💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 29.
Taqabbal minna wa min kum.
Duk taku daya da zasu zuwa board room din dai dai yake da bugun da zuciyarta yake yi fargaba biyu ne a tattare da ita zama cikin manyan masu kudi sannan kuma ga marwan.
Duk inda suka zo wucewa gaishesu ake yi kasancewar mubeena babba a wajen.
Sannan securities ne kaca kaca a cikin companyn ko wani kusa ya zo da tasa tawagarSafina ce cousin dinsu ta ja tsaki ganin da maimunatu za a je meeting din she cant believe daga zuwan yarinyan har ta samu shiga haka ji yanda tayi classy dressing kai kace tana daya daga cikin family din alhaji moh bata san maimunatu ma iyayenta ba matsiyata bane.
Mubeena na shirin bude kofar board room din maimunatu ta rike hannunta tare da rintse ido tana tsananta addua kallon bakinta da yake motsi mubeena tayi tana murmushi tare da dafe hannun maimunatu dake rike da nata tace "is going to be alright,just breath in and out." A hankali maimunatu ta ja numfashi ta saki cikin murmushi mubeena tace "good" sannan ta bude kofan.
Sau tari maimunatu na mamakin mubeena duk shiriritarta sarai ta san me take yi when it comes to work ba zaka gane mubeena ce ba wannan mashiriranciyar
Dakin taron cike yake da maza da mata koma fiye da haka suna zaune sai tattaunawa suke cikin su har da mufliha da Tahir wanda maimunatu bata ganeshi ba duk da irin kallon da yake jifanta dashi tare da murmushi gaggaisawa mubeena ta fara yi dasu tana gabatar da maimunatu
Alhaji Nasir shetima daya daga cikin manya manyan yam kasuwan Nigeria ne wanda kuma yake da 10% share a moh enterprises kuma mai mafi yawan share a company din bayan mamallakin company din dan sauran daga mai 5% sai 6% sai 7% ne.
Fuskarsa na dauke da murmushi ya cewa mubeena "mashaaAllah da samun mataimakiya kyakyawa ne hazaka." Murmushi itama mubeena tayi dan tuni ta saba da halin alhaji shetima da yaga yar kyakyawar budurwa jikinsa zai hau zikiri tace "Nagode sosai yallabai tabbas maimunatu akwai hazaka kuma ina jin dadin aiki da ita sosai." Hannu ya mikawa PA dinsa ya karbi complementary card dinsa ya mik'awa maimunatu tare da cewa "hajiya maimunatu ga katina ki bani kiran in kin kammala bautar kasan ki kina neman wajen aiki inshaaAllah zaki samu." Maimunatu bata yi mamakin sanin da yayi tana serving ba kasancewar id card dinta na like gaban rigarta da murmushi ta ansa katin dai dai lokacin da zuciyarta ta ba da wani irin sauti sakamakon bude kofar gaba daya da akayi Marwan ya shigo cikin dark ash din suits.
Nan da nan yawun bakin maimunatu ya kafe sai hadiye yawu take ba kakkautawa domin ta samu ta jika makoshinta da ya bushe lokaci guda ruwa mubeena ta mika mata a hankali yanda ba wanda zai ji tace mata "relax yaya baya cizo." Daga nan ta nemi waje ta zauna itama maimunatun ta zauna a gefenta ba tare da ta daga kai ta kalli kowa ba
Idanun marwan fes akanta murmushin gefen baki yayi ganin halin da ta shiga daga shigowarsa akan idanunsa wancan tsohon banza ke bata kati duk da bai san a wani dalili bane har ma tana sa hannun ta ansa fuskarta da murmushi.Cikin takunsa na isa ya karasa shiga cikin dakin babban kujerar sa ya nufa wanda yake girke a head na tabkeken table din da yake zagaye da kujeru masu yawa ya zauna.
Maimunatu ita kadai ce karamar ma'aikaciya a cikin dakin tarin babu wani secretary ko personal assistance a dakin taron sai ita wanda hakan ke yi mata nuni da itace CS
Ba tare da wani bata lokaci ba suka fara gudanar da abinda ya tarasu a wajen sam hankalin marwan bai kan kowa sai maimunatu dake zaune kanta a duke tana rubutu a tab dinta da alama tana rubuta minutes ne sam taki dagowa ta kalli kowa shi kuma so yake ta kalle shi dan bakinta kawai yake kallo tana motsa shi kaman yanda ta saba "somethings never change." Ya fada a hankali amma kowa yaji ka sancewar akwai mouth piece a jikin suits dinsa shirun da wajen ya dauka ne ya dawo dashi kallon kowa yayi da idanunsu ke kanshi sai a lokacin ya farga da abinda yayi dan gyaran murya yayi tare da kara musgutawa a hankali cike da kasaita yace "go on" duk da bai san wanda ke magana ba ko akan me ake maganan.
