Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 45
Bayan sati uku
Shirye shirye ake yi sossai na waliman da za'ayi duk da walima ce kad'ai amma gidan ba masaka tsinke a ciki yake da 'yan katsina da 'yan ribadu se sisters din Ammie da suka zowa maami waliman sbd komai ya tashi a danginsu har kasar su take zuwa suma dole su zo mata, Anty salma ma a gidan take yini se dare zaid ze d'auke, tunda Aliyu ya koma za'a iya cewa sati uku kenan be zo ba ko sau d'aya.....
Zaid da yaji batun kiran Aliyu yayi a waya ya mishi tatas wai wato be d'auke shi aboki ba ace yana da aure har na wasu shekaru ya kasa fad'a mishi yana matsayin aminin shi, se yanzu yasan be d'auke shi yadda shi ya d'auke shi ba tunda shi be iya boye mishi damuwan shi ko farin cikinshi.........
Da kyar Aliyu ya shawo kan zaid ya hakura duk da zaid ba me fushi bnae amma ranshi ya baci, ba'a wani jima ba suka shirya se kuma ya dasa da tsokanan Aliyun, idan suka fara waya cikin farin ciki toh ba'a kare shi haka se Aliyu ya hau ya mishi tatass ko kuma wani lokacin shiru ze yi se zaid d'in ya gama tsokanan shi se ya kashe wayan ba tare da yace komai ba.......
Abunda zaid ya lura Aliyu na ma zuhraa mahaukacin so, me wiyar fassaruwa sbd duk lokacin da zaid ya mishi wasa da danganta zuhraa da wani namijin yakan ce 'da wani ya maka kwace don kyaunta' ko kuma yace 'yanzu na ga zuhraa da saurayinta muka gaisa' ko kuma 'idan kayi sake da yarinyar nan ko ni se in d'auke' tou fa zasu kwana biyu Aliyu be d'aukan wayanshi da kyar ze shawo kanshi a chan kuma duk fushin shi kan sojojin shi yake karewa............
Duk da zaid na tausayin abokinshi sbd be iya son abu ba don ma ya lura zuhraa yarinya ce natsatsiya baza ta ta'ba wahalar mishi da aboki ba sbd yana tsoro in taga son da yake mata ta yi amfani dashi wurin juya shi son ranta, amma kuma yana ga Allah ya kama shi da son zuhraa ne sbd wulakancin da Aliyu ke yiwa mata......
Ba wai haka kawai ze miki wulakanci ba shi asali ma Allah ya d'aura mishi tausayin mace a ranshi ba kad'an ba tashin hankalinshi ya ga mace na kuka, amma fa banda wacce ta furta mishi kalmar so ko kukan jini zatayi ze iya taka ta da mota yayi tafiyarshi ya tsani yaji mace ta ce tana sonshi wulakancin da ze mata kare ma baze ci ba, gwara ki ta kallonshi daga nesa duk da kallon ma ya tsana, tun suna cyprus ma kenan da suka dawo nja kuma se abun yayi worst......
A rana se mata sama da biyar sun bi Aliyu da kalmar soyayya haka ze miki tatass ya fattattake ki wani lokacin ma se yasa sojojinshi shi kora ki a wulakance, Zaid ba karamin sani yayi wa Aliyu ba duk da sossai yake boye son nata amma be hana zaid ganewa ba, bafa wai magananta yake yawan yi ba shi ze iya cewa be ta'ba jin Aliyu ya kira sunanta ba amma se da zaid ya gane son da yake mata.........
********
Kwance take kan gadon maami ba kowa a d'akin sbd maami na part d'in Ammie Nasreen da ilham kuma sun fita, ita an hana ta fita tun last three weeks ko kasa bata cika saukowa ba, game take yi a wayar ta amma zuciyar ta fall da tunanin shi sati uku bata sanya shi a idonta ba bata kara jin muryarshi ba fita tayi a game d'in ta lalu'bo hotunshi ta zura wa fuskanshi ido.........
A hoton sanye yake da k'akinsu na sojoji gashin kan nan ya sha gyara fuskan nan a had'e kaman an auko mishi da sakon mutuwa sajenshi daya kwanta a fuskanshi zuwa gemunshi d'an dai-dai na 'yan zamani be wuce kamu d'aya ba ya kawata fuskan nashi sossai yake da kyau blue eyes d'inshi ta Kalla murmushi ya subuce mata tana mamakin yadda yake Kanne idon ya maida shi kanana amma idan ya zaro su kaman kantin ball......