page 36

2.2K 247 99
                                    

💖KINA RAINA💖






By Sawwama A.





Wattpad @sawwama14




Page 36.






_I appreciate each and every of your comments wallahi Allah ne kadai ya san farin ciki da nishadin da comments dinku yake sani na gode sosai._

"I can't believe yau Kin barni nazo ganinki" Tahir ya fada cike da farin ciki,murmushi tayi tace "ai na gaya maka komi lokaci ne we take one step at a time gaggawa aikin shedan ne.

Sipping juice dib dake hannunsa yayi yace "haka ne,i just wish kaman yanda kika barni nazo gidanku zaki bani daman gabatar da kaina ga babanki."
Rolling idanuwanta tayi tare da kara gyara zama tace "Tahir yanzu dai na gama ce maka mu bi komi a hankali inshaaAllahu ni da kaina zan gabatar da kai wajen daddy in lokaci yayi right now lets focus on knowing each other."

Shiru yayi amma ba haka yaso ba,ya so ace ya gabatar da kansa a wajen magabatanta ya san in har manya suka shiga cikin maganan komi zai zo misho da sauki ko da ace wani matsala ta bijiro mishi daga baya.

"Shikenan! I wish zan iya zuwa in ganki gobe a office but i have a lot of work kin san mondays,beside ranan yah marwan yayi min kashedi da soyayya lokacin aiki da na daure na shigo ko na 20 minutes ne."
Murmushi tayi tace "karka damu ni karan kaina aiki yayi min yawa cos ka san wannan week din na bar mubeena da aiki."

Fito da jikinsa yayi daga cikin kujeran da yake zaune ya daura hannuwansa akan guiwarsa ka fin yace "zan iya tamabayanki wani abu?"
Dan daga kafadu tayi tace "why not? Ina jinka"
Numfashi ya sauke yace "how close are you girls are dan yanda relationship din ku yake is kinda...i dont know.." Ya watsa hannayensa irin bai san kalmar da zai using ba.

Murmushi tayi tace "mubeena is a nice person tana min kirki sosai tana sona,in few weeks zamu yi passing out amma ita she want me to take her position in tayi aure which i doubt in haka zai taba yuwuwa."

Ba tare da tunanin komi ba yace "thats very good!"
Kallon mamaki tayi mishi kafin ya farga da abinda yayi ta jefa mishi tamabayn da ya sashi rudewa "why is it very good? Me yasa ma baka son mubeena ne after all you are family?" A dan rude yace "eh bana i mean ba wai bana son ta bane ."

"Toh meye? You even told me not to tell her about us and she has been nothing but good to me,me yasa baka son ta sani."
Kama kansa yayi tare da furta innalilalhi,ya salaam! Ni bana nufin komi da hakan kawai bana son surutu ne nafi son sai komi ya tabbata yanzun tana ji she will get excited alhalin har yanzu ban san makomata ba a wajenki."
Murmushi tayi tare da rufe fuska wai bai san makomarsa ba yau Tahir ne is sounding so serious ba wasa.

Dan hira suka taba yayi mata sallama ta fito rakashi motan khalid ya shigo juya idanu tayi ta san korafi kuma assalamu alaikum.
Tahir ya taba ganinsa so daya yazo daukanta amma bai ce komi ba ya shiga motarsa ya fita a gidan taji dadin hakan ta san da Marwan ne da an shiga uku yau.

Karasawa inda khalid yake tsaye a jikin motarsa tayi fuskar nan tasa a hade ita kam ma sai abin ya bata dariya duk fushin na meye?

"Barka da yamma dict dan fulani."
Bai amsa ba sai na jefa mata tambaya da yayi "munah wanene wannan da tafin?"
Gira daya ta d'aga tare da harde hannunta a kirji tace  a takaice "bakona ne"

"Bakonki? Bako maimunatu bayan kin san da magana na kike entertaining wani namijin?" Ya fada ransa a mutukar bace
Waro idanu tayi tace "ban gane na san da magananka ba last i checked ba sunana Habiba ba in makuwa kayi ba ri in tuna maka sati me zuwa daurin aurenka da yar uwarka habiba sannan ni kace zaka hanani sauraran wani?"

KINA RAINAWhere stories live. Discover now