Page 21

3.3K 227 5
                                    

Zuhraa❤❤
         (The flower)



By: fateemah muhammad gurin
          ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

~~~ I dedicated this page to my one and only namesy, Fatima usman hadejia ~~~~

Page 21

Rukkayah umar wacce aka fi sani da rukky 'yar asalin jos ce karamar hukumar wasai mahaifinta shine minister of defence mai ci a yanzu department d'insu d'aya da Ayush tun 100lvl suke tare sbd jininsu ya had'u...

Lubabatu (lubsy) 'yar kd ce mahaifinta babban d'an kasuwa ne, ita ma tun 100lvl suke tare...

Zainab Abdulaziz (zee) 'yar deputy governor ce na gombe state duk cikin su bayan Ayush ta fisu iyayi ita kuma DE tazo daga 200lvl suka hadu..

Afreen (Afrey) 'yar sarkin bauchi ce ita kuma transfer akayi mata daga Al hikma zuwa AUN a 300lvl suka had'u, ita kuma ta fisu sarauta tana da mugun jan aji da kasaita bata cika magana ba haka bata karuwanci barta da shigan banza da shaye shaye..

Dukkansu kyawawa ne ba laifi kuma kowacce da gidanta duk cikin mafia's quaters suke amma layi daban daban..

%%%%%%%%%%%%%%%

Suna isa gidan suka sauko zuhraa idonta kaman ze fad'o kasa ga tsoro ga kyaun gidan ya rud'ata, ta shiga uku ita kam an kawo ta gidan yankan kai, Anya baffanta ya san inda aka kawo ta?

Innalillahi wa'innailaihi raji'un ta fad'a a fili ganin sojoji barkatai a tsakar gidan sun kakkame guri guda kaman statue, Ammie ce tace "zuhraa sauko mana" tace "Ammie baffa fa?"..

Tace "baffa na ciki ki zo muje kinga magrib yayi" tana rufe baki se ga su baffa dashi da Abba da Abbie sun fito daga part d'in Maami, karasowa yayi gurinsu ya ce "nasan za'a rina wannan se ta tara maka mutane akan sojoji, zuhraa sauko kinji ba abunda zasu miki"..

A hankali ta sauko, Ammie tace "wai malam me yasa take tsoron sojoji ne haka?" Yace "wlh lokacin da ta taso ne tana 'yar shekara 5, mun fita da ita kiwo munzo dai-dai gurin border aka kama wasu da makamai, zasu gudu ne shine aka har'be su, karan bindigan yasa ta suma, tun daga lkcn take tsoron sojoji sossai"..

Ammie zata kara magana kenan aka kira magariba dama Aliyu tunda suka shigo ya fice part d'inshi, har yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya, ya fito yayi mamakin ganinsu a tsatsaye ya karaso tare da cewa "lfy?"..

Ammie tace "ba komai, ku karasa massallacin mu bari mu shiga ciki" ta kama hannun zuhraa suka fara tafiya a hankali zuhraa na d'an dogara sandarta suka shige...

D'akin nasreen suka nufa, nasreen tayi wanka tare da alwala ta fito, ta taimkawa zuhraa ma ta shige ta nuna mata duk abunda bata sani ba da yadda zatayi amfani dashi, ta fito ta ciro mata rigan bacci dogo mai kauri da himar ta ajiye mata...

Se bayan sallahn isha nasreen ta dubi zuhraa tace "mu sauka muci abinci" zuhraa tace toh ta mike ba tare da ta cire khimar dinta ba ta bi bayan nasreen, kasa suka sauko basu tarar da kowa ba kuma dining ba komai nasreen tace "muje na tabbatar suna part d'in maami, don wani lokacin a chan muke cin abinci" zuhraa tace "ohk amma dan yimin bayanin gidan nan waye maami?"

Nasreen tace "kinga su Abba su uku iyayensu suka haifa, biyu maza d'aya mace, Abbie ne babba se Abba se momy tana aure a kano, Ammie itace mahaifiyar mu kuma ba 'yar kasarnan bace, mu hud'u ta haifa, se Abba ya auri maami yar katsina ce basu ta'ba haihuwa ba yanxu ma haka jinya take don tunda aka haifeni take kwance bata magana bata motsi tana da kishiya anty murja kuma maami da kanwarta salma take zaune, se mommy 'ya'yanta biyu"...

Zuhraa❤❤Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora