Page 29

3.2K 230 12
                                    

   Zuhraa❤❤
              (The flower)

By: fateemah muhammad gurin

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 29

   Suna isa FMC emergency aka wuce dashi, dama tun kafin su iso Abba ya kira zaid ya fad'a mishi so ya riga ya shirya komai, shi zaid d'in da dr. Fatima usman hadejia tare da Ammie ne suka shiga kanshi....

Basu kai one hour ba suka fito, zaid ya wuce office d'inshi haka ma dr fatima, Ammie ce ta tsaya yiwa su Abbie bayani kamar haka "ku kwantar da hankalin ku, ba wani abu bane, tension ne ya hau kanshi lokaci daya, har blood pressure d'inshi ya hau dama yana da stress a kanshi so se yayi causing fever gashi ya zo ya yi fashe fashen glass duk ya yanke hannunshi..

Za ku iya shiga akwai injections da zan had'a mishi, banda hayaniya" duk maganan data ke musun nan bata kalli ko bangaren da Abbie yake ba, kuma tana musu bayani ne a matsayin dr. Saudat isma'il sudaiz ba a matsayin Ammien da suka sani ba, ficewa tayi ta barsu baki sake...

Maami ce ta sauke numfashi kan tace "Habiby muje" Abba ya bita suka shige d'akin da Aliyu yake, Abbie kuma bayan Ammie ya bi, knocking yayi daga ciki tace "yes come in" bud'ewa yayi ya shiga, tana ganin shine ta kau da kai...

Karasawa yayi har kujeran da take ya duka kad'an tare da juyo kujerar tayi facing d'inshi, hannu ya sa ya kamo hannunta ya rike, tare da kokarin su had'a ido Amma sam taki yarda a hankali ya fara magana "kiyi hakuri" shiru tayi ya kara da cewa "am really sorry, I didn't meant to hurt yhu, nayi abunda nake gani shine right kuma na zata duk hukuncin dana yanke, akanki ko Aliyu ku masu bi ne ba tare da tambayar dalili ba"...

Hawaye ne ya gangaro mata tayi saurin katse shi "ba haka nake nufi ba nisful hayat, am just afraid, am afraid of loosing him, kasan halin Aliyu sarai in har be son abu ba karamin k'i ze wa abun ba, haka in yana son abu mahaukacin so yake wa abun, kuma kaga halin da ya shiga hawan jini fa? A age d'inshi nan?"

Abbie ne ya katse ta "na sani Noory, na sani, shiyasa nake son ki bani had'in kai ki sa shi accepting d'in auren nan, Idan har ba ke ba nasan ba wadda ya isa ya sa shi abunda be yi niyya ba, saudat dan Allah kar ki damu da halin dayake ciki yanzu, gaba zaki duba mishi, ki duba halin da yarinyar nan take ciki, kuma ki duba hankalin yarinyar nan a kankantar shekarunta, in ta fi haka fa?"....

Shiru tayi tare da d'an guntun tunani tukun ta dube shi tace "nisful hayat, bafa k'in zuhraa nake ba, ni na dauke ta kaman su nasreen ne, kar ka damu zan san yadda zanyi da Aliyu yayi accepting auren" murmushi yayi tukun yace "yauwa nooral hayati, na gode" ita ma murmushi me sanyi ta mayar mishi tare da cewa "muje mun bar su maaminsu su kad'ai" mikewa yayi ita ma ta mike, suka fice a office d'in suna 'yar hirar su.....

Suna shiga d'akin suka samu ma ya riga da ya farka, se de be ma kowa magana ba, karasawa kanshi Ammie tayi tace "Aliyu ka tashi? Ya jikin?" Shiru ya mata, zama tayi bakin gadon tukun ta sa kuka, cikin tashin hankali Aliyu ya mike ya zauna tare da kamo hannunta yace cikin rawar murya "Ammie na lafiya?  me ya faru? Don ban amsa miki ba? Toh na tashi, kuma jiki na da sauki, dan Allah ki share hawayen ki"...

Tausayinshi taji ta san in ba haka ta mishi ba, se ta sha wuya kafin yayi accepting auren, shi kuma weakness d'inshi kenan kukan Ammienshi, cikin kukan tace "yanzu Aliyu mu iyayenka bamu isa mu yanke hukunci a kanka ba? Don mun maka abunda muka ga shine dai-dai se ka hau fushi har ka jawa kanka hawan jini? Haba Aliyu hk nayi mk tarbiyya?....

Mikewa tayi kaman zata bar d'akin, saurin zare drip d'in hannunshi ya dirko daga gadon ya duk'a kan gwiwowinshi yace cikin marairaicewa "ammie dama akan wannan ne kike kuka? Dan Allah kiyi hkr bazan sake ba, inde Auren nan ne, na amince zan zauna da ita har abada, sede nima kumin Alfarma guda biyu"...

