Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
بسم الله الرحمن الرحيم
Page 41
A yau su zuhraa suka gama paper tunda suka fito hausa su keyi kowa mamaki yake jin yadda suke hausan ashe sun iya? Kunya ne sossai ya kama hauwa Ibrahim ganin yadda take zaginsu a gabansu basu ta'ba nuna mata sunaji ba da yadda tayi ta kokarin wargaza shirinsu haka kawai tabi hanya kala kala amma bata ci nasara ba.........
Suna fitowa cikin farin ciki suka nufi hanyar hostel suka ji sallama a bayansu Juyawa sukayi zuhraa tace "Aah hauwa ya kk" cikin kunya da da na sani tace "lfy klau hakuri nazo baku akan abubuwan da na muku, wlh nima ban san yadda akayi nake jin haushin ku ba haka" murmushi sukayi mata nasreen tace "ba komai ya wuce".....
Ita ma murmushin ta mayar musu tace "na gode" Juyawa sukayi suka ci gaba da tafiyarsu suna hiransu suna isa nasreen tace "laaa kun ga na manta zan kar'bi sako a gurin metron d'inmu" zuhraa tace "toh muje mu kar'bo mana" nasreen tace "nop haba nan da chan bari in kar'bo sharp sharp" Juyawa tayi ta fice ilham kuma ta cire kaya ta shige toilet........
Zuhraa wardrobe d'inta ta nufa ta zaro jacket d'in Aliyu tana jin wani yanayi a zuciyar ta tana rike da jacket d'in har ta duka kasa a kan gwiwowinta hawaye ya fara zirara a idonta tambayar kanta ta fara, ko in na koma ne za'a maida ni gidanshi? Toh me yasa be damu da ni ba? Tabbas iska na wahalar da me kayan kara, kenan ni kad'ai nake hauka na?.... .
Ya Allah, in ta tuna yana tare da matar shi suna jin d'adin su amma ita tana nan tana fama da kewarshi se taji haushin kanta tabbas da tana da iko da zuciyar ta da ta dad'e da zare shi daga cikin ranta, ko zata huta ta riga da tasan son maso wani take yi haka Allah ya so ganin ta kenan....
Dafa ta taji anyi tana Juyawa taga nasreen fad'awa jikinta tayi ta fashe da kuka sossai, hankalin nasreen ne ya tashi ta d'ago ta da wuri "zuhraa me ke damunki haka? Yanzu fa na fita na barki lfy" kukanta taci gaba da haka ilham ma ta fito suka sata a gaba suna kallo......
Se da tayi kuka me isan ta tukun iham tace "zuhraa yanzu kam in har kin d'auke mu 'yan uwa ya kamata ki fad'a mana damuwanki" nasreen ce ta katse ta da cewa "ilham ba ya kamata ba dole ne kawai in ba haka ba wallahi zuhraa na fita harkarki kenan har abada haba dan Allah mu duk wani abunda ze same su ke ke fara sani amma ke kina cikin wannan damuwan na tsawon sani na da ke me ze sa baza ki fad'a mana ba ko don rage nauyin dake zuciyarki"......
D'ago kai tayi taga nasreen da gaske take yi, ita ba wai bata son fad'a musu damuwanta bane kawai tana tsoron me ze biyo baya ne amma yau kam ko me ze faru zata fad'a musu sbd su dena jin ba dad'i in tana cikin damuwa kuma ta san halin nasreen zata aikata abunda ta fad'a.....
A hankali cikin natsuwa ta fara basu asalin labarinta daga kan tsintar ta da baffa yayi da wahalan da tasha a gurin inna da 'ya'yanta zuwa rasuwan baffa, auren da inna tayi niyyar mata zuwa yadda abun ya juye zuwa kan Aliyu da yadda sukayi da maami tana isowa nan ta tsaya tana kallonsu.....
Tunda ta fara bada labarin suka fara hawaye cikin tausayinta murmushin karfin hali tayi tukun tace "Hmmm duk abunda na lissafa mukun nan ina ga gwara shi akan halin da nake ciki yanzu, nasreen na kamu da son Aliyu tun ban san me so ba, so me tsanani da muni ban san ya zanyi ba zuciya na na cikin kunci da bakin ciki in na tuna yana chan watakila ma ya manta anyi halitta ta a duniya......
Watakila son shi ne ze yi ajalina, na san baze ta'ba sona ba har Aba........." Bakinta nasreen ta rufe tana girgiza mata kai hawaye na zuba a idonta ta ma kasa magana ba kuma a maganan ilham da kukanta ya fi na kowa se da sukayi me isan su har zuhraan ta dawo basu hakuri da kyar nasreen ta danne kukanta tace........