Page 28

3.3K 224 6
                                    

   Zuhraa❤❤
            (The flower)   

By: fateemah muhammad gurin
        ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 28

  Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci Aliyu what!!! Shi??? Kaman shi yaji aka kira, lalu'ban Abbie ya fara yi don su had'a ido, amma Abbie ya ki yarda ya kalli inda Aliyun yake, karan loudspeakers ya cika mishi kunne da sunanshi dana zuhraa, a take kan shi ya fara juyawa idon shi yayi wani irin jaaa jijiyoyin kanshi duk sun mimmike....

Abba ne ya lura da halin da yake ciki ya mike ya nufe shi, kafin ya isa Aliyu ya daddafa ya mike, ya nufi waje yana had'a hanya a daddafe ya karasa mota yana had'a hanya, fad'awa yayi motar yace "take me home" driver d'in yaja da gudu ya bar cikin Gurin, Abba daya fito kuran motarsu kawai ya gani, girgiza kai kawai yayi ya koma ciki...

Se da mutane suka watse gabad'aya tukun Abba ya ma Abbie maganan abunda suka ji, don shima daga sama yaji abun, "yaya me kayi?" Abbie yace "aure na daura mishi, kai ma kasan ba'a wasa da aure, kuma matar shi ce ta har abada in shaa Allahu" Abba shiru yayi don shi karan kanshi abun ya mishi daad'i sede yana ga kaman ba'a ma Aliyu adalci ba, duk da sun jima suna mishi maganan yayi aure bashi ze sa a mishi auren dole ba, ko su iyayensu basu musu auren dole ba balle wannan zamani.....

Da wannan tunanin suka isa gidan me gari ibi da Alhj manga suka gani suna ta zuba rashin mutunci da sauran 'yan daban abokanshi, su Abba suna sauka sukayo kansu wai zasu dake su, sojoji 4 da suka zo da su ne suka sauko tare da har'ba bindiga sama, a take suka cikawa wandunan su iska...

Ammie da maami ne suka fito maami da sauri ta nufi gurin Abbie tace "yaya wai da gaske ne abunda mukaji?" Abbie yace "gaskiya ne khadija, shine kawai abunda zamu iya yiwa malam buba, da na shiga magana da me garin yace ba yadda za'ayi a fasa auren su, har se na samo mata wani mijin, in ba haka ba ko da su Alhj manga sun hakura yanzu toh se sun keta mata haddi daga baya, so ni a ganina me anfanin d'an da Allah ya bani tunda ina da iko da shi gwara kawai in aura mishi ita, kuma wallahi ban da niyyan rabasu aure ne da naji ya kwanta min har cikin raina, Ina ji a jikina alheri ce ita"...

Maami ta gyad'a kai a zuciyar ta, tace tabbas yaya yayi tunani me kyau, a yau ne nake jin takaicin rashin haihuwa na, tabbas da ina da yaro me shekarun Aliyu da ko yana so ko baya so se ya aure zuhraa kuma ya zauna da ita, toh Ammie fa? Juyawa tayi ta kalli Ammie da kanta ke kasa baza ka ta'ba fad'an yanayin da take ciki ba, farin ciki ko bakin ciki....

Ita kuwa Ammie tunani take ina Aliyu? Ita ta haife shi tafi kowa sanin waye shi be iya shiga tashin hankali ba yanzu se ran kowa ya 'baci, a jikinta taji ana kallon ta d'agowa tayi taga dukkansu kallonta suke d'an murmushin yake tayi tare da zagayawa ta shiga mota, tabbas taji zafin Abunda Abbie yayi sossai ita ba wai kin zuhraa take yi ba, in fact ma tayi farin cikin zamanta surkuwarta sede she has a right on her own son, ko ya ya ne ya kamata Abbie ya shawarce ta kafin ya yanke hukunci akan d'ansu....

Abbie da jikinshi yayi sanyi ganin yanayin Ammie shima ya bud'e motar ya shiga, shi yana ganin duk hukuncin da ze yanke akanta ko 'ya'yanta zata kar'beshi hannu bibbiyu kuma tayi farin ciki da hakan sam be yi zaton ganin ta haka ba, maami da Abba ma motar data kawo su suka shiga, motar su ce a gaba so maami ta ba driver umarnin kaisu gidansu zuhraa....

Suna isa maami ta sauka tare da duban sojan dake gaban motansu tace "follow me" yace "ohk ma'am" tare da balle murfin motar ya bi bayanta, kai tsaye ta shiga gidan "salamu alaikum"
Inji fad'ar maami, "munafukai, algungumai shine har da wani sallaman munafurci? Bayan munafurcin da kuka yi kuka aura wa zuhraa wadda bamu sani ba, wa ya sani ko 'yan yankan kai...... " kasa karasawa tayi ganin wani murd'add'en bakin kurtu tsaye a bayan maamin...

Dama ta san za'ayi haka daga jin labarin matar shiyasa tace sojan ya biyo ta, harara Maami ta sake mata dama maami bata da mutunci in har ka ta'bo ta, bata damu kuyi rashin mutunci ba, jainabu ta Kalla tare da cewa "ke ina zuhraa?" Jainabu ta nuna mata d'akin, kai tsaye ta shige d'akin bayan ta ba ma sojan umarnin tsayuwa daga gurin, duk macen data nemi gaya mata banzan magana ya har'be mata ita...

