page 18

1.8K 156 39
                                    

💖KINA RAINA💖

By Sawwama A.
   



Wattpad @sawwama14




Page 18.

"Uncle sa'ad!" Ta furta tare da zaro idanu,gyada kai yayi hannunsa na cikin aljuhun wandonsa fuskarsa dauke da murmushi yana kallon yanda fuskanta ya dawo ya suntime ga ido ya koma ciki ciki alamun kullum sai tayi kuka,har gobe har kullum yana tausayin rayuwar yarinyan amma taimakon da zai iya yi mata kalilan ne.

Ji take yi kaman taje ta rungume shi amma ina jiya ba yau ba girma ya zo she is not more that little girl he carried,wani kunya ne da tsoro ya dirar mata lokacin da ta tuno da abinda ya kawo shi.

Sunkuyar sa kanta tayi tana kokarin mayar da hawayen dake taruwa a kurmin idanunta. "Maimunatu" ya furta cikin sanyin murya like always.
Kasa dago da kanta tayi saboda kunyaj hada ido da abokin mahaifin nata wanda ba tantama yana tunanin hoton tsaraicinta ya gani a story dinta na social media.

Cikin nutsuwa ta amsa ba tare da ta dago kanta ba,gyaran murya yayi yace "je ki saka hijabinki ki sameni a kasa we need to talk." Gyada kai tayi tare da amsawa da toh.

Cikin sanyin jiki ta koma daki ta daura doguwar riga kan riga da wandon dake jikinta tare da saka hijab dai dai shoulder dinta.
Ko da ta fito ya riga ya sauka  so ita kadai ta bi lifter dan zuwa kasan, a cikin lifter din ta samu daman yiwa jalila text kan cewan ta fita da uncle dinta.

Wani restaurant dake cikin anguwan suka je inda uncle sa'ad ya reserving musu wani booth dake can lungu.
Zaman shiru suka yi after giving their order uncle sa'ad bai ce mata komi ba har zuwa wannan lokacin.

Itama shiru tayi tana jiran taji ta inda zai fara. Yana shirin magana wayarsa ta dau ringing sallama yayi bayan ya dauka "yeah muna tare da ita yanzu haka,chill mana,nace ka bar komi a hannuna abi abu a sannu tukun." Dan jim yayi yana sauraran wayar yayin da zuciyar maimunatu ke ba da sautin duka dan tana iya jiyo kuwwan muryan mahaifinta duk sa bata jin me yake fada amma ta san fada yake yi. Sai da ya gama uncle sa'ad yace "toh naji! I will take care of everything here." Yawu maimunatu ta hadiye tana zazzare ido.

Sallama yayi da daddy kafin ya mayar da dubansa kan maimunatu dake zaune a daddare kaman za ace mata keh! Ta bace.
"Maimunatu what happened?" Shine tambayan da ya jeho mata habawa sai hawaye girgiza kai yayi tare da d'an yatsansa yace "uhm uhm ba kuka nace kiyi min ba tambayanki nayi kuma nake so ki bani amsa." Bayan hannunta ta saka ta goge fuskanta sannan ta ja hanci cikin dakushewan murya tace "wallahi uncle sa'ad ban sani ba i really dont know nima haka na tashi na tsince ni a wannan halin."
Hannayensa ya harde tare da dora habbansa a kai yace "maimuna ban gane ba? Toh hannun waye wayarki ta shiga ranan da abin ya faru garin yaya kika bari aka dauke ki haka har aka samu daman bazawa?"

Kuka ta fashe dashi tace "ah ah fa uncle ah ah bani bace ba fa,wallahi uncle bani bace face din ne dai kawai nawa amma wallahi bank bace." Gyada kai yayi yace "i thought as much amma ke maimunatu wa kika tsokana haka da har za ayi kokarin getting back at you ta wannan hanyan?  Yarfe hannunta tayi tace "wallahi uncle ni bana kula ko balle in yi fada da wani ban san wa ya aikata min waannan danyen aikin ba...." Nan ta kwashe mishi halin da take ciki a makaranta.

"Toh me yasa baki picking calls?  Tabe fuska tayi tace "uncle ni ban san me zance Bane. "
"But that was very wrong kin daukan wayan na dai dai da kin admitting kin aikata laifin ne" kuka ta kara fashewa dashi tana yarfa hannunta "nashiga uku uncle wallahi ban aikata ba."

