chapter 20

10.9K 1.1K 382
                                    

_2⃣0⃣-the venom♡_

Tun Tana daga serving spoon ya dakatar da ita ya amsa yana cewa let me have this..
A sanyaye ta sake mashi tana bin shi da kallo dan maganan kawai yayi amma bai wani kalle ta ba.

Bowl din Abincin ya sauke kasa ya aje  kan lallausan chinesee rug carpet,a hankali taja mashi center table din gefe dakyau sai yace mata sit ta zauna,Serving Plates guda biyu ta jera amma da guda yayi amfani a nitse har yayi serving din su,kallon shi take satan yi but to avoid being cought sai ta yi kokari ta shiga zuba musu smothie a two cups kowa da nashi

Wani shiru Wajen ya dauka da suka fara cin abincin,its feels like heaven dan yayi kewar abincin ta sosai,shikam babu wani alaman jin kunyar ta dayakeyi dan cin abincin shi yake yi normally itace inta kai loma daya sai ta dan jira kafin ta kai na biyu.

A farkon wanda ya zuba musu ya kare sai ta dada kara musu Taga gogan bai dakata ba har suka ci abincin sau biyu..Dan kadan ya rage sai ya jawo smoothie din ya kai bakin sa..,itama dan tura abincin gefe ta yi niyyar yi ya wani balla mata harara bai ce komai ba

Bata daddara ba ta dan tura kadan,zata aje spoon yace"eat up"..duka zaki cinye..wani yamutsa fuska tayi cikin sautin shagwaba tace nifa na koshi ne..

Bai kula ba ya tura mata abincin ya dada balla mata harara,"u most eat all of it,baki da ido?baki ga kin rame ba?kaiwa nan ya kau dakai ya cigaba dashan abunsa shiru.

dan shirun itama tayi tana kallon sa a sanyaye ta jawo plates din ta tuttuura sauran abincin acikin ta badon taso ba,sai da taji tayi dam har ta kasa mikewa.

Shikuwa Tashi yayi da cup din a hannun sa ya koma kan cushion ta mike kenan xata tattara plates din ya mata nuni da remote akan ta miko masa

kallo ya kunna ya hakimce,nan taje kitchen ta gama tsaftace ko ina ta goge wajen tsaf..

A hankali ta bude door Tana dan lekowa suna hade ido
,sai yadan kau dai ba yabo ba fallasa yace fatan kinyi sallah?

Ta danyi shiru sai shima yayi shiru cos baisan ko ya dace ya mata tambayar ko bai dace ba

Doguwar Rigar material ne dama ajikin ta fari mai manyan rose flower pattern,a sadade ta wuce shi ta shiga bathrum ta wanke hannu da fuskan ta tsaf sannan tayi tsarki tayi alwala,data fito kallo daya yabita da shi,batare da yace uffan ba sai yaga ta canko in da direction din gabar ta tsaya, dan hair scarf din tan ta dada lullubawa akanta ta tada sallahn azahar.

Toh Dama karfe uku na yamma ya dan wuce Almost 10minutes tana zaune a position din da niyyar jiran lokaci dan ta hada da laasar,tunanin yaushe ne ya dace itama ta fada mashi zata tafi?

Sai yanzu ma tafara tunanin nashi tafiyar,she just dont know why he dint say anything again

Daf lokacin sallahn ya mike tsaye shima Tana gani ya nufi bathrum din a lokacin ta fara nitso cikin tunani kala kala ciki kuwa harda tunanin yadda zata fayyace masa abubuwan dake faruwa tsakanin ta da sadaat da big sis subaya.

But its becoming hard a zuciyar ta,sosai abubuwa daya na waswasi suke shigowa,bayan su dija da suka san komai kuma suke ganin komai bata tunanin akwai wanda zai yarda cewa sadat na mata  haka.

"...game da maganan sirrin dake makale da auren sadat da subaya kuma bata san ya khal zai dauke maganan ba"...

,banda yau counting as an unsual moment har cikin ranta bata taba tunanin khaldun dakansa zaizo inda take ba bare har ya bata lokacin sa haka ba.

Ahaka ma Ita sam Bata san me nufin sa ba,yazo musamman dan ita  kanwar sace koko wani dalili yasa shi ya waiwaye ta?

taga yana tausaya mata kuma ya biye mata fiye da yadda ya saba da chan amma ko kadan bata aminta da komai daga gare shi ba.

AHUMAGGAHWhere stories live. Discover now