Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 11
Washegari da safe bayan zuhra ta gama duk abunda ta saba tayi wa su hassan wanka ta shirya su suka tafi makaranta, domin ita kam baza ta iya zuwa school ba, ta kaima baffa ruwan wankanshi ta zo tayi sallama kofan d'akin shi ya amsa mata ta shiga "baffa 'yan ummi jam"(mun tashi lfy?) Ya ce "jam dada am noi bandu ma"? (Lfy klau mama na ya jikinki) tace "lfy klau da sauki" ta kara da cewa "na kai maka ruwan wanka ga kuma abun kari nan" yayi murmushi don ya san so take yayi sauri su zo suyi magana ya ce "usoko mi yetti" ta mike ta fita, taje kofan inna tana sallama ba'a amsa mata ba, a lokacin baffa ya fito daga d'akinshi yace mata "innanku bata nan" se a lokacin ta gane me ya faru sam bata ji dad'i ba sbd ko ba komai ita ta raine ta amatsayin mahaifiyar ta take, kuma ai gsky ta fad'a.
Se da suka karya suka suka kimtsa tukunna suka zauna a nutse baffa ya fara bata labarin abunda ya faru a lokacin har tayi wayau da abunda yasa inna ta tsane ta,
Tunda ya fara bata labarin take kuka har ya gama, ya daura mata da nasiha me ratsa jiki da kyar ta budi baki tace "baffa kayan da aka tsince ni dashi fa"? Mikewa yayi ya je ya dauko mata, karba tayi ta rungume a jikinta tana kara sakin wani sabon kuka tare da jin kaunar kayan da kewar mahaifiyar ta na ratsa ta.
Seda baffa ya bari ta gama kukanta tukun ya kara mata nasiha, ya mike ze tafi kenan tace "baffa dan Allah ina neman wata Alfarma a gurinka" yace "toh Allah yasa be fi karfi na ba" tace "dan Allah baffa ka mayar da inna ban ga laifinta ba gaskiya ta fada, sannan kuma hakan da kayi baze sa ta soni ba sede ta kara tsana ta, ni de ina sonta a matsayin mahaifiya kuma in shaa Allahu baze chanza ba, na riga na yafe mata duk abunda tamin tun daga yarantata har girmata har ma nan gaba" baffa yayi murmushi yace "toh mamana zan dawo da ita in shaa Allahu Allah yayi miki albarka" tayi mishi murmushi tare da cewa "ameen" ta mike ta shige d'aki ta adana kayanta ta fito ta zauna tana tunani, bata fita ba don tasan shatu na school.%%%%%%%%%%%%%%%
Bayan Ammie ta gama bashi abinci, ya mike ya fita, a kafa ya nufi gidansu zaid, yana shiga daga gate ya same shi zaune da me gadinsu suna hira da dariya, shifa rayuwar zaid burgeshi yake yi so simple, ga hayaniya kwata kwata be damunshi, shifa mamakin abokantakar su da zaid yake sam halinsu ba daya ba.
Karasawa yayi ya mika masu hannu tare da sallama, da sauri me gadin ya tsugunna da sauri Aliyu ya duka ya kamashi ya daga yana cewa "haba baba ai in ban tsuguna maka ba be kamata ka tsugunna min ba, zafa kayi sa'an Abbie" da sauri me gadin ya mike don yasan da wuya Aliyu ya kara wani maganan, wato in baka gane halin aliyu ba zaka dauka me girman kai ne amma in ka fahimce shi yana da mugun saukin hali da tausayi.
Zama Aliyu yayi a gefensu yana cewa "sorry dude" girgiza kai zaid yayi yana cewa "ya na iya da kai" murmushi kawai Aliyu yayi ya dauko waya ya fara aikin dannawa, kyaleshi zaid yayi ya juya suka ci gaba da hira da baba me gadi, a cikin hiran nasu me gadi ke tambayar zaid "ya ko jikin maamin Aliyu kuwa?" Zaid ke cewa "baba ai se adu'a maami kam magani kasashe d'add'aya ba'a je ba abun yaci tura, wadda suka je ne na karshe likitan yace su gwada na musulunci watakila a yi dace" baba me gadi yace "ni ko da ba don ku baku bada wani himma akan maganin gargajiya da musulunci ba da se in ce akwai wani me magani a garinmu ya kware ta wannan fannin, Kaga akwai wata kanwata da tayi irin wannan ciwon sede ita na watanni ne, da muka gwada kuma alhamdulillah an samu waraka" kafin zaid yayi mgna da sauri Aliyu da ke saurarensu ya kar'be maganan yace "baba a wani gari ne?"
