Page 25

3.2K 222 28
                                    

  Zuhraa❤❤
           (The flower)


By: fateemah muhammad gurin
         ('Yar mutan Adamawa)


Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 25

   A firgice ta farka daga suman da tayi sbd ruwan da akayi ta watsa mata, a hankali ta fara tunano me ya faru, "inaa mafarki nayi haba baffa na be mutu ba" se tayi murmushi tare da mikewa, gani tayi mata a gidansu dayawa se kallonta sukeyi suna girgiza kai, ta dubi chubado tace "chubado lfy? Me ya faru ne haka?"..

Chubado tace "zuhraa kiyi hakuri, ki kar'bi kaddarar ki hannu bibbiyu baffa de lokacin shi yayi, musulmin kwarai aka sani da karban kaddara ki je ki mishi adu'a, Allah ya ji kanshi ya gafarta mishi" zuhraa tayi murmushi tare da cewa "a'a chubado baffa na be mutu ba, yace yana sona in har yana sona ai baze mutu ya barni ba"..

Daga gani bata cikin hayyacinta, wata mata ce makwabciyarsu ta kama ta tare da jan hannunta ta kaita gaban gawan baffa da har an suturce shi fuskan shi ne kawai a bud'e yayi fari tas fuskar a washe kaman me murmushi, tsugunnawa tayi tayi dariya tare da duban makwabciyatsun tace "kika ce ya mutu? Ba gashi ba dariya yake ba? Baffa tashi ga jauro manu nan ze sa maka magani"..

Matar ce ta jijjiga ta da karfi tare da cewa "zuhraa ki dawo hankalinki kiyi ma baffanki adu'a ya riga ya tafi baze dawo ba" wani irin kuka me tsuma zuciya zuhraa ta sake tana tasbihi ga Allah dukawa tayi ta daura kanta akan kirjin baffan tana zuba Adu'an tana kuka, duk mutanen gurin kuka suke yi sbd tausayin zuhraa sbd ita aka yi ma mutuwa, malam liman ne yayi sallama ya shigo tare da wasu maza zasu kai shidda a bayanshi, fuskan baffa ya rufe tare da daurewa yayi musu alama da su zo a dauke shi...

Kam zuhraa ta rike makaran tana cewa "baba ina zaku kaishi, dan Allah kar ku tafi min da baffa na wlh ina sonshi kuma shima yana sona, baffa ka tashi kayi musu magana kace baka mutu ba, dan Allah baffa" kuka takeyi na fitan hankali tana sambatu wani abun ma baka san me take cewa ba, chubado ne ta karaso da wasu mata da kyar suka banbare zuhraa daga jikin makaran aka fice da baffa don kaishi gidanshi na gaskiya...

A wurin ta fad'i summammiya, dogon suma tayi wadda ya tsorata mutane, se washegari da safe ta farka, tashi tayi da wani sabon kukan tana Adu'an Allah ya kawo mata d'auki don shi ne kad'ai zata dogara dashi yanzu, kafin ta mike ta rama sallollin da batayi ba tana sallah tana hawaye ta dade sossai tana yima baffa adu'a bayan idarwan ta, sallama taji daga bakin kofa da gudu ta fita ta fad'a kan wacce tayi sallaman suka saki kuka a tare...

Goggo gaaji ce ta shigo kanwar baffa da 'ya'yanta duka uku, kuka sukayi sossai mutane na basu hkr, ita goggo tana kuka ne na maraici shikenan kuma bata da kowa a duniya banda 'ya'yanta yayin da zuhraa ke kukan rashin madafa, ta san ana waste makokin baffa wtkl inna ta kore ta daga gidan...

Da kyar goggo gaaji ta rarrashi kanta tayi shiru kafin ta fara lallashin zuhraa wacce ko idonta be buduwa da kyau sbd tsabar kukan datasha, abunka da farar mace fuskan ya kumbura suntum, janta goggo gaaji tayi ta kai ta d'akin baffa nasiha sossai ta mata, se da ta ga ta natsu tukun ta sa uwani 'yarta na biyu ta kai mata ruwan wanka, wanka tayi tukun ta dawo ta zauna jugum tayi shiru...

Bayan kwana shidda

Yau ake sadakan bakwan baffa, tunda akayi mutuwan gidan ya koma shiru inna tayi mugun shiga hankalinta, sbd mutuwar ya shiga jikinta, su jainabu ma se suka zama abun tausayi..

Da kyar na gane zuhraa sbd ramar datayi se goggo ta sa ta a gaba tukun take iya cin abinci, ta rame sossai tayi zuru da ita, adu'a sossai akayiwa baffa kafin aka watse duk jama'a kowa ya tafi gidanshi bakinsu na mishi adu'an samun rahamar ubangiji...

A washegarin ranar goggo gaaji ta koma fufore, da dare ba'a bata abinci ba haka ta kwana da yunwa asuban fari taji saukan ruwan sanyi a jikinta, a firgice ta tashi ta zauna tana haki, inna ce ta fara sababi "shegiyar yarinya wato kin samu kwana bakwai ana miki aiki, bari kiyi kwanciyarki ko? Toh maza mike ki min aikin gida kiyi girki kuma ki tafi kiwo"..

