💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 38.
Shiru daddy yayi momy kuma tayi wani mmm tare da tab'e baki ta kawar da kai gefe dan tsab daddy yayi mata bayanin su waye suka zo nemansa
"Mamana me yasa baki son shi?" Kafin ya bayar da amsa mami tayi carab tace "me yasa kuwa banda tana nan tana like da son wancan yaron me shago da ya juye ya koma security ina ganin ma yau ake auransa." Daddy bai ko kulata ba ya mayar da hankalinsa kan maimunatu sadar da kanta tayi tace "kawai ni dai daddy ban jin sonshi,ban ma fa sanshi ba."Murmushi daddy yayi yace "toh ai neman izni suka zo ba neman aure ba ki bashi dama in kun daidaita toh in kuma baki ji son nashi ba sai ki kawo min wani."
Gyada kai kawai tayi tana wasa da yatsunta yace "good,innarki khadija ta kirani a waya wai zato zo ta daukeki ki zaga dangi tunda baki son zumunci da su,me yasa baki kiran kakarki maimuntu?" Dan satar kallon inda momy take tayi ta dan yamutsa fuska tace "daddy in na kirata sai tayi ta amsani wani iri wai ni na cika magana a hankali kuma wai ni bani da hankali bana zuwa dubata,itama din ba son ganina take ba." Dariya daddy yayi yace"kunyanki mama take ji kasancewar kin san ai mahaifiyarki ce yar fari sai kawunk sadam,sai fitinanniya khadija in kuka hadu zaki sha fada wajenta tun tana yarinya take da fitinar fada mamanki ne dai ba ruwanta sanyin halinta yayi yawa Allah sarki Allah ya haskaka makoncinta ameen." Tsam mami ta mike dan taga hirar ba nata bane. Da kallo suka bita har ta kulle,daddy yace "yauwaa mamana wani sako sufyan yace zaki bani?" Maimunatu dake zaune bata san lokacin da tayi zaman dirshan ba, da kallon mamaki dady ya bita yace lafiya?" Murmushi ta kakalo tace "amm dama dama kan masu zuwa neman iznin ne." Ta fada tana kara sadar da kai ita kanta bata san ta inda karyar ta zo ba
Murmushi yayi yace "ja'irar yarinya da kika ce baki san da zuwansu ba,anyway it is all good." Hira suka cigaba da yi inda daddy yake ta bata labarin mamanta da familynta she cant remember when last suka yi irin hiran nan da daddy.Sai wajen 11pm ta mishi sai da safe ta nufi dakinta, wallahi har ga Allah tsoron marwan take ta san shi shu'umin mutum ne u cant guess what he is thinking,da gaske yake yana sonta? In ko da gaske yake sai yayi mata bayanin dalilin da yasa ya tafi ya barta ba tare da ya waiwayeta ba kafin ta yarda da auransa. Teddy bear dinta ta dakko wanda ya bata a 18th birthday dinta ta pressing tsakiya tana sauraron muryan teddy din.
Rungume teddyn tayi tana murmushi a hankali ta furta "Marwan i so love you i was only laying da nace maka bana sonka,kaine soyayyata and yes na ansa sunan munafukar da ka kirani dan duk bugun zuciyata yana bugawa da soyayyarka ce kawai ina bakin cikin tafiyarka ba tare da ka waiwayeni ba,na kasa amincewa da soyayyarkaka fitar dani a cikin duhu ka bayyana min soyayyarka ta usul ba tare da ka rabi jikina ba dan kai yaren taba jiki shine soyayyar da ka sani.
Da sassafe marwan ya saka daddy a gaba sai dai ya tuntubi baban maimunatu daddy ya shareshi,haka marwan ya like mishi yana ta magiya ganin ba zai kyaleshi ba ya sashi daukan wayarsa ya kira dadyn miemie a mutunce suka gaisa sannan daddyn marwan ya bukaci jin ko anyiwa marwan din izini murmushi daddyn mimi yayi yace ba laifi marwan din na iya neman yardan yarinya godia yayi mishi suka yi sallama sannan ya dawo da dubansa ga marwan "toh mahaifin yarinya ya amince ka dinga zuwa zance har ka sami amincewar yarinya kafin ayi maganar aure."
Marairaice fuska yayi yace "daddy ai na zata kawai kudin aure za a kai wani neman yardanta kuma?" Waro manyan idanunsa daddy yayi yace "ahhahh ban gane kai kudin aure ba,sai kace yar tsana. Auran dole kake so suyiwa yar su?" Fuskarsa cike da damuwa yace "daddy ba auran dole bane tana sona amma taurin kai gareta,sam taki saurarona shi yasa kawai nake son a mana auran in anyi na san zamu shirya."