Baban yace "a Gurin yake" Aliyunne ya kara magana "baba kama zaid kwatance yadda zamu gane gobe in shaa Allahu zamu je mu dauko shi" zaid ne ya kara da "Kaga baze yiwu mu tafi da ita ba daukon shin zefi sauki" baba me gadi yace "toh Allah yasa ya yadda ya biyo ku" suka "ameen" dai dai lokacin aka kira sallahn magariba a massallacin estate din su Aliyu tashi sukayi suka nufi massallacin dukkansu.
Washegari da safe bayan Aliyu ya farka da misalin karfe goma yayi wanka ya shirya, ya fito ya shige part dinsu ya same su dukkansu a parlor banda Abbie da ya fita aiki, Ammie da ke zaune a three siter ta na anfani da waya, Aida ma chat take yi, yayin da afrah ke kallo, nasreen kuwa na assignment.
"Salamu alaikum" duk suka had'a baki suka amsa mai "wa'alaikassalam" ya shiga ya nufi kujerar da Ammie take tare da kwanciya ya daura kanshi a kafanta, yaran duk suka had'a baki suka ce "morning hamma" ya amsa da "lfy" a takaice ya dubi Ammie cikin larabci yace "sabahul khair ya Ammie" ta shafa kanshi tare da cewa "sabahul noor khaifa anta" ya amsa da "ana bi khair wal-hamdulillah" ya kara da cewa "Ammie me yasa baki je office ba" tace mishi "zanje ne son se anjima banda wasu patients masu yawa ne" yace "ok, zamuje Gurin ni da zaid dauko wani me magani da zai duba maami" Ammie tace "Anya kuwa Aliyu haka zamu koma kuma, kar fa garin neman gira a rasa ido, ni ban wani yadda da magungunan nan ba" ya d'an 'bata fuka yace "Ammie dan Allah let's give it a try, bamu san inda waraka take ba mu gwada mu ga" tace "toh Allah yasa a dace" yace "ameen" ta sake cewa "a kawo maka breakfast?" Gyad'a kai yayi, ta dubi arfah tace "arfah had'owa yayanku abinci" tace "ohk Ammie" ta mike ta nufi dining ta had'o abincin ta kawo ta ajiye a gabanshi ya mike ya zauna, ya fara ci a nutse, bayan ya gama karyawanne ya mike yace "am off ammie" tace "toh Allah ya tsare se kun dawo" yace "ameen" kannenshi ma suka ce "a dawo lfy" suma da ameen ya amsa musu tare da d'an murmushi ya fice, ya na fita wani soja ya karaso ya sara mishi, hannu kawai ya d'aga mishi yace "zamu d'anyi guntun tafiya, motoci uku kawai nake bukata" sojan yace "ohk sir" tare da ficewa da sauri, shashin maami ya shiga ya mata albishir din kawo mai magani, murmushi tayi mishi a yayinda hawaye ke gangarowa a fuskar ta, itama tana so Allah ya bata lfy ko don masoyanta su huta da kashe kud'i, fita yayi daga part d'in da tausayin maaminshi.
Manyan range rovers ne bakake a jere guda uku, sojoji hurhud'u ne a na gaba da baya, yayin da na tsakiya kuma guda daya driver kawai, a plate numbern din motocin an rubuta "A. A Ribadu" da manyan baki, duk sojojin basu shiga ba sun kame a gaban motocin da sauri aka bud'e mishi na tsakiyan ya shiga baya ya hakimce, a hankali suka fita daga estate din suka nufi gidansu zaid, a gate suka same shi yana hira da baba megadi, sauke glass din Aliyu yayi suka gaisa da baba megadi, zaid kuma ya zagaya aka bud'e mai ya shiga, baba yayi musu Allah ya tsare, suka fice da wani irin gudu kaman masu tashi sama.#vote
#share
#comment'Yar mutan Adamawa