Page 47

4.3K 242 17
                                    

  Zuhraa❤❤
             (The flower)

By: fateemah muhammad gurin
             ('Yar mutan Adamawa)


Wattpad:  muhdfatimagurin


*this page is dedicated to yhu #Ayushermoh'd thanks for the support and Advice Allah ya bar zumunci*

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 47

"Innalillahi wa'innailaihi raji'un" shine abunda daddy ke ta nanatawa da sauri ya d'auki goran ruwan da momy ta shigo dashi don ba Ayush ya bud'e ya watsa mata, ajiyar zuciya ta sauke se kuma ta fashe da kuka a lokaci d'aya tana kwararawa 'yarta adu'a shima daddy kuka yake yi........

Da kyar ya fara kiran 'yan uwa da abokan arziki yana fad'a musu cikin lokaci kankani aka cika gidan ba 'bata lokaci aunties d'inta da momynta dake ta kuka suka mata wanka aka suturce ta aka kaita gidanta na gaskiya, akan kabarinta ya tsaya yana alkawarta abu a cikin zuciyarshi tare da rantsuwa da kabarin.........

********

Zaune yake a parlorn sama bayan ya gama dinner d'inshi coffee yake sha se system dake kan table yana aiki a kai karan wayanshi yaji be dauka ba se da aka mishi three misscall d'auka yayi a na ukun ba tare da yayi magana ba "salamu alaikum" aka ce a d'ayan bangaren.........

"Wa'alaikumussalam" Aliyu ya amsa da, soja ne d'an uwanshi amma be kai Aliyu matsayi ba, Aliyu ya san shi da gulma shi yasa tun farko be d'auki wayan ba ji yayi sojan na cewa "sir ban ganka a wurin rasuwan bane shi yasa na kira in maka ta'aziyar"......

Gaban Aliyu ne ya fad'i yana fatan Allah yasa ba'a gida bane a hankali yace "waye ya rasu?" Sojan ya fara ratta'bo zance "baka sani ba? Ai matarka ta rasu, naji wasu na cewa se da kuka rabu kafin ta rasun wai da....." Kit Aliyu ya yanke wayan "innalillahi wa'innailaihi raji'un" duk da Ayush ta mishi laifi ba karami ba amma ya ji mutuwanta "Allah ya gafarta miki" shine abunda ya furta.......

Kallon Zuhraa yayi da ta fito da gudu-gudu sauri-sauri daga ita se towel karami iya karshi cinyarta mikewa yayi ganin a tsorace take yace "lafiya?" Cikin in ina tace "kyankyaso ne a bayi na" zaro mata ido yayi yace "kyankyaso kike wa wannan abu? Wuce ki koma" hawaye ne ya fara zuba a idonta don ba karamin tsoron kyankyaso take yi ba, shi kuma ganin ta a haka ne yaso birkita shi, tana so ta sashi abunda be yi niya ba......

Tsawa ya daka mata kafin ya rufe baki ta fashe da kuka me sauti, tsaki yayi tare da mikewa ya nufi d'akinta yana tsotson baki, dube dube ya fara har cikin bayi tukun ya ga kyankyason tsintsiya ya d'auka ya buge tare da d'aukowa a parker ya fito, tana nan tsaye in da ya barta a zuciyarshi yace bari ya gwada ta ya gani......

Kyankyason yayi kaman ya jefa mata wani irin ihu tayi tare da sulalewa zata fad'i da sauri ya sake parkern ya taro ta jikinshi "ke!! Ke!!  Fateemah" yana jijjigata amma shiru, mamaki yake yi yanzu wai d'an wannan abun se ya sa ta suma? "Mtseww" d'aukanta yayi ya nufi d'akinta a gado ya kwantar da ita, garin kwantar da itan ne towel d'inta ya kwance daga sama.......

"Yaaa salam" shine abunda ya furta da sauri ya ja ya rufe mata, mikewa yayi ya d'ebo ruwa ya watsa mata a tsorace ta mike ta kankame shi jikin ta na rawa, rabata da jikinshi yayi yana cewa "ke wai me haka ne? Haba d'an karamin gwaron nan kike ma haka?" Turo baki tayi a shagwa'be tace "to ba kai bane ba?" Murmushi yayi tare da zaro ido yana jan iska yace "ni kuma? Me nayi?"......

Hawaye ne ya gangaro a idonta tace "ka kama ka sa min kyankyaso" dariya ya fashe da dashi a hankali kallonshi ta tsaya yi tana gode ma Allahn da ya bata shi a matsayin miji, tana ji kaman ita tafi kowa sa'a a duniya, se da ya tsagaita dariyan ta kara turo baki gaba...........

Zuhraa❤❤Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt