Page 49

3.7K 243 26
                                    

Zuhraa❤❤
         (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
          ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin



بسم الله الرحمن الرحيم




Page 49

Ammie,  maami, da zaid kuka kawai sukeyi yayin da su Abbie jikinsu yayi sanyi har ogan Aliyun zuhraa kam jini ne ya tsaya da aiki a jikinta, tunda taji abunda Ammie ta fad'a ta daskare a wurin da take idonta kyam a kan shi, Ammie da zaid suna kuka ne na kasancewarsu doctors amma su kasa lura da abunda ake ma Aliyu har se da yaci karfinshi...........

Abbie ne yayi karfin halin cewa "sauda ba kuka zakuyi ba, kawai musan Abunyi" mikewa Ammie tayi tana share hawaye tace "bari in kira yaya Aasim in yana cyprus se muyi saurin kaishi" Abba na jin haka suka fita shi da ogan Aliyu sukayi airport, Ammie yayan ta ta fara kira dayake toxicology ya karanta(study of poison) .........

Kuma babban likita ne da ake ji da shi a cyprus, ringing d'aya ya d'auka suka fara magana da larabci "yaya kana ina ne plz" yace "ina cyprus lafiya?" Tace "ba lafiya ba Anyi poisoning Aliyu and bamu lura ba se da yaci karfinshi, plz ka shirya mana komai a hospital d'inku gamu nan zuwa" "subhanallah Ohk se kun zo and kinsan yhu have to be hurry ku ringa rushing duk da idan har kwanan shi be kare ba se kiga ya mike ki kwantar da hankalinki kin san hawan jininki"........

Gyad'a kai kawai tayi kaman yana ganinta tayi mishi godiya ta kashe waya, kiran Abba ne ya shigo wayan Abbie da sauri ya d'auka yace "ya ake ciki?" Abba yace "yaya an samu kuyi sauri a sa shi a ambulance driver d'in ya zama soja yanzu ku same mu a airport" Abbie yace "toh" tare da kashe wayanshi yayi ma zaid magana........

"Kukan nan ya isa haka zaid duk abunda kaga ya samu bawa haka Allah ya tsara mishi kayi maza ka samo mana keyn Ambulance" da sauri ya fita yana share hawaye da soja d'aya suka je suka kar'bo, ba 'bata lokaci aka fito da Aliyu aka sa a ciki basu yadda kowa ya ta'ba shi ba har an gama fita Abbie be ga zuhraa ba komawa yayi ya same ta yadda take a tsaye guri d'ya sam hankalinta ya bar jikinta...... .  

Hannunta ya kama kawai sukayi waje binshi kawai take yi ba tare da tasan me take yi ba, soja d'aya ne ya karbi keyn ya fara tuka su sauran sojojin da ba'a basu umarnin motsawa ba suna nan kyam sun hana kowa sakat a asibitin, doctors kuwa kab doctors d'in hospital d'in aka kama har wa'yanda basu da duty har gida aka bisu a take aka wuce jaaji da su aka fara bincike.........

Suna isa airport Abba ya mika ma Abbie tickets guda 5, kallonshi Abbie yayi da alamun tambaya murmushi Abba yayi tukun yace "yaya ka manta akwai yara a gida? Kuma mata, ni da khadija zamu koma yola ku kuma se ku wuce in yaso mayi exchanging daga baya in har za'a jima"

Abbie ze yi musu maami tace "gaskiya ne be kamata a bar yara 'yan mata a gida ba babba me kwa'ba ba musamman 'yan jami'a" Abbie yace "hkne toh bari mu wuce se munyi waya" Abba yace "in shaa Allahu Allah ya bashi lfy" suka ce "ameen" maami kallon zuhraa kawai take daga gani ka san bata san me take yi ba........

Abbie na rike da hannunta ya jata suka shige ciki, Abba ya kalli maami yace "habibty kin lura da yarinyar nan?" Cikin sanyin jiki tace "eh habiby zata dawo cikin hankalinta in shaa Allahu tana cikin shock ne I guess" murmushi suka ma juna sun san tana hannu na gari so duk abunda ya kamata sun san Ammie da Abbie zasu kula da su.......

Ajiye maami yayi tare da yima ogan su Aliyu da xe wuce sallama, shima yace "zan wuce zamu fara bincike akan doctors d'in asibitin gabad'aya and komai yake ciki zamuyi waya" godiya sossai Abba ya mishi tukun ya wuce, Abba kallon maami yayi yace "ga keyn nan Motan na waje kije ki had'o mana kayanmu, ni kuma bari in sama mana tickets" tace "toh" tare da mikewa ta kar'bi keyn tayi gaba don komawa hotel da suka kama...............

******

ROYAL ARTEMIS HOSPITAL CYPRUS

        Shine aka rubuta a saman babban building na hospital d'in da gudu aka fito da gadon d'aukan mara lafiya dama jiransu ake, ba'a tsaya ko ina ba se A. E ko magana Ammie bata samu yi wa yayan nata ba sbd da sauri sossai ya wuce ya shige shi da doctors uku masu taimaka mishi.............

Kowa a gurin adu'a yake yi na fitowarsu lafiya se kira ake ko wai bayan minti se sun samu me kira daga nigeria, su maami har sun isa yola zaid ya kira ma'aruf ya gaya mishi, Ammie ta kar'ba tare da rokan shi tunda yana kasa me tsarki yayi ma Aliyu adu'a plz, ta bangaren zuhraa kuwa tunda suka shiga jirgi har suka sauka Abbie na rike da hannunta......

Binshi kawai takeyi a baya kaman rakumi da akala, tunda aka shige da Aliyu ya zaunar da ita ko motsi bata yi ba, ba yadda Ammie batayi da ita ba ko kuka ne ta samu tayi ze rage mata wani abin amma ta kasa ko magana...........

                      Two hours later

Nurses da doctors ne suka fara fitowa se da kowa ya wuce tukun doctor Aasim ne ya fito karshe yana share zufa fuskan shi ba yabo ba fallasa ido suka zuba mishi har zuhraa dake zaune tabbas ta san a lokacin in har ya kuskura yace Aliyunta ya mutu toh itama gawanta za'a d'auka, ganin yadda suke kallonshi ne yasa shi murmusawa yace...........

"Alhamdulillah it's successful" zamewa zuhraa tayi ta zube a kasa tare da sujjada se kuma ta fashe da kuka me tsanani, Zaid baki har kunne Ammie kam d'an uwanta tayi hugging tana jin daad'i, Abbie ma murmushi yake matsawa yayi kusa da zuhraa ya d'ago tare da jingina ta da jikinshi yana shafa bayanta.........

Se da suka gama farin ciki tukun suka samu gaisawa da yaya Aasim suka dunguma a motanshi zuwa family house na su Ammie dama ba wadda suka fad'awa zuwansu sbd gudun hankali ya tashi, a hanyarsu ta zuwa gida ne suka ta kira suna fad'awa family an ci nasaran aiki, zuwa gobe ma Aliyu ze iya farkawa...........

Cikin farin ciki mahaifiyar Ammie ta tare su, mahaifin ta Allah ya mishi rasuwa se mahaifiyarsu da suka gina mata katuwar gida take pantamawa, ummi suke ce mata bata san ya su Nasreen suke kiranta ba kawai se tace "ummi ina yini?" Cikin harshen turanci ita ma ummin murmushi ta mata tare da jawo ta jikinta tana tambayar Ammie cikin harshen larabci wannan itace kishiyantan......

Amsa Ammie ta bata da turanci, tare da fad'a mata Abbie da zaid suna masaukin baki, sawa tayi aka tura musu abinci, se da sukayi wanka suka ci abinci suka natsu tukun Ammie ke fad'a ma ummintan abunda ya kawo su, kuka ummin ta saka sai da tayi me isan ta tukun tace maza a kaita ta ganshi.........

Yaya Aasim ne da twin brother d'inshi yaya Aadil suka shigo da sauri Ammie ta mike ta rungume yayanta shima cikin farin ciki yayi hugging d'inta kallon zuhraa yayi da take kallonshi baki sake ya d'aga mata hannu, murmushi tayi tukun ta gaishe shi tana mamakin kaman su da Aliyu kaman an tsaga kara se de shi ya d'an manyanta kuma yafi Aliyu fara'a.......

Kannenta mata biyu ne suka shigo suma cikin farin ciki suka rungume juna zuhraa ta san su so da sannayar juna suka gaisa, had'uwa sukayi aka fara hiran yaushe gamo ganin hiran na 'yan uwa ne yasa zuhraa shigewa d'aki, daga d'akin tana jin hiran su tana ji wadda taji ake cewa yaya Aasim yana cewa.........

Ai ba karamin tsallake rijiya yayi ba a cikin 100%, 2% ne kad'ai masu tsallake wannan poison da aka bashi, Adu'a suka fara kwarara mishi wasu na amsawa da kuma fatan tonuwar asirin me son kashe shi.........




















I'm really sorry wlh da kyar nayi wannan sbd wani matsala nawa, kuyi hakuri dashi sorry to say gobe ma ba lallai ne ku samu ba.🙏🙏🙏
























#vote
#share
#comment



















'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Onde histórias criam vida. Descubra agora