Zuhraa❤❤
(The flower)By: fateemah muhammad gurin
('Yar mutan Adamawa)Wattpad: muhdfatimagurin
*This is for yhu sweetheart #Ameeratuh heart yhu soo much😍*بسم الله الرحمن الرحيم
Page 31
Monday morningGangarawa take da gudu gudu, sauri sauri, daga kan stairs, sanye take da jallabiya red colour tayi rolling kanta da gyalen rigan, powder ne kawai a fuskanta se lip gloss, maami ce a bayanta, tana cewa "baby a hasititta?"(baza ki karya ba)...
Zuhraa da ta kai tsakiyar parlorn tace "maami mi hasitan ha school, nasreen 'yen d'o rena mi, ha yasi nda o vi hamma yid'a renugo" (zan karya a makaranta, su nasreen suna jira na a waje, gashi tace hamma be son jira)...
Kafin maami ta kara wani magana zuhraa ta bar parlorn, girgiza kai kawai tayi ta koma sama don ta karasa shirin fita aiki, don ta koma bakin aikinta a FUTY...
Tana fita taga black picnic ana worming d'inta ta tabbatar a ciki su nasreen suke don shine kad'ai a tsakar gidan, bud'e baya tayi ta shige, cikin sanyin muryanta tace "sorry na sa ku latti" murmushi nasreen da arfa suka mata Aida kuwa harara ta buga mata...
Duk tsoron magana suke yi sbd Aliyu da ke zaune a driving sit, be kalli kowa ba ya tada motar tare da ficewa da gudu sbd a cike yake, ya tsani jira amma wai shine ya zauna zaman jiran wannan yarinyar, hmm darajar Abbie taci wlh, duk shi kad'ai yake zancen shi a zuciyarshi....
Minti kad'an ya kai su AUN secondary section d'in suka shige ya samu parking lot yayi parking, dalibai se shawagi suke, suna sauka wasu 'yan mata da alamu 'yan ss3 ne suka had'a baki wajen cewa "Woww" wata a cikinsu tace "pretty kuna ganin abinda nake gani? Amma guy d'inan ya hadu".....
Ba wadda ya amsa ta, juyawa tayi taga kowa ya sake baki yana kallon shi, wasu gungun 'yan ss2 ma hk suka tsaya gulman Aliyu, a hankali zuhraa ta juya tana kallonshi, itama so take taga abunda ake wa wannan santin.....
"Innalillahi" shine abunda ta ambata ba wai don kyaun shi ba, sbd kayan dake jikinshi, a take wani irin tsoronshi ya shige ta what!! Soja? Na shiga uku soja aka auramin? Abunda take fad'a a zuciyar ta kenan A take idonta ya cika da hawaye, ta tsinci kanta da kasa dena kallonshi...
Tuni su nasreen sun wuce, sbd yanzu be game shi ba ya dizga su a gaban mutane, Idan suka ce zasu tsaya jiran zuhraa, ta bangaren shi kuwa ya tsaya ne don ya d'an bata yuwa sbd sashi jira da tayi amma se ya ga kanshi yake 'bata wa lokaci sbd yadda 'yan mata suka kafe shi da idanu se kace sunga wani bakon hallita...
"Mtseww" tsaki yaja tare da daga ido ya kalle ta, blue eyes d'inshi da brown oily eyes d'inta da ya cika da hawaye ne suka sarke da juna wadda yayi sanadiyar fad'uwar gabansu a lokaci d'aya, a hankali hawayen idonta suka gangaro, tayi saurin kau da kanta tana share hawayen ta...
A kasalance shima ya dauke idonshi daga kanta yana kara jan wani tsakin, toh me ya sata kuka kuma? Wani karamin tsaki ya sake ja, toh ma shi ina ruwanshi? Juyawa yayi ya fara tafiya da kyar ya ce mata "follow me"...
Office d'in principal na makarantan suka shige, wani baturen mutum ne a zaune a kujeran gurin yana jujjuyawa, ganin su ne yasa shi mikewa sbd girmamawa tare da mikawa Aliyu hannu "yhu r wlcm sir, pls hv a sit" zama Aliyu yayi, ba tare da yace komai ba...
Principal d'inne ya kara magana "how can I help yhu?" Aliyu yayi gyaran murya kafin ya fara magana cikin karyayyen turanchinshi "I came with her for interview exam into js2"...