Zuhraa mikewa tayi hawaye na gangara a fuskanta Allah sarki baffa na, fita tayi, tayo Alwala tayi sallah kafin ta fita, ta share gidan tas taje ta dibo ruwa ta cika randunan gidan tas tukun ta hura wuta ta dafa musu taliya jollof sbd abincin da su Abba suka ba baffa har yanzu be kare ba, dibawa tayi kafin inna ta fito taci ta koshi, tana gamawa taje tayi wanka ta fito tana duban kofan baffa, Allah sarki da yanzu ya fito yana mata sannu...

Hawaye ya gangaro a fuskan ta, da sauri ta share tare da mishi adu'a taje ta shirya tsab ta fito ta kora shanukansu ta fice daga gidan, ba wanda ya tashi a gidan...

Se chan wuraren karfe 2 ta dawo da shanukanta gida, "salamun alaikum" inji fad'ar zuhraa, "yauwa" inji inna a zuciyar zuhraa tace wato ma sallamar ma baza a iya amsa mata ba, shiga tayi ta nufi garken shanukan ta d'aure su, ta dawo tace "inna sannu da gida" inna ta sake cewa "yauwa, ga abincinki maza dauka kuma kiyi sauri kije min tallah ehe" zuhraa tace "toh na gode"..

Daukawa tayi abincin be fi loma goma ba, ga wani irin yunwar da take ji, tana ci tana hawaye har ta gama bata ji abincin ya kore ko da kwatan yunwar data ke ji ba, mikewa tayi ta d'auki tallahn don tayi azahar d'inta a jeji tambayar inna tayi na nawa ne, aka fad'a mata ta fice daga gidan...

Gidansu shatu ta shiga ta samu shatu ta shirya ita ma ta d'auki tallahn ta suka fice suna d'an hira duk da yanzu zuhraa ta koma shiru shiru...

%%%%%%%%%%%%%%

Zaune take a falonta ta harde kafa tana shan coke da aka surka da 'yan kayan maye, cross leg tayi tana karkad'a kafa, wani banzan shiga ne a jikinta a lokaci d'aya tana kallo tana danna waya..

Rukky ce ta shigo tana karkad'a keyn motan ta a hannu, tana shigowa ta samu one siter ta zauna, kafin tace "what's up babe" Ayush tayi tsaki kafin tace "wai wannan guy d'in nake kira since yesterday but he refused to pick my call"..

Rukky tace "who? Hamza?" Ayush tace "what!! Over my dead body, haba rukky se kace baki sanni ba wai, bayan rashin mutuncin daya min kuma in kira shi?" Rukky tayi dariyar su ta 'yan bariki kafin tace "oh sorry babe, major ko?"..

Ayush tace "shi fah" rukky tace "wai mai yasa, baki wuce kd kin ma shegen kof d'aya ba? Ayush tace "kul rukky mijin nawa ne shege, wlh zamu 'bata" rukky tace "sorry" Ayush ta 'bata fuska tare da cewa "kinci sa'a ke kawata ce da munyi rashin mutunci"..

Rukky tace "ba na ce sorry ba?" 'Dan tsaki Ayush ta ja tace "ina tsoron zuwa gida ne yanzu mummy taci ubana se nan da two weeks, zan roki daddy ya shawo min kanta" rukky tace "me yasa mummynku ke haka, bayan a ido kaman wayayyiya ce"..

Ayush tace "hmm bar matannan tana shiga min hanci da kudunduni wlh" (wa'iyazubillah Allah ka tsare mana iyayenmu, wai uwa ce ake cewa hk)..

Hiransu sukeyi cikin kwanciyar hankali kafin su Afrey suka shigo, ihu suka sa tare da mikewa su ka kunna home theater suka fara dirkar rawar su ta batsa..

%%%%%%%%%%%%%%

"Kin san Allah ko kina so ko baki so wani satin za'a daura aurenki da ibi, bari kiji in gayamiki dama malam nake shakka toh yanzu baya nan" inna ce ke wad'annan maganganu a lokaci d'aya tana zungure kan zuhraan..

Zuhraa na kuka tace "dan Allah inna kiyi hakuri, ki aura min kowa amma banda ibi, inna duk garinnan ba wadda be san d'an iska bane ba" mari inna ta wanka mata tare da cewa "mijin naki kike kira d'an iska, toh ki rubuta ki ajiye wani juma'an war haka kina gidanshi, kuma ki yi maza ki 'bace min a gaba, kije ki same shi yana waje yana jiranki, kuma inji kin mishi rashin kunya kiga yadda zan mai dake a gidannan" mikewa zuhraa tayi ta fice tana kuka ta nufi waje....










•toh fah readers auren zuhraa next week friday, kuma da ibi.

Ko ya abun ze kasance?
Ina labarin jikin Ammie?

Ko Ayush zata ci nasarar auran Aliyu?

Ku biyo ni kuji yadda abun zai kasance, luv yhaa all 😘•












#vote
#comment
#share

Taku har kullum fateemah muhammad gurin












'Yar mutan Adamawa 😍

Zuhraa❤❤Where stories live. Discover now