Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 38
Yau satinsu d'aya a school d'in sossai suke jin dad'in makarantan komai tare suke yi, duk inda zaka ga d'aya to dole kaga biyu, science class suke dukkansu SS1 A har d'alibai sun sa musu suna triples F(fulani), dayake Idan har a waje suke basa ta'ba yin hausa se su ya su, Idan kuma magana zasuyi da sauran d'alibai to turanci sukeyi duk d'aliban makarantan sun d'auka basa jin hausa....
Yau ma kamar kullum zaune suke kowacce a desk d'inta zuhraa ce a tsakiya daga daman ta ilham ce daga hagunta kuma nasreen ce dayake kowani desk mutum d'aya ne, hira sukeyi cikin harshen fulatanci suna dariyansu hankalinsu kwance......
Dayake ba malami a class d'insu, wata yarinya ce ta shigo class d'in cikin yanga da karairaya ta tsaya a gaban desk d'in zuhraa tace cikin harshen turanci "hi am Hauwa Ibrahim, plz can we be friends?" Zuhraa ta juya ta kalli ilham ta sake juyowa ta kalli nasreen a tare suka ce "sorry nop".....
Suna rufe baki 'yan class d'in suka sa dariya dama haushinta suke ji ta cika yanga da iyayi wai ita 'yar governor Juyawa tayi cikin fushi ta nufi desk d'inta tana cewa "kun tsallake wannan amma mu had'u a karo na gaba, alkawari ne se na wargaza amintankun nan".....
Zuhraa ta bud'e baki da niyyar magana kenan se ga chemistry teacher d'insu natsuwa sukayi dama shi ne last period yana fita ko wacce ta goyi school bag d'inta ta goya suka nufi hostel d'insu, ilham ce cikin tsoro dama ta fi su tsoro tace cikin harshen fulatanci "mun shiga uku, zuhraa, nasreen kun ji abunda yarinyar chan tace?"
Zuhraa ce ta fashe da dariya tare da cewa "kai ilham me abun shiga uku? In shaa Allahu ba me raba mu, haka suka ganmu kuma haka zasu barmu" nasreen tace "gaskiya zuhraa idea d'inki na nuna bama jin hausa yayi, da ban yadda ba amma yanzu ina bayanki 100% da ba don idea d'inkin nan da yanzu bamu san manufar yarinyar nan ba"...
Iham tace "toh me muka mata?" Zuhraa tace "ba se mun mata komai ba wasu mutanen ai daga sunga ana zaman mutunci se su nemi wargazawa" nasreen tace "Allah ya raba mu da sharrinta toh" suka ce "Ameen" da wannan hiran suka karasa hostel d'aya bayan d'aya suka yi wanka suka fito suka nufi dining don yin lunch......
********
"Major, major magana fa nake yi" cewar Ayush tana magana da Aliyu da yake kwance kan doguwar kujera yana danna waya shiru ya mata, ta kara cewa "Aliyu wai wannan wani irin mannin hauka ne? Ya za'ayi ina maka magana kana min shiru" ko kallon inda take be yi ba ranta ne ya 'baci amma se ta saussauta murya....
"Wai baby me kake nufi da nine, ni ma fa mutum ce yau sati na biyu a gidanka amma ko hanyar d'akina baka kallo, in naje d'akinka kuma ka korani, Aliyu baka tsoron hakki na?" Shiru ya mata sarai yana jinta shi ya rasa ya ze yi ne, he's confuse be shirya ba sam be son komai ya shiga tsakanin su tsanan ta yake ji har kasan ranshi.....
Amma tana da gaskiya in Allah ya kama shi da hakkinta fa? Innalillahi da sauri ya mike ya fad'a d'akin shi ya cire riganshi ya jefar daga shi se singlet ya fad'a kan gado tare da lumshe idonshi, banko kofan tayi ta shigo d'an karamin rigan bacci ne a jikinta fari be ko kai rabin cinyarta ba, ba komai a jikinta se pant.....
Gadon ta haura tare da buga pillow d'in da yake kwance a kai bud'e idonshi da ya rine daga blue zuwa ja ja yayi ya zuba mata, gani yake kaman bata cikin hankalinta "Aliyu yau fa komai ze faru se ka bani hakki na, Idan ma rashin lafiya kake se ka fad'a min in nema maka magani"...
![](https://img.wattpad.com/cover/197479788-288-k522853.jpg)