'aki kina aikin waya, tukuna ma da wa kike waya"..
Tace "Adda zaid ne fa abokin hamma" maami tace "masha Allah shine surkin namu kenan, toh gaskiya ban son yawan wayan nan a rage" tace "toh" Ammie tace "toh ma in suna son junansu ya fito mana kawai ayi auren, ki ce mishi ya turo" rufe ido salma tayi tana dariya zata shige d'aki, maami tace "bafa kiran ba kenan, ki shiryo ma su Abbie d'inku abinci maza" tace toh tare da nufar kitchen...
Suna dawowa daga sallah suka nufi dining maami da Ammie duk ba wadda ya motsa dga inda suka bar su, Abba joining d'insu yayi Abbie dake kan dining yace "ya de Muhammad ka zauna a can" maami ma kallonshi take da alamun tambaya, murmushi yayi yace "hajiya abar harara na 'yarki ce ta cika min ciki da fura me d'adi ai kunyi missing"..
Ammie tace "wa kenan?" Yace "zuhraa" Abbie yace "amma wannan son kai ne, dama kai kaje dauko malam shine ko gayyata babu?" Dariya Abba yasa yace "yayah Anya kai dauko malam kake wa haka ko fura" dariya dukkansu suka saka har Abbien..
Baffa yace "kar ka damu Alhaji in de kindirmo ne na kawo muku me kyau da gard'i yana mota" Abbie yace "masha Allah mun gode malam" ya juya ga Abba yace "da baffa be kawo ba da se ka nemo min fura da daren nan na gayama" dariya suka sake sawa..
¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶
Yau sunday a yau Aliyu ya koma wurin aikin shi, kuma a yau da dare su rukky suka d'aga zuwa garin jos cikin farin ciki da jin d'adi, sun isa lafiya, gidan su rukky suka yada zango tarba me kyau aka musu don rukky ita kad'ai ce 'yar su mace tana da yaya namiji da kani d'aya....
Sossai babanta ke ji da ita so duk abunda rukky zatayi ba'a ko'bar ta, abunda take so shi za'ayi, wannan ne karo na farko da Ayush tazo gidansu amma rukky kam taje gidansu Ayush yafi a kirga, cikin zuciyar Ayush take ayyanawa Ashe rukky ma 'yar gata ce ba laifi suna da arziki duk da basu kai na mahaifinta ba...
Washegari
Cikin shiri suka fito yadda suka saba shigansu kaman 'ya'yan arna, wando jeans blue Ayush tasa da farin crop top aka gyara Gashin dokin nan har tsakiyan baya, rukky kuma tasa half gown da ko rabin cinyar ta be kai ba, driver dinta ta dauka dayake shi yasan gurin bokan...
Suka d'auki hanya, tafiya yaki ci yaki cinyewa har Ayush ta fara mita, daji sossai suka nausa bayan sun isa kauyen a can cikin dajin sunyi tafiya na kusan 1 hour kafin yayi parking, suka sauka a kafa suka sake fara sabon tafiya...
•toh fah, ku biyo ni kuji ya zata kaya•
#vote
#share
#comment'Yar mutan Adamawa