💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Page 1.
Matashiyar budurwa ce wacce ba zata wuce shekaru 17 zuwa 18 ba a duniya ta fito daga wani corridor da zai sadaka da palourn gidan.
Sanye take da arabian gown sky blue tare da dan karamin hijabi dai dai shoulder d'inta pink colour,kafadanta na rataye da handbag wanda yake dauke da dan books dinta tare da sauran tarkacenta.
Dining site ta nufa direct,inda mahaifinta da matarsa ke zauna yana breakfast.
Da dan fargaba ta karasa inda suke, muryanta na d'an rawa tace "daddy barka da safiya, an tashi lafiya?" Fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa da "lafiya" take jikinta yayi sanyi har kullum tana fatan ace zata ga sauyin hali daga mahaifinta amma inaa abin dai ba a cewa komi.Mai da dubanta tayi kan momy dake ta doka murmushi tace "barka da safiya mom." Cike da fara'a tace "barka da tashi princess." Hmm shine abinda tace a zuciyarta.
Karamin cup taja ta hada tea sannan ta zauna tana kurb'a kad'an kad'an yayin da mahaifan nata ke d'an zantawa kad'an kad'an.
Sipping last drop na tea dinta tayi ta mik'e tare da fad'in "zan wuce sai na dawo."D'ago da kanshi babanta yayi fuskarsa a tamke yace "keh! Ina zaki?" Cike da mamaki ta kalleshi sannan tace "daddy school ba." Mai da dubansa kan momy yayi yace "ke baki fad'a mata bane?" D'an sunkuyar da kai momyn tayi cike da kissa tace "haba daddy ai ni ban dauka da gaske kake yi ba."
Tsaki ya ja cikin daga murya yace "wani irin baki dauka da gaske nake yi ba kinga na taba wasa irin haka ne?"
Hannunshi dake kan table din ta dafa tace "daddy Allah ya huci zuciyarka ni dai ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba balle inyi bakin jini..."
Kafin wani a cikinsu yayi magana tayi saurin cewa "wai me yake faruwa ne? Meye ne za a gaya min da ya shafi zuwana makaranta na?" Bata iddasa rufe baki ba daddy yace "na soke zuwanki makarantan ne!"
Take hawaye suka fara suntiri kan fuskarta bata iya cewa komi ba sai zubawa momy ido da tayi."Ki daina kallona haka tunda bani na hanaki zuwa makarantan ba." Cewar momy girgiza kai tayi ta mayar da dubanta kan mahaifinta duk wani tsoro ya kau daga zuciyarta "daddy why? Me nayi da za a soke min karatu,me yasa baka sona yanzu daddy?"
Kau da kai yayi gefe yace "tunda kince ke ba kya ji ai kin ta jawowa kanki kenan,tunda kin san baki gane karatu gwara na daina asarar kudina ina biya miki kudin makaranta,ko da yake ba ganewa ne baki yi ba ko soyayya ce kika soma."
Zaro ido tayi tace "daddy ni kuma? Soyayya? Haba daddy wallahi kaje ka bincika ka ji babu wanda nake kulawa da sunan soyayya cikin makarantan nan."
"Baki soyayya cikin makaranta amma ai kina yi cikin anguwa in ba haka ba uban me kike zuwa yi kullum wajen wancan shashashan yaron can me shago kullum?" Daddyn ya jefo mata tambaya
Kafin ta bashi amsa momy tayi carab ta ce "kash daddy karatu yake koya mata fa." Ta fadi hakan da murmushin da maimunatu ce kadai ta san ma'anarsa
Karatun kaniya yaron da ko secondary bana jin ya kammala in yana da ilimin karatun da take yi me yake ci da shagon provision me ya sa karatun bai tsinana masa komi ba?"
Ita dai memunatu bata iya cewa komi ba banda hawayen da take yi tana shirin bud'e baki tayi magana daddy ya katseta ta hanyar cewa "maza ki b'ace ki bani waje ki kuma fara shiri dan ba zan ajiyeki a gabana ki sa min ciwo ba nayiwa Sa'idu magana zai sama miki makaranta a nan cyprus kuma ba zaki je kiyi wani engineering course ba business zaki je ki karanta i cant waste my money on you."
Tana shirin protesting kaman ance ta kalli momy sai taga tashin hankali a fuskarta da alama bata san da maganan zuwa cyprus din ba murmushi ta sakar mata da ta lura daddy bai kallonta.