page 33

3.4K 308 28
                                    

   Zuhraa❤❤
              (The flower)


By: fateemah muhammad gurin
         ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم         

Page 33

          Wasa wasa kwanaki suna Juyawa suna komawa sattittika, sattittika na komawa watanni, yau watannin zuhraa goma sha d'aya da sati biyu a gidan, tayi wani irin kyau fatan ta ya wani irin murjewa ta kara tsawo....

Yau saura sati biyu bukinsu gidan ya fara cika da mutane 'yan uwa na nesa da kusa 'yan uwan su maami daga katsina sune cike da part d'in maami a ta bangaren Ammie kuma kannen mamanta ne kawai suka samu zuwa su uku, zuhraa ce ke saukowa daga stairs cikin jallabiya black color me adon milk da gyalen shi milk....

Taci kwalliya sbd zuhraa akwai son makeup kuma maami ta saka su ita da nasreen makeup class na 6months har sun gama, simple make up tayi tayi kyau sossai, tana karasa saukowa tayi part d'in Ammie direct d'akin nasreen ta shige ta samu ita ma ta gama shiri cikin jallabiyanta red colour ita ma tayi kyau sossai a tare suka fice zuwa d'akin Ammie....

Ammie da maami suka samu da alamu magana me muhimmanci suke tattaunawa a tare suka ce "Ammie, maami mun tafi" Ammie tace "gashi zo ki kar'ba ku kaiwa maman" wani abu ne a cikin paper bag ni de bansan me bane, maami kuma tace "se kun dawo" suka fice suna hiransu na kawaye... 

A parking space suka taka birki nasreen tace "cutie za'ba mana motan da zamu fita cikin shi" wani farin Mercedes Benz ta zaba, nasreen ta zare ido tare da cewa "ke!! baki san motar hamma bne? Chanza maza kafin yanzu ya taka ruwan cikinmu"...

Zuhraa tace "kai angel ina baya nan ina ze ganmu bari ki gani" gurin Emmanuel ta nufa shine in charge of duk wani abu na Aliyu a gidan ta ce mishi "ema Ammie send me to yhu she said yhu should give me that car key" yace "which one?" Tace "Mercedes Benz c350" zaro keyn yayi ya bata.....

Juyawa tayi gurin driver d'insu tace "babana muje ka kaimu anguwa" yace "an gama 'yata muje" driver d'in 'yan matan kenan dattijo me kamala da mutunci sunan shi buba shi yasa zuhraa ke ce mishi babanta, kar'ban keyn yayi suka shige baya ya ja da niyyar fita daga gidan......

Siren sukaji daga kusa kusa se kuma suka ga an bud'e get da mugun gudu motocinshi suka shigo gidan guda hud'u wani irin mahaukacin parking suka yi, tare da fitowa da gudu suka zagaye motar da yake ciki d'aya daga cikinsu ne ya bud'e mishi kofa, sauko da kafanshi yayi cikin takalmin sojoji black colour se kuma kafafuwanshi suka fito tare da jikinshi gabad'aya.....

"Ya Allah" shine abunda zuhraa ta furta a kasan makoshi sanye yake da wandonsu na uniform se farin top ya kama shi duk wani muscles d'inshi ya fito na maza majiya karfi hannunshi na sanye da Rolex watch gashin kanshi ya sha gyara, yana fitowa idonshi ya fad'a nata da ita ma shi take kallo a tare zuciyarsu ta buga.......

Shi a bangaren shi mamaki yake yi dama yarinyar nan na nan? Shi ya manta when last ya ganta in fact ya ma manta da ita se yanzu da ya ganta, yaga ta kara girma da kyau, ita ce ta fara kau da idonta daga kanshi zuciyar ta kaman ze fashe, tana jin wani abu na dragging d'inta zuwa gare shi kamar taje ta rungume kayanta.....

Nasreen ce ta katse mishi kallon kurillan da yake mata ta hanyar rungume shi tace "I really miss yhu bro, ka jima baka zo ba" d'ago ta yayi tare da cewa "miss yhu too angel, ba muna waya ba?" Tace "ai waya daban hamma" murmushi yayi a sama yaji siririyar muryarta tana cewa "welcome home hamma" wani abu yaji ya tsarga mishi daga kanshi har tafin kafanshi.....

Ya tsinci kanshi da kasa amsa mata kai kawai ya d'aga mata, ita kuma ta kau da kai tare da turo d'an karamin bakinta tana masifa ita kad'ai a zuciyar ta, wlh ita ba don nasreen ta fito ba da ba fitowan da zata yi yazo yana wani gyad'a mata kai kaman kadangare tare da murgud'a baki....

Zuhraa❤❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora