💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Da sauri sauri gudu gudu ta karasa gabansa tare da rike hannunsa lokaci daya tana kuka hade da dariya. Murmushi yayi me kayatarwa tare da dafa kanta yace "Munari an girma." Babban yatsansa ya saka yana goge mata hawayen dake makale a kan fuskanta tare da fadin "shhhhsh kukan ya isa haka everything is going to be alrighr." Gyada mishi kai tayi wasu sabbin hawayen na gangaro mata.
Cike da izza ya riko hannunta suka kama hanya shiga palon sa'ad na biye dasu dan tirjewa tayi cike da tsoro kallonta uncle sufyan yayi hade da sakar mata murmushi sannan ya gyada mata kai.
Cike da tsoro maimunatu ke biye dashi dan yanzun bata san matakin da daddyn nata kan iya dauka ba.
Bakin uncle sufyan dauke da sallama ya shiga cikin palon hannunsa a cikin na maimunatu suka shiga palon.
Har daddy ya yunkura zai mike sai kuma ya koma ya zauna tare da kawar da kansa yana muzurai.Kallon uncle sufyan maimunatu tayi taga ya tabe baki tare da cewa "Abdul ai da ka tashi nima kaci mutuncina kaman yanda kayiwa sa'ad dan ya dawo maka da diyarka." Har lokacin daddy bai ce komi ba sannan bai juyo daga kallon gefensa da yake yi ba.
"Mmm ai ni ka ban mamaki ai ni ina tunanin ko kariya daya daga cikin mu ya dakko daya zai tayasa amsansa ba wai ya tozarta sa ba kaman yanda kayiwa sa'ad,ka nunawa diyarka cewan mu bamu da daraja a idonka babu wanda ya isa yaci albarkacinka ta dalilinmu,yau ko lalace maimunatu tayi ya cancanta ka koreta? Haba! Abdul haba!." Zuwa wannan lokacin jikin daddy yayi sanyi sosai yaga rashin kyautawa abokinsa da yayi sauke kansa yayi yana kallon yatsun kafansa dan kam yaji kunyan sa'ad.
Ganin haka ya sa uncle sufyan karasa shiga cikin palon ya sami kujera ya zauna tare da zaunar da maimunatu a kasan kafansa uncle sa'ad ma ya sami waje ya zauna.
Maimunatu ta dade da sanin cewa daddy bashi da wani amini sama da uncle sufyan bashi da wani abokin shawara sama da uncle sufyan da shawaran uncle sufyan daddy ya fita da ita karatu kuma yanzu ma tana da tabbacin uncle sufyan ne ya saka a yi mata transfer ba daddy tunda ga alamu sun nuna bai san da zuwanta a yau ba har sai da ta saka kafa a cikin gidan.
"Rahina! Rahina!! Rahina!!" Uncle sufyan ya kwala kiran sunan momy (kar ku manta uncle sufyan shine mijin yayar momy shine wanda ya hada auransu) lokaci daya zuciyar maimunatu da momy dake sama ya doka.
Wallahi maimunatu ta manta da wata momy ta manta wani bala'in na zaune a Nigeria na jiranta sai dai wannan lokacin ta dau alwashin babu me takata ta bari.
Cikin lullube ta fito kanta a kasa can nesa ta tsaya tare da rinsinawa tana gaishesu.
Cike da masifa uncle sufyan yace "Rahina kina zaune a gidan nan da ranki da lafiyarki har Abdul ya kori diyarsa ki zauna cikin farin ciki?" A firgice bata da masaniya din nan kallon kwayar idonta yayi da sauri ta sadar da kai cikin rawar murya tace "wallahi yaya bani da masaniya ni sam ban san cewan maimuna ta dawo gidan nan ba."
Duba gefen kofan palon yayi tare da girgiza kai duk wannan tabargazan da akayi tace bata ji ba.
Kura mata ido yayi yace "Rahina kina sane da abinda maimunatu ta aikata a kasar cyprus." Kanta a kasa tace "eh yaya."
"Good toh wani mataki kika dauka akan hakan a matsayinki na mahaifiyarta?" Gaba daya ya daureta da jijiyoyinta duk sai ta firgice ganin haka ya sa daddy cetonta yace "sufyan wani irin magana ne kake yi haka? Kowa ya san iya kokarin da Rahina take yi akan tarbiyar nan amma ta watsar ta bi shedanu."Mayar da duban sa kan daddy uncle sufyan yayi yace "toh shikenan, naji kai yanzu duk tarbiyar da kake ikrari kun bawa maimunatu bai san kun shaidi halinta ba har kake shirin sallamawa duniya ita?"