A haka aka round up din meeting din ba tare da ya tabuka komi ba ta kasan lashes dinsa yake kare mata kallo babu wanda ya iya karantar halin da yake ciki sai ita da ta san yana kallonta dan jikinta ya bata yana kallonta ko daman can shi mayen kallonta ne kuma tana yawan gaya mishi ba taso.
Duk da ta lura a cikin dakin ba shi kadai yake kallonta ba,wanda ke zaune kusa da mufliha wanda tafi tunanin Tahir ne da kuma Alhaji Nasir duk yawancin lokuta idanunsu na kanta amma me? Idanun marwan sunfi ko wani idanu kaifi a tattare da ita bata da wani buri da ya wuce a kammala meeting din nan ta tashi ba tare da wani abu ya hadata da marwan ba which she doubt.
A haka tayi zaman awa hudu da meeting din ya dauka a takura. Ana cewa an gama ta fara kokarin tashi bayan sauran manyan bakin sun fara fita har lokacin marwan na zaune bai mike ba balle ya sallami bakinsa.
Cike da girmamawa wasu daga cikinsu suke karasawa inda yake su yi sallama tare da nuna mishi son ganinsu da yake sai dai yayi murmushi yace zai duba yayin da wasu suka fita ba tare da sun waiwayeshi ba suna ganin karamin yaro dashi zai nuna musu iko ko dan yaga shine mamallakin company din ai dai ya san su ba matsiyata bane.
Mufliha da mubeena ke kokarin takawa bakin nasu maimunatu na mara musu baya ganin haka dan dama tun tuni idanunsa na kanta da sauri ya dan d'aga murya wacce take cike da kasala yace "auta ur secretary should stay."
Dam gaban maimunatu ya fadi murmushi mubeena ta mata tare da gyada mata kai ita kuma ta girgiza kai hawaye na dan taruwa a idonta dan bata rai mubeena tayi ta ja ta gefe tace "wai meye haka ne? Be strong mana sai kace kinga me yanka mutane." Ta fada cike da haushin yanda maimunatun ke nuna karara bata son abinda zai hadata da yayanta mafi soyuwa.
Cikin haushi tace "na tabbata ba criticising dinki zai yi ba zai so dai yaga kuma yaji abinda aka tattauna a taron dan na lura sam hankalinsa baya kan taron just be brave kar ki ban kunya."
Daga haka ta sa kai ya fice numfashi taja ta fitar ta nufi inda yake zaune wata mata da ake kira hajiya baraka na zaune kusa da shi suna dan magana isowarta wajen yayi daidai da lokacin da hakiya baraka ke cewa "gaskiya dai ya kamata ka shigo tunda kana kasar na san baby zata yi matukar farin ciki da zuwanka dan kwanaki take min korafin rashin kirkinka." Murmushi yayi yayin da maimunatu dake tsaye a dayan barinsa duk da luguden da naman zuciyarta keyi bai hana ta dan tabe baki ba a hankali tace 'na mamajo."
Karab a kunnensaMurmushi yayi me sauti yace "hajiya inshaaAllahu zan zo a mika min sakon gaisuwana gun baby ta kwantar da hankalinta zata ganni nima nayi kewarta ai." Yar dariya hajiyar tayi tace "atoh ai kun fi kusa ni ba zan wuce sai ka shigo." Da haka ta mike ta nufi kofar duk suka bita da kallo har ta fice a tare suke jin sautin zuciyoyinsu na canzawa.
Ko da fitan hajiya da Taheer ta ci karo yana dakon jiran fitowar maimunatu dan dazu ganin mubeena ne ya sa ya kasa tunkararsa dan sam baya son mubeena ta san da zancen yana son maimunatu har sai ya kama zuciyan maimunatun ta yanda ko da mubeena ta sani ba za tayi nasara tarwatsa mishi farin ciki ba ta kan abinda ya riga ya wuce kuma kaman yanda take da na sani shima haka yake da na sani.
Maimunatu bata ankara ba dan hankalinta na kan kofa saboda sam bata son kallonsa balle su hada ido sai ji tayi kawai ya janyota ta fada kanncinyarsa