_♡7⃣sempa fidelis_
Da safe na dade akan gado na kafin na sauko,wanka na shiga zuciya ta cike da mamakin abunda yayi jiya.
Ina gama shiryawa na fito na wuce kitchen Na girka masa abinci,bai amsa gaisuwa ta ba bare yace min ya jiki,kuma tun Ina jera mashi abincin ya kore ni ko bari nayi serving dinshi ba baiyi.
Haka rayuwata ta kasance like a living hell,ban isa bayi ignoring duties dina ba amma innaje inayi kuma baya kyalewa na karasa sai ya korani
Duk sai naji nagaji da ibadan,haka Nayi ta sa kunne ko zanji ance zamu tafi gida amma shiru har muka cinye kwana takwas
Kullum inna zauna sai na tuno kano
I seriously missed ammuh adama ita kadai ce nake tunanin zata warware min duk wani matsala ta,.haka nayi ta zaman hakuri ban tashi jin meke faruwa ba kuwa sai da najiyo shi yana waya.
Ashe cewa sukayi ya sake saka musu lokaci wanda hakan ne ya jawo delay din tafiyar mu.
Aranar Cikin dare su kayi meeting dinsu,it was very successful komai ya tafi mashi dai dai.
Da safiyar Allah kuwa ko wanke ido banyi ba yasa aka tarkato ni da kaya na na shiga mota akan zamu koma kano
Tsaban iya shege shi sai yabi private jet dinsa nikuma yasa aka bi mota dani
Kusan tafiyar kwana biyu ana jan mu,banda yawan bacci ba abunda nake yi a motar har muka iso kano
Muna isowa naje na gaida jahan Aarah cikin sauki bata ce min komai ba har na fito.
Wajen Ammu adama naje,muka gaisa tana kallo na tace baaahi?..Meye faru ne naga kamar kin fada...
Nace banji dadi bane amma na warke.
Taje ayyah,Allah ya baki lpya khaldun ya sanda haka kuwa?
Ko da shike ma naga kamar tun shekaran jiya shi ya dawo me kuka tsaya yi to?Nan na shiga bata labarin abunda ya wakana ina maganan bansan ma hawaye na sauko min ba
Kunya yasa Ban dai gaya mata abunda ya faru akan period baNace sabida ni yayi kusan buga kansa ko meeting din ma adalili na aka daga har muka ja lokaci..
Ammu Adama Ta ji tausayi na sosai ita da shike ta fahimce mmbi sosai ko fadan ma bata min ba
Tace muje ki huta kici abinci,kafin anjima kije ki gyara mashi site dinsa kinga tunda baki gidan nan ba wanda yaje ta wajen
Ban yo musu ba,hakan kuwa ya faru ammu ta gama petting dina nayi wanka na huta
Chan anjima naf shirya naje site dinsa na shiga kimtsawa fiye smda kwana biyar bamu nan nayi aiki sosai sai dana gaji.
A Kitchen dinsa na tsaya na jira domin na mashi abincin dare mai gaba daya,koda nagama nayi serving dinshi baiko kalle ni ba yace min get lost
Dama nikam nagaji dan haka da murna na bashi waje,sai dai ko karasa isa site dina banyi ba ba sai ga aikan sa akan cewa naje na karbi kayan da aka shigo dashi yanzun na jera masa a closet kafin yayi bacci
Haka na koma na karbe tarin kayan nasa,wasu irin super huge designer shopping bags ne mai dauke da designers shoes perfs,watches and other clothings.
Zama nayi anitse ina jera su,ina kuma binsu da kallon sha'awa ,Allah kadai yasan yaushe za'a saka su dan anan dinma akwai kaya da uban yawa wanda ko taba shi baiyi ba.
Bayan kwana biyu ranar na tashi da safe sai naga ko ina agidan ya cike da motoci anata sharing plesantries da formalites.
I was surprised na fito inata raba idanu, koda naje dakin gogan nawa ma yau a kulle take kuma shima baya ciki.

YOU ARE READING
AHUMAGGAH
Historical Fiction"Never let your best friend become your enemy"...that was my abbus last words before he left the world.Am a perfect girl,with a perfect heart i secrifice alot witout expecting returns.In this world they are two main life directors,the push or pull f...