💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad. @sawwama14
Page 23
Da mamaki suke kallon juna can sai kuma ta saki murmushi tsugunawa tayi tare da tattara abubuwanshi da suka watse a kasan feet dinshi har lokacin bai ce komi ba bai kuma motsa ba sai kallon ta da yake yi kawai.
Mikewa tsaye tayi tare da bawa mutane hanya kasancewar a dai dai entrance din suke tsaye wani ne ya dan matsar dashi daga hanya ganin bashi da niyyan matsawa sai a lokacin ya tattaro duk wani yawu da ya rage a bakinsa yace "maimunatu?" Ya fada ta sigan tambaya dan kara tabbatarwa kansa
Dan baya ya koma tare da fad'in "wow! Oh My God! I cant believe this." Hannunsa daya ya sa ya dafe bakinsa yayin da dayan hannun ya rike kugunsa dashi "my God! You have grown up and turn into a beautiful woman! Yah Rabb!" Dariya tayi tace "now that hurt kenan da bani da kyau."
Dan komawa baya yayi yana kara kare mata kallo sai da ta tsargu yace "no baki gane then u were a kid bu now..... Wow! I cant say,i dont know whats hidden beneath this baggy gown but right now what i see is a grown up beautiful lady." Sosai maganarsa ta daki zuciyarta so all thia while kallon yarinya yakr yi mata bai kalleta a matsayin mace ba sai yau?Murmushi tayi tace "dan Allah bari,wani in yaji ka sai yayi zaton rabon da ka ganni tun ina shekara 8 ne ba 18 ba."
Girgiza kai yayi yace "17" a dan cikin rashin fahimta tace "sorry?" Dan hadiye yawu yayi yana kallon kyakyawan fuskanta babu abinda ya canza sai dan kumatu da tayi "i mean kin tafi shekarub ki 17 not 18." Dariya ta yi tace "toh naji almost all the same dictective dan fulani."
"Ahhh so kin san ni wanene?" Ya tambaya knowing the answer already waye bai san shi ba a arewa maybe da wasu sashi na nigeria
Dariya tayi tana gyada kai dan waige waige ya fara kafin yace "akwai wani coffee shop a kasan nan not very far from here ina ga mu karasa wajen because there are a lots of question i want to ask you,sai dai in ko kina da abin yi yanzu?" Ya tambayeta girgiza kai tayi tana mishi mirmushin da ya lura yanzu its always on her face unlike da, da kullum fuskanta a hade and she always looked distant.A hankali suka fara taka hannunsa sike cikin aljuhu yayin da nata yake rike da purse dinta tare da ledansa da taki yarda ta bashi.
"So yaushe kika dawo?" Ya tambayeta suna kokarin shiga cafe din daga kai tayi tana kallon farin fuskansa dake dauke da dogon hanci madaidaitan idanu tare da kwantaccen bakin saje tace "ai ina ganin ko shekara biyu ban yi a can ba na dawo." Da mamaki yaje kallonta har ya ja mata kujera ta zauna shima ya zauna.
Sai kallonta yake yi not sure what to ask her next rufe fuskanta tayi tana dariya tace "wannan kallon fa?" Kyafta idanu yayi tare da kawar da kai yana murmushi bai son kallon yayi yawa haka ganin abin yake yi kaman a mafarki wai yau gashi ga maimunatu he never thought zai kara ganinta.
"Ai toh mamaki nake yi da kika ce wai baki yi shekara biyu a can ba,toh karatun fa?"
Daga kafadu tayi tace "na zo na karasa a nan yanzu haka ma service nake yi though ban fara ba sai monday"
Ta bashi amsa a nitse,relaxing yayi a kujerarsa yace "ahhhh kune batch din da suka fito daga camp kenan?" A hankali ta gyada mishi kai.
"So what happened?" Ya tambayeta yana kallon kwayar idonta kau da kai tayi sannan ta kuma dawo da kallonta kanshi tace "what happened what?" Daga kafadu yayi yace "what happened kika baro can kika karasa karatunki a Nigeria." Tabe baki tayi tace "nothing really haka nan daddy yace in dawo kuma,you know how he can be." Ta bashi amsa ba tare da taje details din abinda ya dawo da ita ba,there is no need of that."