Page 18

3.3K 244 2
                                    

Zuhraa❤❤
(The flower)

By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 18

A shirye suka fito duk cikin jallabiyoyi dubai fashion da gyalensu Aida na sanye da red colour, yayin da Arfa ke sanye da black colour, Nasreen kuma milk colour, rantsatsiyar mota aka bud'e musu suka shige....

Aliyu suke jira, don duk lokacin da zasu fita, in har suka kuskura ya riga su fita sun shiga uku, suna zaune a cikin motan suna shan Ac, suka ga fitowan Aliyu cikin kananan kaya black trouser da white shirt me bakin layi layi a jiki....

Gashin kannan ya sha gyara yayi kyau se sheki yake, kafan shi kuma wani tsadadden timberland boots ne fari, yana rike da wayoyinshi iPhone 11 da Samsung s8 edge...

Aida ce tazo dai-dai kunnen arfa tace "sis guy dinanan haddadde ne, da ba don uwa d'aya uba d'aya muke ba da se inda karfi na ya kare" Arfa ta d'an harare ta tare da cewa "lallai Adda kika sake yaji ki kinsan se jikinki ya gaya miki, min kam wala ko yali am,(ni ba ruwa na)...

Aida zata dake magana kenan ya bud'e driver sit ya shiga, ya juyo baya yace "Angel to front" tace "yes bro" tare da bud'e kofan ta zagaya ta koma gaba...

Yayi wa motan key yaja a guje ya bar estate din, dama in zeyi fita irin wannan da sisters d'inshi su kad'ai suke fita ba tare da sojojin shi ba kuma shike driving...

Suna isa straight yayi parking space, yayi parking motar, suka fito suka shige cikin mall din babban mall ne da ake ji da shi a jimeta 'San hussein'...

Suna shiga Aliyu ya samu guri ya kame, su kuwa basket suka ja kowa da nashi, suka nufi layin abubuwan da suke bukata..

Hankalinshi nakan wayanshi yaji an ce "Major How comes kana gari ban sani ba?" A hankali cikin natsuwa ya daga kai ya kalleta, ko da be kalle ta ba yasan muryan..

Yarinyar oganshi ce Lt. T.y Abdulsamad da take nacin sonshi, shi be sonta ba tsarin shi bane amma taki ta gane, duk inda yake tana gurin, shi wlh ya rasa yadda zeyi da ita...

'Yar kaduna ce, gidansu a barrack dinsu yake, kuma a Apti American university of Nigeria(AUN) take karatu 300lvl, sunanta Aisha amma Ayush ake ce mata...

Karamin tsaki yaja tare da murmushin yake yace "Au ashe in zanzo garinmu se na gaya miki?" Tayi fari da ido tare da Murmushi, gaskiya kyakyawa ce ta karshe, fara sol tana da dogon hanci da dan karamin baki, sede idonta kanana ne, kuma tsiririya ce sossai ba gaba ba baya....

Wando ne a jikin ta ya kama ta tsam tare da d'an karamin top wanda in ta d'aga hannu se cibiyar ta ya nuna, da d'an karamin veil iya wuyanta, heavy make up ne a fuskan ta...

Cikin make murya tace "Haba sweetbae ba haka nake nufi ba, yaushe ka shigo, ai da ka fad'a min, in shirya maka tarba me kyau"..

Yace "iyayena sun shirya min, thanks" tace "hmm toh baby what are u doing here, banga kana shopping ba" yace "I brought my sisters" wani takaici ne ya kamata, ita fa ta tsani ya ra'bi wata mace ko da mahaifiyar shi ce..

'Dan karamin tsaki taja, ita be ta'ba kai ta ba in ta ce ya kai ta ya dinga mata wasa da hankali kenan, zama tayi a hannun kujerar da yake tana wani karairaya kanta na kara girma, ganin duk 'yan matan gurin masu safa da marwa suna iyayi don ya kula, se hararar ta suke...

Zuba mishi zance ta fara kaman yadda ta saba iyakaci yace mata eh ko a'a, dama ta saba so ba ruwanta, inde ze kula ta, suna nan zaune se ga su Aida sun fito kowa basket dinta shake da kaya..

Se kallon tara saura kwata take musu, ba lefi suna d'an d'asawa da Aida, amma ta tsani arfa har gwara arfah kuma da nasreen dayake ce ma angel, "Anty Ayush" inji fad'an Aida, ta wani yatsina fuska tare da cewa "hi Aida"..

Mikewa Aliyu yayi tare da kallon Arfah da nasreen da sauri suka ce a tare "Ina yini anty aisha" da kyar tace "lfy" yatsu biyu Aliyu ya daga mata ya yi juyawarshi ya wuce..

ATM card d'inshi ya mika musu ya kalli Aida tukun ya juya ya tafi, ta gane nufinshi ta karbo mishi, dama haka suka saba, da sauri Ayush ta taso ta bishi suka jera suna tafiya tana iyayi..

Mota ya bud'e ya shige, ita kuma ta tsaya jikin window d'inshi, saukewa yayi tare da cewa "ya akayi kuma?" Tace "haba baby motana ne seda na zo nan ya lalace nayi nayi in tayar yaki"..

Sanin kanta ne ba zuwa zeyi ya duba ba shiyasa tayi mishi karya, shima yasan sarai karya ne amma se ya biye mata yace "toh me kike so?" Tace "ka sauke ni school plz"..

A lokacin su Aida suka iso suka shiga motar da sauri, kallon nasreen data bud'e gaba zata shiga yayi yace "angel koma baya" juyawa tayi tana tura baki ta koma baya, motar yayi wa key da sauri Aisha ta zagaya ta shige gaba, tasan ba karamin kokari tayi ba data sa shi magana sossai yau...

Har cikin school ya ajiyeta be ko kara kallon inda take ba yaja da gudu ya juya don sun bar medical center a baya, ta'be baki Ayush tayi tace "oho de ka kawo ni" fidda waya tayi ta kira driver d'inta dama dashi taje, tace mishi ya zo school ta dawo..

Suna shiga asibitin direct d'akin da zuhraa take ya nufa suna binshi a baya, da sallama ciki ciki ya shiga, badan tana kallon kofan ya shigo ba da se ta ce beyi sallama ba ta amsa a hankali da muryanta me sanyi tace "wa'alaikassalam"..

Tunda ya turo kofa suka had'a ido da d'an sauri ya kawar da kai, danshi be cika so suna had'a idanu ba sbd faduwar gaban da yake ji matukar suka had'a idanu..

Jan kujera yayi ya zauna tare da gaida baaba rahane ta amsa mishi a mutunce, su arfa ma suka gaida ta, suka dubi zuhraa suka ce ya jiki tace 'da sauki'

Nasreen ta dubi baaba rahane tare da cewa "baaba wannan wacece kyakyawa da ita?" Kafin baaba tayi magana aka turo kofan tare da sallama Ammie ce ta shigo, a tare suka ce 'evening mom' tace "masa'ul khair kaifa antum"(evening how are you all) suka ce "bi khair wal-hamdulillah"...

Nasreen ce ta sake magana "Ammie wace ce wannan"? Ammie tace "'yar wanda ke yiwa maaminku magani ne, lokacin da hammanku yaje Gurin ne ya kad'e ta da mota" Murmushi Nasreen tayi tare da karasawa ta d'ane gadon tace...

"U r so cute, will you be my friend"? Kowa ya zuba ido suna zaton bata jin turanci tunda kauye take, har Aliyu dake danna waya hankalinshi na kansu, se ji sukayi tace "yeah y not, you are so cute too, by the way am fateemah Abubakar Gurin by name, but zuhraa ake ce min and you?"

Dukkansu mamaki ne ya kashe su, da sauri Aliyu ya juyo ya zuba mata ido, suna had'a idanu ya kawar da nashi tare da ta'be baki, Nasreen tace "am Aisha Ahmad ribadu ana kira na nasreen, nice to meet yhu" tare da mika mata hannu zuhraa ma hannun ta bata sukayi musabaha..

Nasreen ta juyo ta dubi Aida tace "kinga big sister na Adda Aida" zuhraa ta daga ido ta kalli Aida da tunda suka shigo ta lura da yadda take mata kallon banza, yake tayi tare da daga mata hannu, itama zuhraa da hk ta mayar mata...

Nasreen ta sake duban Arfah tace "and this is my sister too Arfah, diya nake ce mata" Zuhraa ta kalli arfah tare da Murmushi tace "nice to meet yhu diya" arfah ma Murmushi tayi mata tare da cewa "nice to meet you too, hope zaki dauke ni sister" zuhraa tace "of course yes, y not"..

Murmushi suka sakarwa juna tare da musabaha, Ammie ta kalli Aida tare da girgiza kai, ita kam Alhamdulillah bata san Ina Aida ta dauko wannan halin nata ba Allah ya shirya min ke Aida...

Aliyu ne ya katse ta daga tunanin da take yace "Ammie mu tafi koh, nasan kinyi closing" tace "yeah muje" nasreen ce ta katse su "Ammie dan Allah ku barni na kwana gurin zuhraa" Ammie tace "a'a nasreen sede gobe kizo ki yini mata"..

Zata kara magana ta gamu da Idon Aliyu, ko ba'a fad'a ba tasan warning yake mata, in ta kara magana kuma sunanta gawa, juyawa tayi ta kalli zuhra tace "bye zuhraa se nazo gobe, Allah kara sauki" zuhra na Murmushi tace "bye nasreen thanks" arfah ma sallama ta mata, Aida dayake ita ce karshe ko kallon ta batayi ba ta fice.....










#vote
#comment
#share












'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now