💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 43.
Mubeena da tsananin farin ciki ta tashi ba zaka ce ita can take cikin tashin hankali ba jiya, Allah Allah take yi ta ganta a gaban maimuna da izzarta ta kama hanyan gidan su maimuantun Kuma har lokacin Bata bar Kiran wayarta ba duk da har zuwa lokacin ba ya shiga.
Tana Isa bakin gate din motar daddy na sawo Kai sai ta gyara parking kawai ta fito Shima ganin haka sai daddyn ya fito, Dan rissinawa tayi ta gaisheshi hade da gabatar da kanta as kanwar Marwan Kuma abokiyar aikin maimunatun kara fadada murmushinshi daddy yayi yace"madallah, ya baban naku da shi Dan uwan naki?" Dan har cikin zuciyan shi daddy yake son maimunatu da mutanen Nan masu nagarta (saura kuce dan yaga suna da kudi ne😏) murmushi tayi Tana sadar da kai da Kai tace "kowa lafiyq, amm Daman na biyowa maimun ne muje wajen aiki. "
" Ashha ai kuwa kinga anyi rashin sa'a yanzun nan da na fito dama zan bi Tasha ne in sa mata wayarta a mota Dan jiya da yamma tabi kanwar mahaifiyarta Zaria manta wayar da tayi ne ma ya sa bata sanar daku ba. " Dan murmushin yake mubeena tayi tace " wayyo! In ba damuwa daddy ka bani in sa mata wayar a mota tunda munfi kusa da tasha Kuma ba mamaki yayana kaga ya kama hanyan zarian yau ko gobe."
Dan dariyar jin Dadi daddy yayi yace " toh shikenan. " Ya koma cikin motar ya fiddo mata da wayan.
Godiya tayi mishi sannan suka yi sallama sannan kowa ya kama hanyan wajen aikinsa.
Mubeena ji tayi ta fashe da kuka ga maimunatu tayi Nisa ga wayarta a hannunta tsaki ta ja Dan haushi ta san sai yayanta yafi ta bakin cikin wannan tafiyan da maimunatu ta tsira dare daya ba tare da sanar mata kafin ta tafi ba.
Marwan bai Sami kansa ba ranan saboda da sassafe ya Sami Kiran ogansa daga abacha barracks suna wani aiki ne ya rike su har yamma mubeena Kam ta bar mishi missed calls ba adadi Dan wayarsa ma a silent ya sata.
Sai bayan magrib ya bar cikin barracks din maimunatu kawai yake muradin gani ko gida bai nufa ba balle ya cire uniform dinsa ba ya wuce gidansu for the first time.
Yana tunanin ko ya haduwarsu zata kasance oho
Yana tsaye cikin compound din hannun rigarsa a nannade tun alawlan magrib da yayi hannunsa daya cikin aljuhu dayan rike da wayarsa Yana kara Kiran layinta for the 100th time Amma the same story hango daddy yayi yana shigowa da sauri ya karasa gareshi tare da dan rissinawa yana gaidashi shiru suka yi kafin cikin tsoro daddy yace "kanwarka bata gaya maka maimuna ta tafi Zaria ba?" Ya tambayeshi dan sai yanzu ya ga wautarsa na bayar da wayan maimunatun ga stranger.
Girgiza kansa yayi yace"wai mubeena?" Da sauri daddy yace "eh ita." Ajiyan zuciya ya sauke yace"duk ya bamu hadu ba amma naga missed calls dinta."
Sai lokacin hankalin daddyn ya kwanta inviting Marwan cikin gidan yayi yaci dinner yace ah ah zai wuce gida.
Mubeena na kwance Tana aikin nata na fama waya Marwan ya banko kofar yau ko knocking din ma bai yi ba a firgiceta mike hade da dafe kirjinta tace "Kai yayana ka tsoratani" Dan dafe kansa yayi yace"sorry daga gidansu miemie nake." Kashe wayarta tayi tace"to ba Ina ta kiranka baka picking ba." Ta mike hade da dakko wayarta a kan mirror dinta tace "ga Nan wayarta daddynta zai Kai park nace zan Kai." Da sauri ya Mika hannu yace" bani nan gobe zani zarian. " Murmushi tayi tace I thought as much. " Tare da mika masa wayar " yayana zani. " Girgiza Kai yayi yace" ba yau ba. " Ya fada tare da fita a dakin.
Tun a hanyar shiga side dinsa ya kunna wayar ko gama booting bata yi ba kira ya shigo wayar murmushi yayi da yaga me kiran......
Cikin isa da izza ya ansa wayar yayi magana minti daya zuwa biyu yayi sannan ya kashe wayar cike da satisfaction wanka yayi yana jinsa cikin nishadi sannan ya janyo wayar yana dubawa.
Ba karamin dauriya yayi ba wajen kin duba messages dinta gallary dinta kawai ya shiga yana kallon hotunanta gwanin kyau babu komi a fuskarsa sai fadaddan murmushi
Zaune ya tashi yana kara bude hakoransa da ganin abinda yake cikin wayar hotunta rungume da teddy din da ya cire makudan kudi ya siya mata on her 18th birthday hakan yana nufin har yau tana yinshi.
Bai kara shagala ba har sai da ya ci karo da hotunan su na cyprus tashi yayi yana juyi gaba daya murna ta cika shi kisses ya dinga mannawa wayar kamar wayar gaba daya ce maimunatu.
Daren ranan dai marwan bacci farin ciki yayi da safe kuma da kyar ya bari goma tayi kafin ya je office din daddy dan samun address din inda take a zaria minti goma bai kara yi a garin abuja ba ya dauki hanyan zaria.
Tafiyar awa biyu yayi saboda tsananin gudun da yake yi bai tsaya ko ina ba sai anguwar da daddy ya gaya masa.
Fitowa yayi daga motarsa a wannan lokacin maimunatu ta fito ita da Badamasi second cousin dinta zai kaita gidan su ta gai da mamansa ta sha kyau cikin riga da skirt na atampha ya tsaya sai kashe mata hotuna take wai tayi kyau ita kuma tana kyalkyala daria.Cak numfashin marwan ya tsaya kunnuwarsa har wani tiririn hayaki yake fitarwa dan masifa idanun nan har sun canza kala run rine ta juya tana yi wa badamasi magana ne idanunsu suka sark'e take maganan ta kwarar da ita ta fara tari ba kakkautawa.
Hannu badamasi ya sa yana dan bubbuga mata baya bai ankara ba sai ji yayi an cabke hannunsa tare da murdewa....