💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 26.
Wani yawu me daci ta hadiye tare da jan hanci sai ta kakalo murmushi ta dafa hannun mubeena dake kan nata tace "its ok,abu ne da ya riga ya wuce bana son tunowa." Gyada mata kai mubeena tayi tare da squeezing hannunta ba ta pressing ba duk da yanda ta so taji wanene wannan da yayi wa maimunatu illa,sosai take sha'awan rayuwar maimunatu bata da hayaniya da ace yau yayanta is single babu abinda zai hana bata yi ruwa tayi tsaki ba ya so maimunatu toh ina shi din idanunsa ya rufe akan soyayyar babe dinshi and there is nothing anyone can do yanda ya likewa yarinyan nan.
Gyaran murya maimunatu tayi ganin mubeena tayi nisa cikin tunani a hankali ta dawo da dubanta kan maimunatu itama ta kakalo murmushi tana shirin yin magana wayarta dake kan table ta fara ringing da sauri taje ta picking ba kowa bace adda muflee ce "sorry yanzu zata kawo miki." Ta dan yi jim kafin ta ansa da "toh shikenan,right away." Daga haka ta katse kiran file din da maimunatu ta shigo dashi ta fara dubawa tana signing maimunatu na zaune tana kallonta har ta gama sannan ta taso ba tare da ta jira mubeenan ta kirata ba
Mika mata file din tayi fuskanta dauke da murmushi tace "pls ki kaiwa adda muflee tana jiranki yanzu,we will continue our discussion whenever you are ready." Murmushi ta saki tare da gyada kanta amma ta sani ba zata taba cigaba da wannan discussion din da kowa ba an gama shi kenan har illa mashaaAllah.
Office din madam mufleeha tayi da ikram karaman baby dinta ta fara cin karo yarinyan na ganinta ta taso da gudu ta rike kafafunta anwar ma dake zaune kasan carpet din office din ya taso da gudu yana mika mata hannu.
Murmushi tayi ta tsuguna duk ta rikesu a jikinta tace "ina zuwa bari in ba momy aika in zo ko?" Da haka ta karasa cikin makeken office din zuwa table din mufleeha yaran na binta a baya kaman jela.
Murmushi ta sakar mata lokacin da take gaisheta ta sa hannu ta ansa file din tana tsokananta maman yara dan dama haka take matsawar suka hadu da yaran zasu like mata sai sun bita har office dinta.
Yau ma haka suna shirin binta wani matashin saurayi ya bude kofar office din saura kadan ci karo maimunatu taja baya kallo yake kare mata ita kuma ta mayar da kanta gefe dan ta tsani kallo.
Ihun yaran ne suna mishi oyoyo uncle ya dawo dashi daga kallonta da yake yi mamansu ta dafe kai tace "yauwa gwara da kazo ka debi yaranku ku bar min office yara sun mayar min da office kaman nursery da sauri maimunatu ta fita ba tare da ta tsaya taji amsan da zai bata ba.
"Hamma Khalid me yasa kake hora ni haka,nace maka ban san cewan zata baza hotunan ba me yasa ba zaka fahimce ni ba?"
Rintse idanu yayi yana massaging goshinsa da hannu daya yayin da dayan hannun yake rike da wayarsa yace "biba ba horaki nake yi ba sam,kawai ina nuna miki mahimmancin jin maganana ne,nifa mijin da zan aureki ne in baki fara kwatanta jin maganana tun yanzu ba when zaki fara?"
Kara gyada kwamciyarta tayi hade da turo baki kaman tana gabanshi tace "ni ban ki jin magananka ba,ni wallahi yanda kake complain kan fitan hotunan sai ya dinga ban mamaki kaman wanda suka aikata wani mugun abu,hamma ko dai baka so a ganno da kai ne ko ban kai in zama matar shahararren dan binciken da kasa tasan da shi bane,ko kuma akwai wacce kake boyewa ni?" Ta karasa maganan tare da kankantar da ido kaman tana gabanshi.
Da sauri ya girgiza kai yace "ko kadan, kina magana kaman bani na ganki nace ina so ba,why wouli i be ashame of showing you to the world?"
Limshe idanu tayi a hankali tace "i thought as much,hamma yaushe zamu je yola ne time na ta karatowa ammi tace in tambayeka."Numfashi ya sauke yace "me yasa wai ba za a bar maganan zuwa yolan nan ba sai bayan biki wani zuwa gaisuwa da bankwana sai kace wanda zasu auri bare." Tabe baki tayi tace "al'ada ce dole muyi hamma."
Murmushi yayi yace"biba yaushe zaki daina ce min hamma ne?" Rufe ido tayi kaman tana gabanshi a hankali tace "soon,hamma ai lokaci ne kuma ya kusa." Dariya yayi yace "Allah ya kaimu lokaci zamu ga karshen cika baki. "
Dariya kawai tayi suka yi sallama fuskansa dauke da murmushi habiba akwai kunya bai san ita da maimunatu wa yafi wani kunya ba he will be one of the lukiest person in thw world in ya samesu su biyu dan duk basu da problem,banbancinsu kadan ne habiba na da surutu whole maimunatu ke da zurfin ciki.Dailing number din maimunatu yayi ya sa wayar a kunnan sa,yanda kiran ke dokawa haka zuciyarsa ke dokawa yana adduar Allah yasa ta picking sai da wayan ta kusan tsinkewa ta picking.
Tana iya jiyo saukar ajiyan zuciyarsa "munah." Ya furta can kasan makoshinsa sosai muryar da yayi amfani da ita ta tsirga cikin jikinta,jin bata amsa ba ya sashi mainata kiran sunanta.
Gyaran murya tayi kafin ta amsa sannan ta zarce da gaisheshi. Wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa jin muryarta normal sabanin kwanakin baya da tsinci labarin auransa.
"Munah ya kike?"
A gajarce ta amsa da"lafiya lau."
"Ya soyayyata kuma?"
Ya kara jefo mata wata gaisuwar
Dan murmushi tayi tana nanata kalman soyayyah
"Yes soyayyah ta munah,pls maimunatu kar ki rejecting dina."
Shiru tayi tana sauraronsa.
Bai damu ba ya dinga nuna mata yanda yake sonta sannan abinda yake shirin yi ba haramun bane.A hankali tace "khalid!ka sanarwa da amaryarka kana neman wata bayan ita?" Shiru yayi murmushi tayi tace "look here,i dont want to be the side chick,khalid in iyayenka da matar da zaka aura sun san da maganata,sun san cewan kana son aurena bayan habiba kuma suka amince khalid sai ka dawo muyi magana amma in ba haka ba,naki in yarda da zama side chick an dade ana yi amma sam ba zai faru a kaina,in kaje ka nemi yardan iyayenka da matarka sai ka dawo muyi magana wala Allah in yarda.....