_Monday/11/019_
_3⃣5⃣-Tort♡._Bayan angama case a kotu atare suka dawo gidan gaba dayan su da sharadin bazasu bude maganan ma kowa.
Jikin kaaamil nee ya tsanan ta,da alaman high fever ke damun shi dan babu abunda yake yi sai surutai yana kiraye kirayen sunan bahiyya.
Fannin jahan khatun kuwa Banda bacin ran halin da kaamil yake ciki ji take kamar zatayi hauka jin ance jahan Aarah ta iso gidan..
Sukam da suka iso gidan a site din su hjy indirah suka yada da zango,.
Khaldun dake jin kanshi daban yau duk sai ya rasa ta inda zai fara gyaro ta da bahiyyar sa,hira kadan yayi da su ya fice baima san meke faruwa a fannin su kaamil ba..
bayan fitar sa,jahan Aarah tace ma subaya kuje ku huta,nima zanzo namu shashin daga baya...ba laifi suka bar wajen su ukun bahiyya ta mata jagora har zuwa site din ta ant murja na biye da su suna ta hirar su abun sha'awa..
Acikin sirri jahan Aarah ta gaya ma hjy indirah duk abunda ake ciki,jiman tawa take yi sosai tana jin mamakin halin kirki irin na bahiyya sai ga alhaj hamood ya shigo..yayi musu sallama yace Aara,ashe kaamil ba lpya..yakamata muje ku duba shi
.. dama ita kam bataje ta gaishe da dilshad ba,jin ance kaamil na kwance yasa suka debe jiki ita da hjy indiran suka nufi wajen san atake..
Sarauniya Dilshad da ahalin ta duka suna cikin dakin..
Daga yin sallamar su jahan Aarah tuni iskan wajen ya sauya tsari,Wani kallon banza aka watsa ma juna
kasan ido jahan Khatun ke duban su daya bayan daya acikin wuya take ansa gaisuwar jahan Aarah..
Jahn Aarah tayi kamar bata san ma tanayi ba ta haishe da sarauniya dilshad bayabo ba fallasa ta amsa tana mata sannu da zuwa..
"Kaaamil?...Ya jikin ka...Very soft nd calm take shafa kanshi tana duban shi da kulawa..,har cikin ranta take kaunar sa as much as yadda take son danta saood,jikin sa yayi zafi sosai har jira ake yadan sassauta kafin doc ya shigo ya masa Allura..hjy indirah tace meke da munshi babu wanda ya ansa ta atake ta juya ta sauke haushin hakan akan su hilda da junnut da suka ki ficewa su basu wuri..
Tace wai ku bakusan manyan ku ba?..maza ku fice ku bamu wuri..Tsuliya azage suka fita sum sum kamar yan matan bin kida basu ma gaida kowa ba.
Tuni Jahan K ta bata ranta ta fara kukuni,tace ciwon maita aka laka mashi,...
ina zaman zaman na ankawo ni wata kasa marar dadi daga yau wannan yaxo maka gida sai gobe wannan yazo..rabon kaamil da yayi ciwo yana kame kamen suna tun da chan da aka saka min ido a persia..ko Mena tsare ma mutane oho
Har ta gama mitan ta babu wanda ya daga kai ya dube ta
hjiya indirah ta budi baki kenan alhaj hamood yayi gyaran murya cikin nitsuwa yayi maganan sa...jahan Aarah kam duk hankalin ta nakan kaamil don batace musu uffan ba matar tana da tausayi sosai..Jahan khatun kuwa ba dan jan numfashi sai ta shiga fetsa magana tana cewa mayya aka kawo gidan ta...ita so take a kore bahiyya ta ko sa ma ta bar mata gida..tun abun na wasa har maganan dai ya dawo babba awajen hjy indirah
Ranta ya baci bataji dadi ba, .tace way shin wacece mayyar,?bahiyyan ce mayya koko wata daban?..ai naga duk yaran ki ne agidan nan,cin maita kuma ai sai tsoffi...
Sarauniya dilshad ta kalle hjy indirah da wani irin sigar baraxana..bata kula ta ba itama ta bata rai abun taalhj cikin rashin jin dadi yace dan Allah ya isa hakan nan abubuwa dayawa ne agaban mu
...da yaren su na persians dilshad Tace mashi ai tunda kaamil ya kwanta ba abunda yake cewa sai bahiyyya...
Yaya baza ace da ita mayya ba?
YOU ARE READING
AHUMAGGAH
Historical Fiction"Never let your best friend become your enemy"...that was my abbus last words before he left the world.Am a perfect girl,with a perfect heart i secrifice alot witout expecting returns.In this world they are two main life directors,the push or pull f...