_page2:The cross roads_
Wasu suna ban haushi seriously,kaga labari ya maka kana so kabi to meyasa bazaka karanta shi yadda ya dace ba,?dont jump some part just to come and ask me whats he meaning of ahumaggah nayi full describtion din sa a first chapter,read it all if u wanna be in the crew amma gaskiya bazan juri silly queations da maida min aiki baya ba thanks as u comply
Cikin daren A daddafe muka iso gida,samu mukayi abbu ya riga ya dauke motsi amma kuma numfashin sa bai dauke ba.
A gefe na ajiye maganin sa duka muka zube gwiwar mu agaban sa muna jimanta yanayin sa he is kind of stable now
nan na fita na shiga hade ruwan magani tare da ruwan zafin da junnut zata dan tsaftace jikin ta ita kuma tana dakin tare da abbu tana tallafa masa.
Babu abunda junnut take yi sai hawaye.Abbu yayi luiii da shike ma bayada karfin magana sai ido yake binmu da shi har muka gama duk abunda zamuyi.
Anan Bamu kama hanyar gari ba sai da na tabbata junnut tayi wanka ta dan kimtsa kanta kafin na gyara na abbu kwanciya na fito na rakata har layin gidan su sannan na dawo.
Cikin wani irin yanayin tunani nake tafiya,babu abunda nake tunowa sai alkawarin mu da junnut da yadda komai zai zamto min daga gobe..
Shekara ta goma sha hudu ne kawai a duniya dan haka bansan ko hukuncin dana yanke dai dai bane ko ba dai dai ba.
Washe gari Da safe Bayan na hada ma abbu na maganin sa na bashi ya sha,sai nayi zamana gaban sa na tsura masa idanu na bance uffan ba...,na dade a haka ina tunani dan a daren jiya ma ko tunanin kiftawa baizo min ba,yanzu ma kallon shi kawai nake ina tuno irin rayuwar farin cikin dasuka bani shida ammuh a lokacin da bankai haka ba
Tabbas ummah surbajo tana da ilimin da zata sama min mafita game da rashin lpyar Abbu..
So nake abbu na ya warke sosai ya rayu koda babu ni atare dashi...Sanyin safiya na kan busowa na fito nayi alwala nazo kan abbu nayi masa karatun qur'ani dai dai inda na kama..
Chan naga Abbun Ya farka ya bude idanun sa amma ko tashi da kyau bazai iyayi ba.
A Yadda na saba wanke shi nayi masa alwala haka nayi ta taimaka masa har yayi sallah...
Dan kadan ya sake shan maganin sannan ya kwanta yana kallo na,sosai yanayin sa ya dada rikita ni..
Gani nake idan ya kwanta baccin hala bazaima tashi ba tsaban wahalar dayake sha da jikin nasa.
Dana ga kallon
nasa yayi yawa
Chan sai abun ya fara bani a kwakwalwata ko dai wani abun yake bukata ne?sai nima bance komai ba,inda yabi da ido nake bi sai banga me yake kallo ba face ni,sai na tashi tsaye Ina dan dube dube ko zanga ya min alama..
Murmushi kawai yaso yayi amma Wani tari sai ya shake shi,karasowa jikin sa nayi a dame nace sannu abbuh...
Tarin bai tsagaita ba sai naga abbu ya ruko duka hannaye naYace bahiyyah,jiya a ina kikaje kika samu magani?
KAllon sa nayi A hankali na furta "jeji",wani runtse ido naga yayi alaman baiso yaji hakan ba amma baya da karfin da zai yi scolding dina..
Yace ke da junnut kuka je ko?
Toh meya faru da ku naga jini a rigar ta,ke kuma har yau idanun ki basu washe ba..shin bazaki fada ma mahaifinki damuwar ki ba bahiyyah?Yadda yayi maganan sautin muryansa na karkarwa yasa Sai nayi shiruuu tsawon lokaci kaina a kasa bance komai ba.
Muna cikin haka aka yi sallamah agidan mikewa nayi na fita abbu na bina da kallo mai dauke da alaman tambaya.
Dogaren sarki nagani,yace Aika ne daga gidan sarki modibbo akan cewa naje cikin gaggawa
Abbu dai bai sake tanka ni ba Nan na shirya kaina na nufi gidan su junnut.
![](https://img.wattpad.com/cover/195550205-288-k381569.jpg)
YOU ARE READING
AHUMAGGAH
Historical Fiction"Never let your best friend become your enemy"...that was my abbus last words before he left the world.Am a perfect girl,with a perfect heart i secrifice alot witout expecting returns.In this world they are two main life directors,the push or pull f...