Page 40

3.6K 228 14
                                    

 Zuhraa❤❤
          (The flower)    


By: fateemah muhammad gurin
        ('Yar mutan Adamawa)

Wattpad: muhdfatimagurin

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 40

     Zaune yake a kasa duk sanyin garin na sauka a kanshi ya takure sossai a gefen gado ya had'a kai da gwiwa yayi zurfi sossai cikin tunani yana jin kewar abubuwa dayawa amma ya rasa na me, zuciyarshi na cikin kunci da maraici yana ji kamar be da kowa a duniya......

Be san lokacin da hawaye ya fara gangaro mishi ba ji yayi an kunna wutar d'akin se da ya share hawayen fuskan shi tukun ya d'ago ya zuba mata ido sanye take cikin jeans da shirt d'amammu sossai suka fito da suran jikinta kanta ba d'ankwali se uban attach da ya zubo har kan d'uwawunta......

Tafiya take cikin tangad'i ta fad'a kan gado, kallon ta yakeyi har ta fad'a kan gadon mamaki yake yi me ya gani a jikin wannan har ya aure ta, yana jin haushin shigan jikinta a matsayinta na matar aure kuma musulma, ya rasa yadda ze yi da ita tunda suka zo garin ta fara nuna mishi asalin halayenta......

Ita ce shaye shaye, friends d'inta duk maza in ta fita se tsakar dare zata dawo, gashi komai shi ze ma kanshi kullum yana hanyar restaurant ga kayan abinci ya saya ya tara amma be ga amfaninsu ba, komar da kanshi yayi tsakanin cinyoyinshi ya ci gaba da tunaninshi dayaga baze amfane shi da komai ba ya tashi ya d'auro alwala ya fara nafila........

*******

                  2 years later

Sossai rayuwa ke tafiya mata yadda take so, sam be tanka ta tayi abunda ta ga dama se de abunda ta rasa soyayya da kulawar shi kullum yana nan jugum ran nan a had'e zata yi abunda ta ga dama amma be d'aukar ta raina shi ko ta fad'a mishi maganan banza......

Yau ma kamar kullum ya shigo gidan yana parking mota ita kuma ta fito zata fita gabannin magrib duk da holland ze yi wuya ka samu massallaci kusa ko kaji kiran sallah sede ka kiyasta time kallon time yayi ya d'ago ya kalli jikinta.......

Bud'e motar yayi tare da kiran sunanta "Aisha ina zaki hk da wannan dressing?" 'Bata fuska tayi tare da jan karamin tsaki a ranta take cewa yau abun ya motsa kenan wlh wannan d'an rainin hankalin yana ja min asara, duk da bata samu yadda take so na ta juya shi se abunda tace ba amma ta d'an samu sassauci daga wasu halayenshi amma kwana biyu se aiki ya 'baci kullum tana kan turawa rukks kud'i ana zuwa gurin boka.........

Wani tsakin ta ja jin tsawar da ya daka mata "ke ba da ke nake ba? Ina zaki da wannan shigan kuma da magariban nan?" Ai kuwa yana jin tsakin ya sa hannu ya buge bakin, rike bakin tayi tare da raurau da ido tace "dan Allah me shigan nan yayi?"..... 

Wando ne three quarter d'amamme a jikinta se shirt me tsiririn hannu wadda in ta d'aga hannu ba abunda ze hana cibiyar ta bayyana se ta d'auko wani yaloluwar riga kaman jacket wadda ya kai mata har dunduniya ta baya amma ta gaba ba abunda ya rufe, ta sha attach a kan nan har gadon baya da wani uban hill a kafanta.......

"Ba inda zaki je wuce ciki" cikin kuka tace "pls baby bazan dad'e ba I promise" ba tare da ya ce mata komai ba ya kar'be keyn hannunta yayi shigewarshi ciki, cikin takaici ta juya ta koma ciki don tayi da boyfriend d'inta zasu had'u a wani hotel amma gayen nan ya hanata gunguni ta fara da ba don har yanzu yana da kud'inshi da kyaushi ba kuma duk samarin da tayi bata ji wadda yake gamsar da ita kaman shi ba da ta dad'e da rabuwa dashi......

D'akinta ta shige tare da kashe wayan ta fad'a kan gado bata kai minti goma da kwanciya ba ya shigo daga bakin kofa yace "Aisha had'o min dinner" ya juya yayi ficewar shi wani irin tsaki ta ja tare da jawo wayanta ta kunna tayi ma rukks transfern kud'i tukun ta Kira ta tana d'agawa tace "plz rukks ki koma min gurin na kan tudu aiki ya 'baci".......

Zuhraa❤❤Donde viven las historias. Descúbrelo ahora