page 49

2.8K 279 98
                                    

💖KINA RAINA💖










By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14








Page 49.









Dan jim tayi tana kallon kiran,kaman kar ta picking sai zuciyarta tace mata meye amfanin avoiding calls dinsa? Picking tayi tare da yin shiru tana jiyo sanda ya sauke ajiyan zuciya sannan cikin muryar shagwaba yace "haba maimoon,mai na aikata haka me girma da zaki shareni kwana biyu sannan ni in na kira baki picking,kin san a halin da kika sakani kwana biyun nan kuwa? Gashi kinki ganina in naje gidanku sai ace min baki nan,why maimunatu?" Ya karashe magana yana wani sakin kukan shagwaba.

Tabe baki maimunatu tayi tana ji kaman ta kurma ihu ko ta kudunduma mishi ashar dan takaicin shagwabar na sa sabanin da, da abin yake bata dariya.

Juya idanu tayi tace "uhm" kawai dan ta ma rasa me zata ce mishi tana sake saken abinda zata ce mishi ta sake jiyo muryar tasa yana mata tabara "uhum mimi? Talk to me mana mimina." Bata san lokacin da magana ya fito bakinta ba "dont! Dont ever call me that again,baka da wannan daman na kirana da sunan nan." Ta sauke numfashi tana limshe ido dan cikin tsawa tayi maganan shima shiru yayi kafin cikin sanyin murya yace "am sorry,amma me nayi miki haka? Menene laifina? Pls ki gaya min domin na baki hakuri ina tsananin sonki maimunatu pls kar ki guje min kar ki bari wani ya shiga tsakanin mu." 

"Babu abinda kayi min babu kuma wanda yake shirin shiga tsakanina da kai but i am sorry for wasting your time aure zan yi Tahir nan ba da jimawa ba."

Wani irin zabura yayi yana cewa "no no no no pls kar kiyi min haka,kin san a halin da zaki sani kuwa matsaear kika yi min haka dan Allah kiyi hakuri ki saurareni wallahi i will explain everything to you amma kar ki barni yaya zaki yi min haka,yaya zaki kubce min a daidai wannan lokacin da nake jina me sa'a maimunatu pls ki saurare ni wallahi ba laifina bane sharrin shaidan ne har ga Allah na sota pls dont believe duk wasu abubuwa da ta ce miki kar ki badi mubeena ta raba mu ita ba gashi auranta zata yi ba." Gaba daya ma a rude yake bai san me yake fadi ba shi dai burinsa maimunatu ta saurareshi dan da gaske yake yana tsananin sonta.

Maimunatu bata ji tausayinsa ko na kobo daya ba tace "ban gane me kake fada ba fa Tahir,me ya faru? Me yasa Mubeena zata rabamu kayi mata laifi ne?" Shiru yayi yana kokarin tariyo magnganun da ya gama fada cikin rudani. Kar dai mubeena bata gaya mata ko mi ba ya so ya tona ma kansa asiri? Bai gama tunanin ba ya jiyo sautin murmushinta.

"Hmmm the cat got ur tongue? Tahir kenan you think zaka escaping sakamakon abinda ka aikatawa mubeena ko? Wrong! Allah ba azzalumi bane Tahir sai dai wanda ya zalinci kansa kai da karan kanka ka zalinci kanka anyway bani da hurumin gaya maka ko wani irin magana saboda duk wanda yayi mai kyau kansa yayiwa kuma maganan aure babu ruwan mubeena ina tunanin ko da maganan mubeena ko babu ba zan aureka ba kayi hakuri saboda i found my lost love ina maka fatan Allah ya hadaka kai ma da wacce zata soka tsakani da Allah kaima kuma ka sota haka." Ba ta jira komi ba ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.

Tahir kam saroro yayi yana kallon fuskar wayarsa dake dauke da hoton fuskan maimunatu tana murmushi bai san yanda aka yi ya yi saken da soyayyarta ta yamutsa mishi zuciya ba.
A zabure ya mike kaman wanda aka tsikareshi keys dinsa ya kwashe ya fita daga gidan a guje yake tuki motoci sai kauce mishi suke Allah ne kadai ya kai shi inda zashi lafiya.

Cikin sa'a yana shiga ita kuma tana shirin shiga motarta ita da kawarta da kuma cousin dinta suka tsaya suga waye ya shigo gidan haka, fitowan Tahir ya sata jan tsaki tayi kokarin bude motar ta kasa saboda yanda jikinta ke rawa.

Bata ankara ba taji ya damko dantsenta ya fara janta keeee kallon kallo sauran yammata biyun suka tsaya yi dan dai sun san wannan ba muhammad bane gwara ma cousin dinta ta so ta gane face dinshi.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now