Page 55

3.9K 232 11
                                    

Zuhraa❤❤
           (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
        ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 55

Kwance take akan gadon da ya kasance na Aliyu a cikin part d'inshi dake gidansu se cije baki take tana lumshe ido ta rasa me ke mata daad'i bata san me ke damun ta ba tunda suka zo yola yau satinsu biyu kullum se tayi fama da ciwon mara sama sama amma na yau yayi worst tana cikin wannan yanayin ne Aliyu ya shigo da sallaman shi runtse ido tayi da sauri kaman me bacci......

Sam hankalinshi ba'a kwance yake ba sbd yanayin da take ciki bata so ta kara tada mishi hankali da maganan ciwon maran nan shiyasa bata ta'ba fad'a mishi ba, zama yayi a bakin gadon yana shafa kumatun ta a hankali yake cewa "cutie pie tashi haka baccin nan ya isa magrib ya kawo kai" mika tayi kaman me baccin gaske ta bud'e idonta da suka tashi daga fari suka koma ja tsabar azaban da take ji........

Zaro ido yayi don be ta'ba ganin idonta a haka ba da sauri ya fara ta'ba wuyanta da goshinta yana furta "baby are yhu alright, tashi muje asibiti in bakya jin daad'i" da sauri ta rike hannunshi dake ta'be ta'be a jikinta tace "honey am fyn kawai bacci nake ji" Yace "are yhu sure?" Kai ta d'aga mishi.......

Tana tauna lebenta na kasa minti minti kuma se ta runtse ido, girgiza kai kawai yayi yana kara jin sonta a ranshi sossai yake lura da ita kullum se tayi ciwo amma bata ta'ba bari ya sani sbd bata son tashin hankalinshi kullum kara godewa Allah yake da ya bashi mata kamar zuhraa ta gwammaci ta yi ciwon ta ita kad'ai da ta tada hankalinshi........

Taimaka mata yayi tayi alwala ya d'aura ta kan sallaya yasa mata hijabi se da ya ga tada sallah daga zaune tukun ya fice ya je massallaci se da yayi isha ya shigo da abincinsu a hannunshi don ya hana su nasreen zuwa sossai se in be nan wai zasu takura mishi ita Ammie kuwa har part d'inshi take zuwa dubata maami ce de bata zuwa.......

Sede zuhraan taje daga parlorn kasa da kwala mata kira ya sauko su gaisa haka Abbie da Abba, lalla'bata yayi taci abinci da kyar don bata jin daad'in komai bayan sun gama ya taimaka mata tasa kayan bacci don ce mishi tayi baza tayi wankan dare ba ze musa mata ya sa mishi kuka haka ya kyale ta cotton dogon riga na bacci yasa mata ya sauka har kasa amma cikin ya d'ago gaban rigan sossai....

Kwanciya sukayi yana rungume da ita tana jinshi har yayi bacci ita bacci yaki zuwa ga ciwo se karuwa yake tun tana dauriya har ta raba jikinta da nashi ta mike zaune ta dafe maran tana hawaye da ta samu ya lafa mata se ta kwanta wahalallen bacci ya d'auke ta chan wuraren 2 na dare ta farka da azabbabben ciwo se "wai Allah na" take fad'a tana duk adu'ar da tazo bakinta...... .   

Har kasa ta sauka ta duka bakin gadon tare da kife kanta ko ciwon ze sauka amma inaa se dad'a karuwa yake ba shiri ta fara kiran sunanshi "hamma hamma wai innalillahi" a firgice ya farka da sauri ya kunna wutan d'akin ya diro kasa yana tambayar ta lafiya ba magana se hawaye tana nuna mishi mararta da bayanta...........

Da sauri ya sungume ta dama akwai motan da ya ajiye kayan haihuwanta a ciki sbd irin wannan da gudu ya fita da ita a hannunshi ko nauyinta be ji, yana fita ma yaranshi suka fara haske haske duk da wutan da ya zagaye estate d'in kaman rana ganin ogansu ne yasa su saurin nufo shi ko kallonsu be yi ba Yace "Samuel fito da motan nan"........

Da sauri Samuel ya d'auko motan Aliyu ya shigar da ita baya shima ya shiga tare da d'aura kanta a kan kafanshi, Samuel yaja a d'ari da irin tukinsu na hauka amma duk da haka Aliyu gani yake ba gudu yake ba se tsawa yake daka mishi, zuhraa ta fice hayyacinta se adu'a take bata karasa wani se ta sake ta kamo wani tsabar azaba........

Zuhraa❤❤Onde histórias criam vida. Descubra agora