Hanki ya fitar a aljuhunsa ya goge fuskarsa yace "kar ki damu maimuna ko wani dan adam da kalar tashi jarabawar ke kalan naki kenan ki roki Allah ya baki iko da daman cinye wannan jarabtar,daddynki ya turo ni ne dan in dawo dake yace yana ganin zai hakura da makarantar ki ya mikk aure kawai."

Dafe kirjinta tayi tana salati yau ta shiga uku kafin tayi magana yace "saboda haka in kina da wansa kike so ki gabatar min dashi in kuma babu sai ki gaya min in san abinyi."

Shiru tayi tana tunanin Marwan,yau ga dama ta samu amma babu marwan,bata san halin da yake ba,bata san matsayinta ba a wajenshi a halin yanzu,shin wani amsa ya kamata ta baiwa uncle sa'ad?

"Ke nake sauraro maimuna!" Uncle sa'ad ya katse mata tunani gyaran murya tayi sannan ta kara sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta cikin sanyin murya tace "babu kowa uncle."
Gyada kai yayi yace "Allah ya kyauta,yanzu yaushe zaki gama jarabawar?"
"Nan da six days" ta bashi amsa. Good before then ni kuma zan yi kokarin ganin na karban miki transfer dan ki koma tsohon university din da kike karatu ki cigaba in har nayi nasarar shawo kan daddynki saboda haka kiyi kokarin ganin cewan baki bani kunya,zan shiga maganan nan ne dan na yarda da tarbiyarki maimuna na san ba zaki taba watsi da tarbiyar da muka yi miki ba." Gyada kai tayi tana me jin kunya watsi da tarbiyarta wajen biye marwan suna fasadi gashi yau marwan din ya gujeta babu shi bau labarinsa yau fiye da sati uku,yah Allah ka yafe min shine abinda ta fada a zuciyarta.

Maimunatu ta zage dantsa wajen ganin jarabawarta ya kara kyau dan kar ta ba uncle sa'ad kunya yayin da shi kuma yake ta faman zirga zirga yana ganin hukumar makarantan dan  ganin an bata transfer ba tare da an mayar da ita baya ba gefe daya kuma ya kaiwa company din layin da take amfani dashi kukan abinda ya faru da ita.

Bincike suka yi mishi sosai inda suka tabbatar mishi da cewan wani da basu sani bane ya hacking layin nata har ya aikata mata haka suka kuma nemi yafiyarta dan hackers da yawa na waje suna aikata barna.

Da wannan shaidar hankalin uncle sa'ad ya kwanta ya san shawo kan mahaifinta yanzu ba mai wahala bane. Cikin sati biyu maimunatu ta hada komatsanta suka yi shirin tafiya gida Nigeria.

A hanyarsu ta zuwa air port take tunanin yaushe zata samu ilimi me  inganci yau tana nan gobe tana can? Kallon garin take ta window din motar inda suke wuce wajeje da yawa da marwan ya kaita.

Lallai marwan cikakken mayaudari ne yau da ta sakar mishi jiki ya aikata zina da ita da ya ci banza ya barta da dora hannu a kai tunda yau gashi an wayi gari marwan ya gudu ya barta,for the last time ta dailing number dinshi labarin dai daya ne number din is switch off murmushi ta saki dan dama ta san abinda zata ji kenan ba tare da tayi tunani komi ba ta wurgar da wayar kan titi mota ta bi ta kanta a firgice jalila ta kalleta amma bata ce mata komi ba.

Ta yar da wayar ne dan bata son kullum ta cigaba da kiran layin marwan tana ji a kashe yanda ta yar da wayar nan haka zata bar tunanin marwan ta shafe babin rayuwarta da marwan har abada zata cigaba da neman tuba wajen Allah akan abinda suka aikata ita da marwan zata dawo da rayuwarta kwatankwacin na da abu daya ne ba zata cigaba da yi ba shine hana kanta farin ciki.

Zata inganta rayuwarta da ibada hade da neman ilimi kuma zata cigaba da kasancewa cikin farin ciki tayi hulda da mutane sannan babu wani da namijin da zata bari ya shigo rayuwarta tayi karatun halayen da namiji ba zata bawa ko wani irin namiji daman da ta baiwa marwab ba......

KINA RAINAWhere stories live. Discover now