💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 47.
_i can see that my wattpadians love hoton mems dina thats maimunatu Gani maimunerh my own mems masu cewa in nemo Marwan suna so su gan hotonsa ban san inda zan samo wannan fitinannan ba mai mayan ido the hunt is urs to make in kun samo hoton da ya dace dashi ku turo min ta watsapp 09032871327
Shiru yayi ya tsareta da manyan idanunsan nan baka jin motsin komi sai hannun agogon dake girke a bangon dakin duk second daya da zai wuce sai bugun zuciyar marwan ta sauya yana tsoron jin kalmomin da zasu fito daga bakin maimunatu he mean everything he just said matsawar bata sonshi zai rabu da ita amma ya sani rayuwarsa zai shiga taraddadi amma na dan wani lokaci ne domin komi na duniyan nan me wucewa ne rayuwarsa da maimunatu zai wuce kamar ba a yi ba shi mai juriya ne zai jure rashinta kaman yanda ya jure a wancan lokacin, abu daya ya sani shine har ya koma ga mahallicinsa maimunatu zata kasance cikin zuciyarsa dan ita din tana ransa a ko wani wucewar dakika sonta wata halitta ce a cikin zuciyarsa da bashida ikon kankaresa da kansa har sai wanda ya kirkiri son ya raba shi da shi.
Kaman daga sama ya jiyo muryarta cikin natural sanyin ta da ya santa da shi tun fil azal, ba muryar masifarta da ta kirkira dare daya ba tace "ka sani kaine mutum na farko da zuciyata ta fara so a ko wani fitowar rana da faduwarka KANA RAINA ina so bani so tunaninka na makale a cikin raina i hated myself for loving you ban daukeka komi ba face fasiki mayaudari!" Rintse idanu marwan yayi domin sosai kalmominta na karshe ya bi duk wata jijiya da ke makale jikinsa ya haura zuwa brain dinsa.
Numfashi ta sauke ta cigaba da cewa"but then what can i do da abinda ba ni na daurawa kaina ba na dade da ganewa ba sonka ne ba nayi ba bakin cikin halayanka nake yi marwan,kyamar halin da ka sakani a zamanin zaman mu a cyprus nake ko ka san cewa babu namijin da ya taba rike hannuna wanda ba muharramina ba sai kai,ko ka san kaine ka taba kusanto ni da zina ko ka san abubuwan da muka aikata ni da kai wata nau'i ne na zina? Ba lallai sai da penetration bane zina ke aukuwa ta yaya kake so in kalleka in kalli future da kai marwan?
Ka duba halin da ka saka mubeena a ciki nayi imani hakkin matan da kayi mu'amala da su ne ya sauka kan mubeena ba zance bata da laifi ba akan abinda abinda ya sameta ko in daura laifin kocankwan kanka ba but kaine jagaba akan abinda ya faru da ita.
Kaman yanda aka ce ku nemawa diyoyin ku uwa ta gari haka muma yake a gare mu,wacce uwa ce kake tsammanin zata so yau ace ga abinda uban yayanta ya aikata? Ban kasance mazinaciya ba ban taba kasancewa da wani namiji ba in ba kai ba yaya tsoro ba zai kamani ba?"
Cikin murya kaman me rada yace "but i repent kuma zamu yi musu addu'a nothing will happe in sha Allah have trust on him."
Gyada kai tayi tace "i will accept you but with one condition." Cikin sauri yace "name it!" Hannunta ta dan daga tace "chill we are not in a business field trying to seal a deal aure kake nema." Ta karashe magana tare da daga gira daya.
Murmushi yayi tare da gyaran murya har ma da gyara zama yace "tohm naji na gyara,now whats your condition?"
Daga idonta sama tayibtare da tsuke baki ta dan dafe gefen kumatunta da yatsanta daya kaman me tunani shi kuma ya shagala da kallon zanan lallin da aka yi mata wanda ya zauna yayi das akan fatanta kaman a manna mata shi ji yayi kaman ya kamo hannun yayi ta manna mishi kisses kawai.Sauke idanunta tayi akan shi tace "its conditions not condition gaskiya." Waro idanunsa yayi yace "woah now am scared,ya nake ji kaman wannan conditions din naki is not something good?" Dan tabe baki tayo tare da daga kafadu tace "ai in zaka iya ne ko?" Gyada kai kawai dan ya san koma meye zai iya matsawar bai sabawa addininsa ba wanda ya san maimunatu wont ask for something like that.
"NO more brotherly hug to any of your cousins." Daga kai yayi ya cire yatsansa daya yace "one" tace "ba zaka kara tab'ani ba har sai shari'a ta mallaka maka ni." Ya kara fitar da wani yatsa na biyu yace "tw....wait! What?" Gyada kai tayi tace "yeah,you heard me hakan ne zai tabbatar min da kana sona ko kuma jikina kawai kake so ba zan boye maka ba kokontan ingancin son da kake min yana daya daga cikin abinda yasa nake doubting soyayyar ka gani nake jikina kawai kake so tun wancan lokacin da baka samu ba ka kuma sai baka kara waiwayata ba yanzu kuma da ka ganni kake kokarin samu."
Wani yawu mai kauri ya hadiye yace "dan Allah ki daina doubting son da nake mikj kice komi amma ki daina karyata son da nake miki miemie ina sonki wallahi pls ki yarda dani ko da baki yarda da kalma bakina ko daya toh ki taimakeni ki yarda da wannan dai daya."
Kallonsa tayi cikin ido tace "toh ka tabbatar min da wannan soyayyar da kake min ka sa min yardanka a cikin zuciyata da raina."
"Saboda already ina cikin ranki ko? Yarda dani babu a tattare da ke."
Wani irin murmushi tayi mishi me narkar da zuciya tace "eh kana raina a ko da yaushe."
Wani irin juya idanu yayi tare da dafe kirjinsa dan wallahi sai da zuciyarsa ta skipping beat a hankali yace "nima tun ranan da na fara ganinki KINA RAINA i thought its just love uhm uhm ashe soyayyar karamar yarinya ne ya kamani da zan kwana but yau zan koma in cewa daddy mun gama fahimtan juna pls a bani matata" dukka giranta ta daga tace "oh really? I dont recall hearing you say ka aminta da conditions dina." Rolling idanuwa yayi yace "na aminta da duk wata condition dinki da wanda kika fada da wanda ma baki fada because i love you and i want to make you mrs moh."
Wani murmushin tayi mishi tana jin wani fresh air na ratsa duk wata kofa ta gashi dake jikinta mik'ewa tsaye tayi ta kama hanyan kofa tace "kaci abinci la'asar tayi." Sai da ta kai kofan ta juyo tare da cewa "hey you really look good in kaftan zan siya maka hula irin naku na yan Borno......" Da sauri ta fice daga dakin yana kiranta amma tayi nisa.