Share hawayen Ammie tayi ta d'ago shi, ta maida kan gadon ta sa cotton tana share mishi jinin tare da kokarin mayar mishi da drip d'in tukun tace "shikenan Allah ya maka albarka, me nene alfarman da kake neman?"...

Yace "dan Allah ku barta a wurinku har se ta mallaki hankalin kanta zuwa ta gama secondary ko ta fara jami'a se ta tare, sannan kuma auren ya zama sirri tsakanin mu, ko zaid ban so ya sani, ko su mama da baban yola" Ammie ta kalli Abbie ya gyad'a kai tare da cewa "hakan ma yayi, amma kana ganin zamu iya yanke hukunci a kanku ba tare da sanin iyayenmu ba?...

Abba yace "dan Allah yaya tunda ya amince, mu bar maganan sanar da su maman in yaso se lokacin tarewar tan, me Alfarma ta biyun?" Aliyu yace "duk lokacin da na samu matar da nake so zan kara aure" da sauri Ammie ta d'ago zatayi magana Abbie ya d'aga mata hannu tare da cewa "ai sunna ne karin auren, a duk lokacin da ka samu wata zaka iya auren shikenan?"

Kallon mamaki Ammie take ma Abbie ita a ganinta a nawa Aliyun yake daxe yi maganan mata biyu, he's just 30 fa, gaskiya a'a, sarai Abbie ya san musawa take son yi amma ze mata bayani yadda zata fahimta in sunje gida...

Maami ce ta katse musu tunaninsu tace "nima ina neman Alfarma plz" Abba yace "ta me fa?" Tace "ina son a barmin zuhraa a gurina, har zuwa lokacin tarewar ta, in zama mata uwa" Abbie yayi murmushi tare da cewa "wannan ba matsala bace khadija" murmushi maami ke yi na farin ciki....

Haushi ne ya kama Aliyu sbd ganin yadda maaminshi ke murna don an ce wannan yarinyar ta zauna gurinta d'an karamin tsaki yayi, tare da duban  Ammie yace "Ammie a sallame ni na warke" tayi dariya don ta d'ago jirginshi tace "maaminsu d'anki kishi yake don yaga kina murna kin samu 'ya" dariya suka saka duka, banda Aliyu da ya bone fuska yace....

"Ammie manaaaa wa ya ce miki haka?" Dariya suka kara sawa, Maami tace "kar ka damu d'ana kai ne d'an fari kuma kai ne na karshe, ba me ture maka kambunka" dariya su Abba suka sake sakawa Abbie yace "a ina din bayan kin yi wata daughter?" Aliyu ya saurin cewa "Ammie ayi discharging d'ina, pls naji sauki"...

Ammie tace "ba wani, kai de kawai kana son gocewa maganan nan ne mun gano ka, kuma se ka kwana a asibitin nan, ga magunguna nan zo ka sha" dariya duka suka sa shi kuma ya bata fuska sarai Ammie ta san ya tsani kwanan asibiti, kamar yadda ya tsani shan magani, gwara a mishi allura, cikin shagwa'ba yace "maami na kinga Ammie ko?"...

Wani dariyan suka kuma sakawa, ganin yadda ya maida fuska kaman baby, ya sani sarai kokari suke su sa shi ya sake ganin yadda fuskanshi take a had'e kaman an mishi mutuwa, shiyasa yake biye musu, haka su Ammie da Abbie suka dinga tsokananshi yayin da maami da Abba suke kare mishi, suna dariya cikin annashuwa da farin ciki...

Se chan dare Ammie ta yi discharging d'inshi suka fice tare suka nufi gida dukansu, kowa d'akinshi ya nufa yayi wanka tukun suka sake had'uwa a part d'in Ammie tare suka ci abincin dare tukun, Abbie yayi sallama ya bud'e musu taro da adu'a tukun ya fara cewa....

"Aliyu, Aida, Arfajah da nasreen ga karin 'yar uwa nan munyi muku, da ku da ita duk d'aya kuke a gurin mu, kaman yadda in ku kananan kunyi laifi manya ke hukun ta ku haka ita ma ban son inji wani abu mussaman daga ke Aida....

"Ke kuma zuhraa daga yau maami ce mahaifiyar ki a gidan nan, ki dauke ta kaman wacce ta haife ki, na yaba da tarbiyar da baffa ya miki sossai sbd natsuwar ki, banda rashin kunya kinga de duk yayyunki ne, se ki fad'a min class d'in da kike hammanku yaje ran monday yayi miki registration a school d'in su nasreen"...

Nasreen farin ciki ya kamata se murna take yi, zuhraa tayi kasa da kai tace "in shaa Allahu Abbie zaku same ni me biyayya, school kuma js 2 nake" Abbie yace "masha Allahu class d'inku ma d'aya da nasreen d'in, toh Aliyu kaji monday se kuje a mata interview kayi mata komai kan ka wuce" yace "toh" watse wa sukayi bayan Abba ya rufe musu taro da adu'a, maami ta kama hannun zuhraa sukayi side d'inta......














#vote
#comment
#share














'Yar mutan Adamawa

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now