Page 37

3.6K 235 13
                                    

    Zuhraa❤❤
              (The flower)

By:fateemah muhammad gurin
       ('Yar mutan Adamawa))

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 37

    "Kutumar ubaaa, wlh ba ze yiwu ba" kowa ita ya zuba ma ido ana jiran aji menene baze yiwu d'inba, takaici ne ya kara kamata ganin ba wadda ya fahimci abunda take magana akai, ita zatama iya rantsewa bata san wainar da aka gama toyawa ba, tunda ta shigo parlorn idonta ya sauka akan Aliyunta......

Rungume da yarinyar da ta gama mata rashin kunya, kallonsu kawai take yi har aka gama da Anty murja bata sani ba, wani abu take ji yana ta so mata daga k'asan zuciyar ta yana dukan kirjinta kansu tayi gadan gadan tana isa ta fisgo zuhraa da har lokacin bata bar kuka ba, duk fuskanta ya kumbura yayi suntum da shi..... 

D'aga hannu tayi da niyyar wanka mata mari, da azama Aliyu ya rike hannun kaman an kunna mata wuta, hauka ta fara na se ta daki zuhraa, zuhraa kuwa ido ta zuba mata tana kallo abunma dariya yaso bata, Aliyu kuwa ganin Ayush d'in ta ki natsuwa ya fisgo hannunta suka nufi hanyar waje........

Ba yanzu yake son kowa yasan waye zuhraa a wajenshi ba kuma ya tabbatar in har ta cigaba da haukan nan tabbas se su Abbie sun fad'a mata, fisge fisge ta fara ita de Aliyu ya sake mata hannu ba yanzu ta shirya barin gidan ba wlh se taci kaza kazan zuhraa....

Abbie ne ya daka mata tsawa "ke!!! Ki natsu ki kama kanki, kin kuwa san matsayin zuhraa a gurin Aliyu?" Maami ta kara da cewa "da kuwa kin sani da baki yi wannan haukan ba toh ma......" Katse ta Ayush tayi tare da cewa "kutumar uba ne ba..." Lafiyayyen mari Aliyu ya sauke mata se da taga stars.....

Natsuwa tayi tare da maida kallonta gareshi, had'e fuskan da yayi kaman hadari ne ya sa taji fargaban sake magana sbd ta san halinshi ita ma ganganci tayi tana shirin zagar mai iyaye a gabanshi, kofa ya nuna mata fita tayi da gudu tana kuka Abba ne ya dubi Aliyu yace "be kamata ka daki matarka ba duk abunda zata maka kuwa, dan Allah a kiyaye gaba"....

Aliyu yace "toh Abba in shaa Allahu zan gyara" tare da Juyawa ya fice daga parlorn bayan ya kalli inda zuhraa take, hayewa sama tayi ta fad'a d'aki tare da kara sakin wani kukan, wardrobe d'inta ta bud'e ta d'auko kayan da aka tsince ta da su ta rungume a jikinta tana sambatun Allah ya bayyana mata mahaifiyarta.....

********

Yau monday gidan yayi wani iri kaman ba mutane a ciki tun ranar da abunan ya faru kowa ya natsu, sossai imani ya shigesu, Aida da Arfa sun tafi school bayan sunyi sallama da su zuhraa duk da ba wani maganan kirki ya had'a su ba amma zuhraa taji d'ad'in yadda Aida ta mata magana ba hantara da tsanar ta data ke gani a kwayar idonta.....

Zaune suke a gaban maami da Ammie sossai suka musu nasiha me ratsa jiki akan abokan banza da sauransu Abba da Abbie ma sunyi nasu kafin suka damka musu kud'i tare da ficewa aiki, kuka zuhraa ke yi ita har ga Allah bata son wani boarding da an barta da day d'inta da ya fi mata, kuma Abunda ya kara bata haushi wai se jiya da dare aka fad'a musu kwana tayi tunane tunane.......

Da kyar maami ta lallashe ta tare da lalla'bata har tayi shiru suka shiga mota da kayansu suka kama hanya, sun zata nan GG yola ne se suka ga an kama hanyar barin yola, nasreen ce tayi karfin hali tace "Emanuel ya naga kana barin yola? Ina ne makarantan".....

Be juyo ba yace "Turkish na kano" zare ido sukayi zuhraa tace "yanzu kana nufin kano muka nufa?" Yace "yes ma" kuka zuhraa ta sa me sauti nasreen ke lallashinta da kyar ta samu tayi shiru tare da kwanciya a jikin kofa tana kallon waje abunda ke damunta shine rashin ganin Aliyu ta so tasa shi a idonta kafin su wuce amma ya ta iya.....

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now