chapter 1

29.8K 1.4K 178
                                    

Page 1
_the HORN OF AFRICA_



This is how our bahiyyah looks like!

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

This is how our bahiyyah looks like!

Misalin karfe 6 na safe ne,Juyi nake ina kikkiftawa salon kwace baccin gajiyar da har yanzu yake bibiyan idanu na.

"Yau ma Daga inda nafi kwanciya a chan dungun daki na tattaro karfi na duka nayi mika don na watseke,da kyar na waro idanuna  dan kuwa Bibbiyu nake gani har wani jiri ke deba na,hakan kuwa bai hana ni daddagewa na zauna tsam ina muzurai ba sai dai duk da haka idanuna sunyi dishi dishi kamar wata mai kallon gajimare.
sanda na dauki mintuna uku da hannun dama na ina yarfe su kafin suka dawo min normal sai dai har yanzu  Basu nuna min abbu na ba.

'Wani irin faduwar gaba ne ya taso min"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na furta acikin zuciya na.Wani mugun fargaba ne naji ya rufe ni atake,a hujajan na mike tsaye ina dube dube dan bansan sanda sanyin sautin murya na ya fidda sautin sunan sa ba'..cike da damuwa na fito ina cewa
ABBUH...!

...jiya cikin dare Abbu ne akwance kusa dani kamar gawar da yaki kabarin sa.

Dan Daga ni har shi bansan ya akayi safiyan yau ta riske mu ba.

duba shi na shigayi sai dai ina dora kafata bakin dakin daya raba jingar karar dake tsakar gida sai na hango rayawar karan masara har an sakaye kofar bayi dashi alama nacewa da mutum aciki yana zagaye.

'Bayin nadan bi da ido na dan wani lokaci domin na tabbatar ko shine aciki,bayan kamar minti biyu nayi ajiyan zuciyan tare da sauke boyayyen nishi nan na juya na koma cikin dakin dana fito.

"...Yagaggen Tabarman kajinjinin dabinon da muke kwana akai na dora hannu na akai na jawo shi batare da na nade ba na karkade duk kasan dake kai na fito dashi waje.

A jikin dangar kara daya suturce mana asirin jimammiyar muhallin mu na tsaya,sanda na zare kararen da suka rage mana na hura wuta sannan na yarfa tabarman akai na juyo tsakar gida.

Daga nan A Gaban wata dakilalliyar ramin murhu nayi tsugune,Hura wuta na shiga yi da gaske domin sanyin safiyar mu  ta sha banban dana kowa a yankin mu.

"Sunana Bahiyyah Ahmadu Alba.
ni Bansan daga ina muka fito ba bare nace na san asalin mu amma yanzu haka a wata katafaren yankin jeji mai tsananin sanyi da duhun itacuwa muke zaune nida iyaye na da jinsin zuriar wasu fulani wanda su ba bakake ba kuma su ba farare ba.
 
Nan din Yanki ne
Daya tsaga tsinin kahon nahiyar africa,Kenan mu ba acikin wata kasa muke ba.

A cikin kasashen afurka da suke zageye damu kuwa sun hada da ethiopia,somalia,djoubuti da cibiyar bahohin ruwa guda biyu wato quardafui da somalian sea,sai kasar kenya dake gudu maso gabas.

Shiyasa ma idan anka duba yankin mu da kyau sai inaga kamar muna cikin wani tsauni ne a chan Cikin dajin daya ya raba gulf of eden da kuma bahar maliyar(red sea).

Tsawon shekaru na a duniya na dauka acikin wannan yanki aka haife ni,Sai dai nasha mamaki sosai a lokacin da ammu wato mahaifiya ta tazo gaban ta na mutuwa.

AHUMAGGAHWhere stories live. Discover now