Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 9
After two hours dr. Sajid malik ya fito yana sharce gumi, ya dubi Aliyu ya ce "muje office" Aliyu be ce komai ba ya tashi ya bishi, suna karasawa dr. Ya dubi Aliyu yace "major nayi iya kokarina akan ciwon mahaifiyarka sede duk wani bincike da mukayi ba mu samu matsalan komai ba, komai nata lfy klau ni a tunani na ciwonta ba na asibiti bane why not ku gwada Islamic medicine amma to be sincere ciwon nata be shafi asibiti ba" Aliyu ya sauke numfashi yace "gskyanka dr. Inda aka samu matsala kenan bamu ta'ba gwada Islamic medicine ba, bari in je in fara mana processing komawa se mu nema malami" dr. Sajid yace "toh Allah taimaka ga takaddar sallamarta se kayi signing" signing Aliyu yayi ya fita, nan take ya wuce airport ya fara shirya musu komawa gida.
%%%%%%%%%%%%%%%
Su zuhra suna gama alwala suka dawo gurin zamansu suka samu hammansu ya riga ya shimfid'a musu abun sallah hawa sukayi suka yi sallansu suna idarwa suka dauki kwarya suka nufi shanukansu suka tatso madara me kyau da dumi, suka koma suka ba hammansu nashi, su ma suka koma gefe suka zauna suka fara shan nasu, se da suka koshi suka d'auraye kwaryar suka ajiye, suka ci gaba da hira yayin da shanukansu suna gefe suna kiwo.
Har seda magariba ta gabato suka kad'o shanukansu suka yo gida suna karasowa kowa ya shige gidansu.
Zuhra na shiga ta samu baffa na alwala ta duka tace mishi "baffa sannu da gida" yace "yauwa mamana ya kiwo? Ba wani abunda ya faru ko?" Tace "eh baffa ba komai, bari inje in daure shanukan in zo nima inyi sallah" yace "to mamana Allah ya miki albarka" tace "ameen"tare da mikewa ta shige garken shanukan ta d'aure ko wanne a jikin tikensa ta fito tayi alwala ta shige dakinsu, ta idar da sallah kenan se ga jainabu ta shigo d'akin ta fara zubarda kayan zuhran, duk da zuhra bata da wani kayan kirki amma akwai tsabta kayanta tsab tsab a ninke, sanda ta zubar da komai tukun ta dauko wani kayan bakin saki na fulani da baffa ya d'inka musu ita da zuhra last week ta nufi hanyar fita d'akin sauran kayan da ta zubar bata mayar da komai ba, zuhra ta mike a fusace dama zuhra me hakuri ce amma in ranta ya 'baci ba dadi, ta tsani wulakanci, ta nufi jainabun tare da tare hanya ta maka mata harara tace "koma ki ajiye min kaya kuma ki mayar da sauran inda kika same su" jainabu ta harareta tace "bazan mayar ba na karfi ne, ke har kin isa? Banza shashashar da mahaifiyar ta bata sonta amma ta kasa barin gidan," ran zuhra ya kara b'aci ta d'aga hannu ta zabga ma jainabu mari tare da cewa "ni kika zaga ko, yau se na nuna miki shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ne, duk abunda kike min ina shanyewa ne kawai sbd ke kanwata ce be kamata komai kika min in rama ba amma yau zan cire miki wannan rashin kunyan" jainabu tace "kutt kika mare ni?" Kawai ta kamo wiyan hijabin zuhra ta kai mata bugu da sauri zuhra ta rike hannun, nan take suka kaure da dambe abu da me hkr nan da nan zuhra ta kai jainabu kasa ta hau kanta ta fara jibgar ta kaman ta samu kayan wanki, se da zuhra ta mata jina jina kafin ta mike a kanta tana haki ta d'auki kayan ta ta ninke ta mayar ta gyara sauran kayan ta bar jainabu nan kasa tana rabka uban ihu kaman ana yanka ta, zuhra tsaki ta ja ta tada sallan isha tana idar wa ta d'auki tallan ta ta fice dandali. (Duk fa abunda sukayinnan inna bata gidan).
Inna na dawowa ta samu jainabu kwance a kasa tana ihu da sauri ta karasa tana tambayar ta me ya faru, jainabu tace "wai don kawai naje nace zuhra ta aramin kayanta na bakin saki ban wanke nawa ba shine ta rufe ni da duka, inna ki ga jikina duk ta kumbura min fuska" ta karasa da fashewa da wani sabon kukan inna ta rafka salati tare da sake ashar tana cewa "ita zuhran ce ta miki haka lallai wato yarinyar nan ta raina ni bari ta dawo wallahi se na rama miki wannan ai iskanci ne kuma tayi karya wallahi" ta inda take shiga bata nan take fita ba, karshe ma mikewa tayi ta shige dakinsu zuhran ta dauko sabon kayan ta sa wuka tayi musu pieces ta zubar a d'akin ta san in har ta kwace baffa yaga guda biyu a jikin jainabu se ya tambayeta ina ta samo, in ta fad'a kuwa duk se ransu ya b'aci kuma ya kwace ya mayar wa zuhran gwara ayi biyu babu.
Zuhra baiwar Allah tana can tana ma innar ciniki ita kuwa wadda akeyi don ita tana nan tana shirya muguntan da zata mata(Allah shi kyauta)
Zuhra ta dawo gida da wuri har ta manta abunda sukayi da jainabu d'azu, wani rashin sa'a ta dawo ta tarar baffa be dawo ba, ai kuwa tana sallama bata karasa ba taji bugu ko ta Ina da muciya da itace seda inna taga ko numfashi zuhra bata yi tukun ta d'ibo ruwa masu sanyi ta sheka mata, zabura tayi tare da sauke numfashi hawaye na gangara a idonta, inna ta fara zaginta kuma da munanan kalmomi marasa kyau a cikin zaginne take cewa, banza wadda uwarta tayi karuwanci ta haife ta don taga baza ta iya rikewa ba ta jefar, 'yar iska banza ni kuma aka had'a ni da k'aya.
Wani irin zabura zuhra tayi a take ta manta da ciwon da jikinta keyi ta ce cikin matsanancin kuka "inna kina nufin bake kika haifeni tsintata kuka yi? dan Allah inna karkice haka sbd kin tsaneni wlh ina sonki a haka, dan Allah kice ni ba shegiya bace, inna dan Allah kar ki min haka" taci gaba da sambatu tana kuka wani abun ma bata san tana fad'a ba sbd rikicewa, se lokacin inna ta dawo hankalinta ta tuna katob'arar data yi, a dai-dai nan kuma baffa yayi sallama, zabura zuhra tayi ta nufe shi tana kuka take cewa "baffa ka fad'a min gaskiya don kawai inna bata sona ne tace haka ko? Ai kaikam kaine mahaifina ko?" Baffa a take ya rud'e ya fara zufa yana ma hanse dake tsaye gefe kallon banza, zuhra na ganin expression dinshi ta gane da gaske ne kenan, nan take ta zube sumammiya.
Baffa ya kalli hanse yace "hanse ki tafi gidanku na yanke igiyar aure na dake kanki guda d'aya" ya dauki zuhra ya shige d'akinshi da ita ya bar inna na zabga ihu a tsakar gida.#vote
#share
#comment'Yar mutan Adamawa