💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 25.
Sun kwashe a k'alla mintuna sha biyar ita da uncle sufyan suna waya inda yayi ta mata korafin bata son kiransa dariya kawai tayi dan ita bata ga ta inda zata dau waya ta kira uncle sufyan ba,toh tace mishi me?
A haka dai suka yi sallama,wayarta ta tsirawa ido tana tuno me take yi kafin kiran wayan uncle sufyan ya shigo,wani status din da mubeena ta kuma yi ne ya tuno mata da abinda take son gani da sauri ta shiga status din nata inda taga har ta cire hoton sai rubutu da tayi kamar haka
_lucky those that were able to see his picture before he blastered me lol._ haka nan sai maimunatu bata ji dadin yanda bata samu ganin the face behind *moh interprises* ba.Kashe data dinta tayi tare da fita daga cikin whatsappp din wani irin bugawa kirjinta yayi ganin date da time dake fuskar wayanta yau birthday din Marwan ya subhana! Da sauri ta kife wayar tare da rintse idanu kaman wacce take ganin fuskar marwan din a cikin wayar.
"He turn 34 in har yana raye." Ta fad'a fili lokaci guda kuma ta zaro idanu jin abinda bakinta ya furta in yana raye? Where does that thought come from?
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un ta furta tare da yaye bargon da ta rufu da shi ta mike tsaye tana sintiri hannu ta dora a kai idanunta na kawo kwalla "me yasa ban taba yin tunanin ko wani abu ne ya sameshi ba? Ya rabbi ka sa ba haka bane, Allah kasa marwan lafiya lau yake yana raye,Allah kasa yaudarata kawai yayi amma yana rayuwa somewhere else cikin kwanciyar hankali." Ta fada tana rushewa da kuka she cant bear the thought of wai marwan bashi a raye ta gwammace ace yau yaudaranta yayi ya tafi amma yana wani wajen ya fara ajiye iyali.
Kuka take yi tana addua wishing din marwan all goods of life,tsohuwar laptop dinta ta dauko ta kuna,wanda bata wani abu muhimmi dashi tun bayan dawowarta daga cyprus limshe idanu tayi tana kokarin hana kanta aiwatar da abinda taake shirin aiwatarwa har laptop din ya gama booting.
A hankali ta bude idanunta akan system din ta fara shige shige har ta samo abinda take nema wani folder ne da aka rubuta M.
Ta dade tana kallon folder din har dai daga baya tayi shahada ta bude ba komi ke kunshe a cikin folder din nam ba sai hotunan marwan da wanda yake shi kadai da wanda suka yi tare.
Rabonta da ta bude wannan folder din tun da ta bar kasar cyprus da gaske take bata son ta dinga tuno Marwan cikin sand'a ta clicking sannan ya bud'e hoton farko ta bude marwan ne ke zaune kan iron bench yana dariya sosai idanunsa a waje dama gasu manya hannunsa daya rike da littafi dayan kuma ya kai zai ansa wayar da take shirin daukan sa hoton dashi.
Murmushi ne ya subuce mata hawaye na zubowa a kwarmin idonta she can vividly remember that day yana koya mata karatu ne. A hankali ta furta "happy birthday to you."
Next hoton taje hotonsu ne su biyu a cikin kasan ruwa, sai wanda tayi mishi yana kan doki a ranch din frnds dinshi. Haka ta kwashe lokaci me tsawo tana kallon hotunan wasu tayi dariya wasu tayi kuka.
Kallon kankantarta take yi a hoton she wonder ne marwan ya gani a tattare da ita lokaci,she was so young and neive ziciyarta ne ya bata amsa da shi yasa ya samu yanda yake so a tattare da keh,kuka ta rushe dashi tare da rife fuskanta da tafukan hannunta.Fadi take "why? Why marwan? Why? Me na taba yi maka da na deserving wannan ukuban me na taba yi maka mai zafi haka? Ban taba nufinka da komi ba sai alkhairi i did nothing but love you amma ka zabi ka banzatar dani i just hope and pray banzatar dani din kayi ba wani abu ne ya sameka ba sabida har gobe har kullum kana raina,nayi iya yina na kasa cireka a raina bani da buri da fata da ya wuce ka fita a raina ba but all in vein ko da yaushe kana raina." Haka ta dunkule a kan gadonta tana rusa kuka.
Bacci bai dauketa ba sai wuraren karfe uku inda ta dinga mafarke mafarken marwan da mr moh kaman yanda ta lakanawa moh din.
Exotic mafarki tayi wai marwan na romancing dinta a cikin dakinta na cyprus.Da matsanacin ciwon kai ta tashi a makare kaman ba zata je office ba taga in ta zauna a gidan ma tunani ne zai dameta tana balla buttons din dogon top dinta wayarta ta fara ringing ba kowa bane sai khalid har ga Allah tunowa da tayi da marwan ya mantar mata da batun khalid da matsalarsa.
