chapter37

13.3K 1K 263
                                    


_3⃣7⃣-Brave heart♡._

Jahan Aarah ta dake tana ci gaba da masa mugun kallo tace "akan wani dalili?" Ya dago kai yana kallonta xai yi magana ta rigasa tana girgixa kai tace "to ban amince ba, in kuma ban isa da kai ba sai ka nuna min yanxun nan in ga,Aaban,fita ka ban waje"

kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata,a dan fusace tace"to ko dukana xaka yi irin wanann kallo haka, ban da ka raina mutane meye dalilin ka da yin auren nan ina shirme ba,salon ka ja min magana a gari yarinya karama na zaman ta lafya ka tashi ka ce xaka azabtar da ita?

abokiyar xamar da kuke shirin kawo maka wato kenan ku hadu kuyi ta cutan ta ko, to baka isa ba kayi kadan, in kanwarka aka yi ma haka ai ba zaka ji dadi, plss leave"...khaldun ya kuma sunkuyar da kansa kamar karamin yaron mwi shirin yin kuka yace

"to amma mama naga da amincewar ta a farko kuma wannan abun naga ba haramun bane bare ace rabuwar shi yafi..

..."Wani tsawalellen kallo ta banka masa,wa ni xaka kawo ma wanann maganar? Dan kaga ban yi fushi dakai da kake sata dole ta amsa ba Kana wasa da nine?
Toh in ka isa ka je kayi zaman auren nan muga, get out in daina ganin ka a dakina, baka tunani kawai"

Wani kasalan xuci zancen nata ke dago masa, a lalace ya tabe baki mikewa  yayi yana shafa kansa bai kuma cewa komai ba ya nufi kofa kamar zai fita..

Alhj hamood ne ya shigo dakin yana ma jahan mugun kallo sigar zolaya yace"sannu, kin yi kokari..wato kamar yanda ki ka hanani ni yi ma mijin subaya ta hukunci,shine da na ma xaki hanasa abunda yake so?

Anan kam baki isa ba,gyaran auren sa babu fashi ni nayi wanann alkawarin"

Khaldun dake rabe agefen shi yayi murmushi jin dadin wannan kalma yace " A'a dad abun bai kai ga haka ba, tunda mama bata so kawai ni na fasa bana son abun da xai bata ran Sarauniya ta,a bar maganar auren kawai har sai ta amince"wani kallon banza Alhj hammod ya ke masa yace "sannu me uwa,

wato ni xaka watsa ma kasa a ido na zo tare maka bakin rai koh,yayi maka kyau..

ficewa Alhj hamood yayi daga dakin, Khal yayi murmushi ya dawo kusa da jahan dinsa dake zaune ko kallon inda mai gidan ta yayi bata yi ba.

Cike da sanyin jiki ya durkusa kusa da ita a hankali ya fara magana

"mamah, kiyi hakuri idan na bata maki wllh na bar batun auren tunda ba ki so,kila hakan ne yafi min alkhairi,ki kwantar da hankalin ki na rufe zancen daga nan wllh"

jahan ta dago tana kallonsa shikadai yasa ta ina zai iya sace xuciyar ta tace

"Ka turo min bahiyyar gobe sai in ji ko da gasken da amincewar ta tin farko dakake fada. in tace ehh,to baxan hanaka zaman auren ka ba tunda nima ga abinda uban ka ke cewa a kaina,in kuma tace bata san da zancen ba to ko me zai faru baza ka cigaba da xaman auren dole da yata ba..noor ta sha wahala sam baku da tausayi wallhy"

Khal ya girgixa mata kai yace"No mum ni na bar maganar in har ranki bai kwanta akai ba" .

Jin kansa kawai tayi akan cinyar ta yana mai sauke wasu nannuyan ajiyan zuciya kamar mai shirin fitar da kalmomi masu nauyin gaske daga zuciyar shi....

Mum...i want the marriage.

I know,abunda nayi ban kyauta ba,but i do care about he...rrr.. I swear...

Kuma Kinga sai inkin amince zan iya cigaba da zaman aure da ita..

Nidai Pls ki duba ki gani i wont repeat such mistakes..im sorryy ummah..

Yadda ya karasa maganan hwanin tausayi yana wani nokewa cikin maraice murya,yasa gaba daya jikin jahan yayi sanyi

jahan tace "ni ka tashi ka ban waje kayi abinda nace maka bana son dogon magana" ya dan Marairaice mata yace "wai  fushi kika yi da ni, wallhy har xuciyata na fada maki bazan karaba..mum kar ki raba auren nan"

AHUMAGGAHWhere stories live. Discover now