page 48

2.4K 238 69
                                    

💖KINA RAINA💖










By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14








Page 48.






Girgiza kai yayi kawai tare da mikewa dan yaji masallacin anguwan suna tayar da sallah,da hanzari ya fice.

Maimunatu kam ta sami mama da aunty khadija na sallah a palon mama sai kawai ta shige cikin kuryar dakin itama ta gabatar da nata alawlan.
Tana cikin addu'a tana murmushi aunty khadija ta shigo dakin itama murmushin tayi har tana shirin tsokananta sai ta fasa ta mayar da hankalinta kan sadiq da yake bacci kan gadon mama.

Ninke sallayarta tayi ta karasa jikin mirro tana kara gyara fuskarta ita dai aunty khadija da kallo kawai take binta. Tana cikin sa lip gloss aunty khadija tace "kin gama dashi din ko in fadawa daddynki maganar?" Juya idanunta tayi tace "aunty khadija mun shirya ba sai kin gayawa daddy ba." Kama haba aunty khadija tayi tace "wai daman fada kuka yi ne?" Gyada kai tayi amma bata ce komi ba ganib haka yasa aunty khadija tabe baki ta san ba gaya mata zata yi ba.

Zama tayi bakin gadon dakin tana kada kafa aunty khadija tace "naji kaman ya shigo fa ba zaki koma wajensa ba?" Dan girgiza kai tayi tace "bari a dan yi kaman 5 minutes haka." Dan dariya aunty khadija tayi tace "su aji manya." Itama murmushi tayi dan ta san tabbas in bata yiwa kanta burki ba a kan marwan ba wani aji ne da ita ba gwara ta koya controlling kanta a kanshi in ba haka ba tsaba wahala zata sha a hannunsa da wannan shegen ikon nasa gwara ta koyi kwatarwa kanta yanci. Babu gardama a tsakaninsu amma kam babu tursasawa tsakaninsu wannan karon.

Kallon agogon wayanta tayi sannan ta mike ta nufi kan mirror har ta dau turare zaata kara a jikinta sai ta fasa ta juya ta kama hanyan  palon alhaji inda marwan ke zaman jiran dawowarta.
Turus tayi ganin bai taba komi na daga abincin da ta ajiye mishi ba.

Tana daga tsaye a bakin kofar ta rike kugu hade da karyar da wuya tace "baka ci abincin ba?"  Baya iya ganin fuskarta saboda ranan la'asar da ya kallo kofar da take tsayan sai ya zama ta bawa ranan baya.

Yace "baki bani ba zanci miemie?" Girgiza kai tayi ta karaso gabansa ta duka tare da bubbude warmers din serving dinsa shinkafa da wake da miyar tayi sannan ta tsiyaya masa zobo ta koma gefe ta zauna sakkowa kasa yayi ya zauna dan kallonta yayi yace "miemie pls sakkowa min dasu kasa." Kasake tayi tana kallonsa amma yana kallo ta gama arranging mishi komi kan center table din ba tun yau ba ta san marwan da son mulki da ba da order a fili tace "somethings never change." Ta fara sauke abincin.

Shima murmushin yayi dan tuno wannan kalaman su ya using ranan meeting dinsu ranan da ya fara ganin ta a Moh.
A nutse yake cin abincin yana jin dadinsa na ratsa mishi kwanya kunnensa har motsi yake yi sosai ya missing irin cimar nan shi bai san me yasa gida basu son yin irin abincikan nan ba da wuya a mixing shikafar da wake sai dai tsuranta ko kuma a saka mata su carrots dama dama zobo wasu lokutan ana yi,haka dai yayi ta sake sakensa yana cin abinci dan dama haka ya taso komi babu a cikinsa ko breakfast bai yi ba.

Maimunatu kam tsura mishi ido tayi tana mamakin abincin da yake ci ta san shi ba ma'abocin cin abinci me yawa bane amma ta lura ya kusan cinye tulin abincin da ta saka mishi banda yankan nama kusan hudu da ya cinye Allah ya sa ta saka mishi abincin da yawa duk sa ta san shi ba abinda ya dame shi in bai koshi ba cewa zai yi ta kara mishi.

Kau da kanta gefe tayi tana wasu tunane tunane kaman ance umya dago yaga ta kurawa waje daya idanu da alama tayi zurfi cikin tunanin da take yi kara tsiyaya zobon yayi ya sha sannan ya tsiyayya ruwa ya sha ya sa tissue ya goge bakinsa shi kanshi yayi mamakin abincin da ya ci ko da yake rabon da ya zauna ya ci abinci haka an dade.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now