Kan dressing stool dinta ta zauna kafin ta amsa kiran da dasashiyar muryata.
Amsa mata sallamar yayi duk sai yaji babu dadi da ya ji muryarta haka ya san kuka tayi saboda ya sani tun kafin tafiyarta karatu tana sonshi yaki bayyana mata soyayyarsa a wannan lokacin saboda kar ya tabbatar da abinda daddy yake cewa na suna soyayya ne,ya san dole yanzu taji babu dadi musamman yanda a dan watannin da suka gabata babu abinda yake nuna mata sai zallan soyayyarsa da kulawarsa duk da kuwa bai taba furta mata ba sai a jiyan.
Murya a sanyaye yace "munah ya kika tashi?" A hankali ta amsa mishi da "lafiya lau kai fa?"
Lumshe idanu yayi yace"alhamdulillah." Daga nan kuma yayi shiru ya kasa cewa komi,tana shirin ce mishi tana shirin zuwa aiki ne yace "munah jiya sai kika ki sauraro na,why? Ban sanki da haka ba,me yasa ba zaki tsaya kiji uxuri na ba is not fair."Murmushi me ciwo ta dan saki sannan tace "bana binka bashin bayani,ina ganin girmanka da mutuncinka bana son inji ka yi min bayani irin wanda kullum maza suke yiwa yammata ne."
Shima a gefensa murmushi yayi maimunatu ta bala'in dacewa da rayuwarsa da taimakon Allah sai ya mallaki maimunatu.
"Ba kya so kiji nace miki cousin dita ce ko? Ba kya so ince miki a gida ne aka ce in aureta ko?" Shiru tayi bata ce komi ba dan kaman ya shiga ranta ta sani sarai salon yaudaran samarin yanzu kenan."Munah!quite alright Habiba cousin dita ce amma ba ayi min dole in aureta ba a gida aka ban shawaran auranta ni kuma nayi na'am dashi saboda tana da hankali sannan kuma..." Sai yayi shiru itama shiru tayi tana karasa mishi maganan a zuciyanta sannan kuma yana sonta.
Numfashi ya sauke yace "anyway zan auri habiba sannan still ina so ki bani dama kafin ki yanke hukunci kar ki nesanta kanki dani kar ki yanke hukunci ba tare da kinyi zurfin tunani ba abinda nake so inyi ba haramun bane kin sani maimunatu kar ki haramta mana juna."
Dogon numfashi ta ja ta sake sannan tace "naji amma ka bani lokaci pls." Gyada kai yayi kaman yana gabanta yace "ok,but pls karki kara yin kuka." Murmushi kawai tayi a ranta tana fadin if only he knows kukan me ko na wa tayi
Sallama suka yi tana cigaba da shirinta,wani glass dinta ta dauko kato baki ta saka saboda ta rufe kumburin da fuskanta yayi na kuka..Ko da taje office da mubeena taga yanda fuskanta ya kumbura sosai hankalinta ya tashi dan duk a tunaninta saboda khalid ne.
Suna cikin office din mubeenan ne maimunatu ta kai mata wasu files ta signing.
A hankali mubeena ta tashi ta nufi kan sofan dake can wani bangaren office din tayiwa maimunatu nuni da ta zo ta zauna.
A nitse maimunatun taje ta zauna,fuska cike da damuwa mubeena tace "sis kiyi hakuri da yanda rayuwa ta zo miki kowa da kalar tashi jarabawan,fatanmu da kokarin mu har kullum shine Allah ya bamu ikon cin jarabawan nan,na san da zafi ace ka rasa masoyin da kake so it hurts alot musamman ma ace ka rasa shi ne ga wata macen,sai ka fara questioning kanka ta inda ka kasa,my dear ba kasawa kika yi ba shi haka so yake mutum yake,beside wannan me zata nuna miki banda farin fata?"Murmushi maimunatu tayi tace "ba komi nagode sosai da kulawarki amma ni damuwata ba na khalid bane kamar yanda nace miki ni da khalid ba soyayya muke yi ba fa." Gyada kai tayi tace "ba soyayya kuke yi ba amma kina sonshi." Shiru maimunatu tayi tana kokonton ta gayawa mubeena tana da wanda take sone ko zata barta da maganan khalid ko kuma yaya?
"You see na gaya miki kina sonshi gashi kin kasa denying,ni dai hakuri shi zance kiyi sabo..."
"Eh ina sonshi amma zuciyata tana tare da wani." Maimunatu ta katsewa mubeena maganarta ba tare da ta gama shawara da zuciyanta ba.
Baki bude mubeena ke kallonta "ban gane kina sonshi amma Zuciyanki na wajen wani ba,me hakan ke nufi?"
Hannu maimunatu ta sa ta shafe fuskarta kafin tace "it means akwai wanda na so ya kasa barin zuciyata duk da kuwa ina jin son khalid amma son...son...m..........
Thank you all for wishing me a happy birthday