Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
~~~this is for yhu sweetheart, KHADIJA DANBABA SANUSI heart you so much~~~
Page 22
Bayan sati biyu
Da sassarfa Aliyu ya shigo part d'in maami har da had'awa da d'an gudu ya haura samanta da sallama ya shiga, da wani murya me sanyi aka amsa mishi "wa'alaikassalm sadauki"..
Da gudu ya karaso ya rungume maami yana cewa "maamina kece, ashe zan sake jin muryar ki, Alhamdulillah ya Allah, ashe zan sake jin wannan sunan a bakinki" hawayen dayake dannewa ne ya gangaro mishi..
Maami se murmushi take ta d'ago shi tana cewa "Anya sadaukin da na sani ne? Me na wani kuka? Kar su Angel su shigo su ganka haka fa, ba ruwana" dariya ya saka yana share hawayenshi yace "maami hawayen murna ne wlh maami ya akayi kika fara magana"..
Murmushi tayi tace "wai ni wa ma ya fad'a mk ne, baka fa dad'e da komawa ba gashi ka dawo, kar fa ka samu mtsala a gurin aikinka" d'an shagwa'be fuska yayi yace "maami bakiyi murnar ganina ba kenan?"..
Shafa kanshi tayi tace "wa ya kai uwa murnar ganin d'anta? Na mk tambaya bk amsa ba" yace "angel ce ta fad'a min, kuma batun aiki ai yau friday kinga gobe da jibi ba aiki so weekend nazo sunday in shaa Allahu zan koma"
Maami tace "toh Allah ya kaimu ya bada sa'an aiki" yace "ameen, maami ban labari" tace "na me?" Yace "yadda akayi kika fara magana" tace "ikon Allah kenan, na tashi da asuba kawai nayi adu'an tashi daga bacci kamar yadda na saba akan labba kawai se naji murya ta ta fito, juyawa nayi na kalli abbanku..
Shima ni yake kallo cike da mamaki yace "khadija ya kaman naji muryar ki?" Nace "nima haka naji" a tare muka saka dariya matsowa yayi yana cewa "da gaske khadija kin fara magana Alhamdulillah" sujudu shukur yayi ya jima kafin ya mike yana hawaye da sauri ya fita, se gasu sun shigo gabad'ayan su har dasu Ammienku...
Sossai kowa ya nuna farincikin shi toh ban san wadda ya fad'a maka ba, ka bugo mana sammako hk karfe 9 ne fa yanzu"..
Fuskan shi na nuna tsantsar farin cikin da yake ciki ya kama kafanta yana matsawa kad'an kad'an yace "maami saura legs dinki da hands" maami tace "fingers d'ina suna motsi ai"..
Yace "Allah ya baki lafiya maddawamiya, maami let me go and fresh up in dawo in yi breakfast ina kallonki" tace "ameen okh kayi sauri kasan ba d'adi zama da yunwa"..
Mikewa yayi ya fice a parlorn kasa ya ga Anty murja sama sama suka gaisa ya fice ya nufi part d'inshi, yasan part din mahaifiyarshi ba kowa Ammie na asibiti su arfa kuma na school..
Tunda ya fita dga part d'in maami ake kiran shi a waya, ko wayan be fito dashi daga aljuhu ba, d'an karamin tsaki yaja dayaga me kiran yaki dena kira, yana karasawa d'akinshi ya cire wayoyinshi ba tare da y duba ba ya jefa kan gado ya tu'be kayan jikinshi, ya daura towel ya shige toilet..
Ya jima sossai kafin ya fito har ya fito wayan shi be dena kira ba wani tsakin ya sake ja ba tantama yanzu kam ya gane me kiran Aisha ce, be kula wayan ba ya je gaban mirror ya fara shafe shafe a natse se da ya gama tsab tukun ya nufi closet d'inshi ya shirya cikin kananan kaya...
Yana fitowa again wayan shi ya sake daukan kara dauka yayi ya amsa ya kara a kunne daga d'ayan bangaren akace "hello babe se kira nake kaki ka dauka ko laifi nayi maka?"..