Tsit kake jin magulmatan matan sunyi shiru kaman ruwa ya chinye su se zare idanu suke yi, da sallama ta shiga d'akin zuhraa ta gani a ra'be a jikin bango tana kuka sossai, ita zuhraa tashin hankalin data ke ji yafi karfin na farko hamma Aliyu ina zan kaishi?  Wannan ai ya fi karfina..

Jin da tayi an ta'ba ta ne yasa ta d'an firgita a zatonta inna ce, se taga maami, mikewa tayi tare da rike maami tace "maami d'an Allah wai da gaske ne hamma Aliyu aka aura min? Na shiga uku, maami ya zanyi na san be sona to me yasa ya yadda ya aure ni?  Maami tace "natsu mana zuhraa wa ya gayamiki be son ki? Eye Abbie dinku ne ya had'a auren kuma da baffanki na raye ze fi kowa farin ciki da auren nan...

Zuhraa ta ci gaba da kukanta tana girgiza kai, maami ta jawo gyalen dogon rigar jikin zuhraan ta yafa mata, tare da jan hannunta da nufin fita daga d'akin, zuhraa tace "maami ina zuwa dan Allah akwai abunda zan dauka" cikin kuka take maganan sake ta maami tayi, nufan bakkon kayanta tayi, ta fara zubar da kayan kasa, a chan kasa taga abunda take nema, ledan kayanta da aka tsince ta dashi ne, dauka tayi ta rungume ledan tare da fashewa da wani sabon kukan...

Maami da tausayin zuhraan ya mata yawa har ta fara taya ta kukan, share hawayenta tayi ta Kama zuhraan suka fice daga gidan ba tare da ta kara kallon kowa ba, suna fita suka samu su Abbie da baba suna magana ganinsu yasa sukayi sallama baba se godiya yake musu, suka shiga mota suka fice daga garin....

**********

Ta bangaren Aliyu kuwa suna isa estate d'insu se daya shafe fiye da minti talatin a mota kafin ya sauko da kyar, duk sojojin shi suka taso suka nufo shi suna tambayan lafiya, ba wadda ya Kalla a cikinsu bare su samu amsa...

Da kyar ya karasa d'akin shi yana had'a hanya, yana shiga yaji maganan da marokan nan sukeyi yana dawo mishi kai, a take ya fara fashe kayan parlonshi, duk kayan da yasan na glass ne se da ya fasa haka ya shige d'aki ma ya dinga fashe fashe, tukun ya fad'an saman gadon shi ya dukunkune yana kiran sunan Allah,  hannunshi se jini yake zubarwa, a take zazzabi me zafi ya rufe shi...

Nasreen ne da arfa zaune a cikin garden suka ji karan fashe fashe da gudu suka nufi part din hamman nasu, se de suna shiga parlorn arfa taja tunga ta tsaya tare da kama hannun nasreen tace "sis kar ki karasa, komai ze iya faruwa kin san abunda yake yi in har yana cikin tashin hankali yanzu Ammie ce kawai zata iya tunkarar shi, muje mu kirata a waya"..

Gyad'a kai nasreen tayi tare da ficewa da gudu ta d'auki wayan ta tayi dialing number Ammie, ta bangaren Ammie lokacin suka shigo yola kiran nasreen ya shigo mata, gabanta ne ya fad'i hannunta na rawa ta d'aga kafin tayi magana taji nasreen na cewa cikin tashin hankali "Ammie kina ina hamma, hamma" kafin ta karasa ammie ta yanke wayar tare da dakawa drivern tsawa "drive fast Emanuel"..

Ai kuwa an tabo mishi ya kara wuta a dari ya wuce su maami, ganin haka yasa Abba yace wa drivern su shima yayi sauri yasan ba lafiya ba tunda yayanshi ya yadda ake gudu dashi haka, kuma yasan sunyi akan suna shiga yola gidan baba na yola "mahaifinsu" suka yi zasuje.....

Suna shiga estate d'in da sauri Ammie ta sauka ta nufi part d'in Aliyu data ga saurin be mata ba se tasa gudu, tana shiga ta fara kiran sunanshi "Aliyu, Aliyu" shiru taji da kyar ta samu hanyar wucewa sbd glasses haka d'akinshi ma, gadon ta haura ta janye bargon tana kiran sunanshi, a lokacin su Abbie suka shigo, kuka Ammie ta fashe da shi tana jijjigashi...

Da kyar ya bud'e idonshi da yayi wani irin ja kaman an zuba borkono yace "Ammie naa" se yayi luuu da idanun ya sume mata, kuka take tana jijjiga shi ta rasa ma me zatayi, a gaskiya Ammie irin matan nan ne masu masifar son 'ya'yansu bawai son daze 'bata su ba, abunku da ba 'yar nigeria ba, ita ba ruwanta da wani abu wai kunyar 'yan fari...

Abu kad'an akan 'ya'yanta se ya d'aga mata hankali, kuma ta tada 'ya'yanta ne akan tsarin larabawa so ba'a musu dole abunda suke so shi ake musu, Abba ne ya dawo d'akin tare da wasu daga cikin sojojin Aliyun suka dauke shi da gudu suka sa a mota, su Ammie ma motan suka shiga banda su arfa da suka basu umarnin tsayawa a gida, suka fice asibiti da gudun tashin hankalin........
















#vote
#share
#comment















'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora