Page 14

3.2K 231 1
                                    

Zuhraa❤❤
       (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
          ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin


بسم الله الرحمن الرحيم

* I dedicated this page to my lovely friends, khaih sun ma wuce friends sun koma aminai ko in ce 'yan uwa Allah ya bar kauna.
Khadija dan baba Sanusi, and
Hauwa Ibrahim yahya. Heart you so much. And congrats Allah ya kara ilimi mai albarka yasa a fi haka.*

Page 14

Har d'akin Ammie ya shiga ya fad'a mata sakon Abba tare da bata lbrn abunda ya faru, itama fad'a ta mishi sossai da nasiha sannan ta fice daga d'akin don cika umarnin mijinnata, wani irin takaici ne da haushin yarinyar da bai san sunanta ba yaji ya kamashi, wai me yasa kowa ke ganin laifinshi? Shi ya kawota ya daura kan titi ko kuwa shi ya kad'e ta? Wani tsaki yaja ya fice daga d'akin, parlorn ya koma ya zauna sbd yana son aje duba maami a gabanshi, hirarsu sukeyi cikin kwanciyar hankali hora ne irin na manya shi yasa be sa musu baki ba, wayanshi yaja ya fara sana'ar dannawa, wata dattijuwan mata ce ta fito da basket babba a hannunta na kayan shayi da d'an abubuwan da baza a rasa ba, d'an dukawa tayi tare da ce musu "barkan ku da warhaka" a tare suka ce "yawwa" banda Aliyu da ko dago kai be yi ba, Abbie ya ce "ke zakije gurin yarinyar ko rahina?" Tace "eh Alhaji" ya sake cewa "toh idi driver ya kaiki kar ki shiga motan Aliyu" ta sake cewa "toh, amm Alhaji numbern d'akin?" Duk suka zubawa Aliyu ido, dagowa yayi be yi niyyan magana ba da cewa ma zeyi be sani ba amma ba karamin kwarjini Idon baffa ya mishi ba, da kyar ya bud'i baki yace "26" ya maida kanshi waya ya cigaba da abunda yake, ficewa tayi tana jinjina kai halin Aliyu se shi ita ko zata so ganin matarshi.

Se da aka kira la'asar sannan duk suka mike kowa ya nufi d'akinshi Baffa da Aliyu sukayi site dinshi yayin da Abbie ya haura sama Abba ma part dinshi ya nufa, a harabar gidan suka hadu dukkansu suka rankaya massallaci a layin farko suka jeru Aliyu ya shige gaba ya ja sallah, dama in yana gari shi ke jan sallah, suna idarwa suka fice a tare suka nufi shashin maami, dama Abba ya fad'awa salma ta gyara ta malami ze shigo ya duba jikinta.

Da sallama suka shiga d'akin salma ta amsa musu idonta nakan Aliyu kafin ta duka ta gaida su gabadayansu suka amsa a tare banda Aliyu, maami na kwance saman gado da duguwar riga me kyau da tsada kayan da suka zama tufafinta tun da ta fara ciwo kullum tana cikin dogon riga kala daban daban, da hijabi me d'an tsai a jikinta daya kai mata gwiwa, kallonta sossai baffa ya tsaya yi har seda Abba ya fara jin haushi tukun, baffa yace a bashi ruwa a cup, Aliyu ne ya mike ya nufi side bed dinta ya dauki cup da ke kan tire a gurin da jug dinshi ya tsiyaya ruwa rabin cup din ya mika wa baffa, karba yayi yace "adu'an da zeyi ze d'an jima kowa ya kama ya samu gurin zama, shi kuma a bashi sallaya" nan ma Aliyu ne ya mike ya dauko sallaya ya shimfid'a baffa da Abbie suka zauna yayin da Abba ya zauna bakin gado dai-dai kan maami, Aliyu kuma ya zauna kujerar dressing mirror.

Bayan kusan minti talatin da zamansu baffa ya mike da cup d'in da ya gama adu'a a hannunshi, ya musu umarni da su mike duka yace "idan har na watsa mata wannan ruwa ta motsa to asiri me mugun karfi da wuyan karyuwa akayi mata, in kuwa bata motsa ba se mu koma gargajiya" duk daga kai sukayi bisimilla baffa yayi ya watsa mata ruwan, wani irin zabura maami tayi ta kusa hantsilowa daga kan gadon da sauri Abba ya rikota ya gyara mata kwanciya hawaye na zirara a idonshi, duk dauriyan shi tausayin maami ya hana shi nunawa ya jima yana danne kukanshi a Idon mutane sede ya samu guri yayi kayanshi ya share hawaye amma yau, ya kasa wannan jarumtan, daura kanshi yayi saman kafad'an yayanshi ya sa kuka, wani irin tausayinshi ne ya kama Aliyu, maami, baffa da Abbie.

Idon Aliyu yayi wani irin ja kaman an watsa mishi citta ya dubi Abbie da shima hawaye yake sharewa a fakaice kar ya ci gaba da karyawa d'an uwan shi guiwa, duban shi yakai kan maami ita ma kukan takeyi, baffa ya duba a kausashe yace "dan Allah baba ka fad'a min wadda yayiwa maami haka, ni kuwa na dau alkawarin tozartashi a Idon duniya se ya d'and'ana azabar da Allah ne kawai yasan iyakarshi, se yaji ya tsani kanshi a duniya na yi alkawari se ya gwammaci haihuwarshi yaje gurin Allah kuma ya musu hisabi da maami" ya karasa muryashi na rawa tare da d'aci a harshen shi, baffa ne ya dubi Aliyu yace "Aliyu bani da wani hurumin sanin waye ya mata kai tsaye, sede Allah ne ke da ikon hakan mu zuba ido tare da Adu'a Allah ya toni asirin ko waye ne" ya kuma kai dubanshi ga su Abba yace "Alhaji kai daya kamata ka tausashe shi shine kake tayashi ko ba'a fad'a min ba nasan kaine babba dashi kuma matarshi ce wannan, yayinda kai kuma kake mijin d'ayar hajiyar kuma mahaifiyar Aliyu, Allah ne fa ya bamu daman sannin wannan d'in ba wayon mu ba ba dabarar mu ba, kuma shi ze warkar da ita da izinin shi, godiya ya kamata ka mishi tare da dagewa da Adu'a don ganin ta mike da kafafunta" nan Abba ya saki Abbie yana share hawayenshi tare da cewa "astagfirullah ya Allah, Allah na gode maka da wannan haske da ka bamu, Allah kai ke da iko akan wannan baiwa taka, ya Allah ka tashi kafad'unta ka kuma toni asirin wadda yayi mata wannan mummunar aikin, ka tozarta shi tun anan duniya Albarkacin annabin mu manzon tsira annabi Muhammad (S. A. W)" duk tare suka karasa tare da cewa "ameen don nabiyul rahmati" Abbie ya dubi baffa tare da cewa "me abunyi malam? Baffa yace "gsky se na koma gida na hd'a mata magunguna, kafin na tafi zan bata ruwan tofi a ringa shafe mata jiki da shi kafin na dawo ya rage wani abun in shaa Allah" Abba ne yace "toh se ka bar tafiyan zuwa gobe idan 'yar ka ta farka daga asibiti se ka wuce sbd kar ta farka bata ga Idon sani ba hankalinta ya tashi" Abbie yace "hkne" baffa yace "toh se wani hanzari ba gudu ba, d'akin nan tun shigowata jikina na bani ba lfy ba in ze yiwu a fitar da ita daga d'akin nan mu bincika" Abba yace "toh" tare da kwalawa salma kira da hanzari ta shigo yace ta tayashi kama maami a daurata kan keken guragun da aka ajiyeta ana zagaya wa da ita, tace toh tare da jawo keken ta kawo shi gaban gadon suka daura maami akai ba abunda ke iya zama a jikinta harta kanta a langwa'be yake.

Baffa yasa hannu a aljihu ya fito da wani d'an roba karami ya bude wani abu baki a ciki ya mikawa Abbie yace "ku shafa a hancinku duk inda kukaji wari sossai to akwai asiri a gun" Abbie ya shafa ya mikawa Aliyu yana cikin shafawa Abba ya dawo shima shafawa yayi, baffa ma ya shafa suka bazu tsakar d'akin.

A hankali Aliyu ya nufi gadonta ya zare bedsheets din da pillows din ya watsar ya d'aga katifan da yana wuya mutum biyu su d'aga amma shi kad'ai ya d'aga, yana d'agawa wani tukunyar tabo ya bayyana an rufe bakinshi da jan kyalle, Baffa ya isa gun yasa hannu ya dauki tukunyar ya kawo tsakar d'akin ya fara jera wasu Adu'o'i a hankali tukunyar ta fara tsagewa ita kad'ai wani irin ihu sukaji yayin da dakin ya fara girgiza wutan d'akin na daukewa ya kawo, yace ku ci gaba da duk adu'ar data zo bakinku, duk adu'a suka fara wani irin tsoron mahallicinsu ya shigesu, a hankali komai ya dai-dai ta wutan ya dawo dai-dai, tukunyar ya fara darewa wani irin fashewa tukunyar yayi tushhh!!! Wani bakin ruwa me uban wari ya buge su, toshe hanci sukayi na d'an lokaci kafin warin ya tafi, baffa ya tsuguna tana duba me a ciki jinjina kai yakeyi tare da fad'in Alhamdulillah har so uku ya kara da cewa "hakika Allah shine abun godiya daya bayyana mana ta hanyar da akayi asirinnan cikin sauki" Abba yace me wannan din?, baffa yace "mahaifarta wato da mahaifarta akayi amfani gurin yi mata mummunan asiri da karyashi se Allah, toh Allah ya kawo karshensu in shaa Allah" dukkan su zare ido sukayi tare da had'a baki gurin cewa "mahaifa fa?".

Sorry zaku dinga ganin post d'ina lokaci zuwa lokaci, exams ya gabato kai ya dau zafi se kunyi hkr. Thanks for reading.












#vote
#share
#comment











'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang