page 17

1.7K 160 19
                                    

💖KINA RAINA💖

By Sawwama A.
   




Wattpad @sawwama14




Page 17




Ba kowa ke kiranta ba illah daddy kyar kyar jikinta ya cigaba da kyarma sam ta kasa tattara courage din ansa kiran har ya tsinke mai da dubanta kan jalila tayi wacce ke yi mata kallon tausayi dan taga wanda yake kiran.

A marairaice take kallon jalilan not knowing what to say or do. A nutse jalila ta dora hannunta bisa kafadun maimunatu cikin sanyin murya tace "look here maiimoonattu calm down and take a deep breath." A hankali maimunatu ta ja numfashi ta fesar kaman yanda jalilan tace.

"Good." Shine abinda jalila tace sannan ba tare da ta kalli idanun maimunatun ba ta shaida mata cewan school authority na son ganinta a mugun tsorace ta kalli jalila wani sabon kuka na kubce mata yau ita kam ta shiga uku.

"Shhhhh dont cry i will stay by you." Jalila ta assuring dinta amma hakan bai sa ta tsagaita kukan da take yi ba da kyar da sudin goshi jalila ta shawo kanta ta dan yi shiru sannan ta rike hannunta zuwa office din VC din makaranta maimunatu na rakube a jikin jalila kaman wacce tayi wa sarki karya kallo daya zaka yi mata ta baka tausayi.

Da yawa wasu daga cikin daliban kallonta suke yi cike da tausayi dan wanda suka santa sun san ba zata taba aikata hakan ba sun san kawai sharri ne dan attention ya dawo kanta wasu kuma da suke jin haushinta saboda dedication dinta wajen karatu sai isgilanci suke yi mata amma bata kula ba ina ma take da karfin halin kulawa maimunatu ta kalli mutum so nawa balle tayi mishi magana.

Bata da abokin hira bata yawo bata hulda da kowa babu wanda ya taba ganinta da wani dan uwa ko aboki ko saurayi sai dai wasu lokuta in marwan ya zo daukanta ko ya dropping dinta and babu wanda ya san alakar dake tsakaninsu duba cewan duk su din bakaken fata ne.
In kaga maimunatu da wani toh tabbas aboki ko abokiyar karatu ne kuma karatu ne ya hadasu,abin tambayan a nan shin wa zai aikata mata wannan danyen aikin? Wa ta batawa haka da zai so tozarta rayuwarta? Yarinyan da abokin mutunci ma bata dashi balle na fada.

Tambayan da ya cika kwakwalwan jalila kenan but she is not in the right position to ask her.

A bakin kofan office din jalila ta dakata tare da kokarin zare hannunta,gam maimunatu ta riketa tana gunjin kuka dan wani bala'in tsoron tunkaran hukumar makarantan take ta yaya zata fara kare kanta? Me zata ce musu wanda zai sa su yarda da ita? A hankali jalila ta dora hannunta kan na maimunatu dake damke da dayan hannunta tare da gyada mata kai kan cewan komi zai wuce. Wani dunkulalen hawaye ne ya zubowa maimunatu a karo na barkatai da sauri jalila ta zare hannunta tare da juyawa tana dauke hawayen tausayin maimunatu sannan ta juyo. Kwarin guiwa ta bata sannan ta murda kofan ta turata ciki ba tare da ta shirya ba.

Ko bayan shiganta office din VC din shiru tayi tana sauraran hukumar makarantan ta inda suke shiga bata nan suke fita ba in da suke gargadinta da in zata tallata tsaraicinta tare da tallata sana'arta ba a cikin makarantar ba sannan aka bata suspenssion na semester din gaba kasancewar jarabawar wannan semester din ta karato.

Ita dai maimunatu babu abinda take yi sai kuka bata musa laifin da ake tuhumarta da shi saboda bata da hujja da haka aka sallameta ta fito ta samu jalila a waje tana jiranta.

Jikinta ta fada tana kuka izuwa yanzu hawaye ma basu fita a idonta sai gunjin kukan kawai idonta wani irin azabar radadi yake yi mata haka jalila tayi ta lallashinta tare da janta zuwa wajen motarta.

Jalila zata girmewa maimunatu da kusan shekaru biyu kasancewar maimunatun ta gama makaranta da wuri ne.

Har gida ta mayar da maimunatu bayan ta bata address din gidanta.
Wannan shine karo na farko da wani a kasar ya san gidan maimunatu bayan marwan,jalila ita ce mutum ta farko da ta shiga jikin maimunatu kuma har ta barta kasancewan tana neman kafadan kuka sai da jalila ta tabbata ta sha tea da aspirin sannan ta bar gidan.

Bacci me nauyi ne ya dauketa wanda ita kanta ta manta rabon da tayi irin baccin saboda jalila har da maganin bacci ta hada mata.

Bata farka ba sai wajen yamma zuwa lokacin idanunta da kanta sunyi nauyi sannan fayau take jinta.
Da kyar ta samu tayi wanka tazo ta jera sallolin da suka wuceta.
Jakarta ta janyo inda ta fiddo da wayarta missed calls ne rututu da text mesaages na mutane dabban dabban ciki har da missed calls din daddynta da su uncle sa'id ta san duk so suke su ji dalilin abinda suka gani a status dinta.

Abin takaici babu missed call ko message din marwan ko daya wasu hawaye ne suka zubo mata me marwan ke nufi da ita ne?
Dora kanta tayi a kan guiwanta tana rera kuka a hankali wayar ta ce ta fara ringing daddy ne damm gabanta ya fadi wayar ta ajiye can nesa da ita tare da kara rakubewa tana kuka kaman tana gaban daddyn yau ita me zata ce mishi tana ji tana gani har kiran ya tsinkewa wani ya kuma shigowa still daddy ne haka shima ya gama ringing bata dauka ba nan kuma na uncle sa'id ya shigo nan ma kara volume din kukanta ta yi anma bata picking ba har ya tsinke.

Haka kiraye kiraye suka dinga shigowa wayarta da numbers din da ta sani da wanda bata sani ba amma bata dauka ba sai aukin kuka da take ta yi kafin kace me zazzabi me zafin gaske ya rufeta dama ba wai ta gama samun sauki bane.

A cikin wannan halin Jalila tazo ta sameta babu shiri ta danganata da hospital emergency aka kaita dan bata cikjn hayyacinta taimakon gaggawa aka bata har aka samu numfashinta ya dawo dai dai.

Jalila ita tayi ta dawainiya da ita har ta samu sauki aka sallameta,ita ta dinga bata shawarwari tana dada karfafa mata guiwa har ta dan sake suka fara karatun exams har zuwa wannan lokacin maimunatu bata yi magana da kowa daga gida ba sannan bata daukan kiran kowa in ba na Jalila ba.

Dalili daya ya saka bata canza layi ba saboda har kullum tana saka ran jin kiran marwan amma shiru kake ji kaman malam yaci shirwa.

Suna tsaka da exams wata rana tana karatu ita kadai a cikin dakinta idomta ya fada kan teddy din da marwan ya siya mata lokacin birthday dinta shiru tayi ta kurawa teddy din ido har gobe ta kasa daina mamakin dalilin da ya saka marwan bai kirata ba

Bakin cikinta daya bata san kowa nashi ba,bata san wa zata kira ta tambayi halin da marwan ke ciki ba. Me yasa basu taba introducing wa juna families dinsu ba? Toh ko dai dama Marwan yaudaranta yake dama ya shirya rabuwa da ita ne? Wannan tunanin shi ya dimauta maimunatu ta fashe da wani marayan kuka tare da kife kanta a kan table dinta.

Door bell dinta aka danna hakan ya sakata mikewa tare da goge idonta dan ta san jalila ce cos tace mata zata zo suyi karatu,hallacin jalila ya sa maimunatu ta kasa koranta a rayuwarta kaman yanda ta saba koran duk wanda ya so kusanci da ita.

Ba tare da ta tsaya ta duba wake knocking ba ta bude kofar sai da numfashinta ya dauke na wucin gadi ganin wanda yake tsaye a door step dinta.....

Ni kaina dai wannan page din bai min dadi ba bans on koke koke mtswwww

KINA RAINAWhere stories live. Discover now