💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 34.
Kyakyawan mari ta watsa mishi tare da binshi da wani mugun kallo shima ranshi a b'ace yake kallonta tofa mishi yawun bakinta tayi tare da goge bakinta da bayan hannunta. Cikin mugun mamaki yake kallonta muryarta a dakushe tace "kana ce kowa dan iska ne irinka? Ko dan kayi amfani da damar da ka samu a shekarun baya ka lalata min rayuwa kana ce na cigaba da harkar da ka dora ni akai ne? Toh albishirin ka Allah ya kubutar dani daga mugun tarbiyar da ka d'ora ni kuma kayi kadan ka mayar dani ruwa marwan sannan one more thing mazan dake rayuwata ba fasik'ai bane irinka."
Daga haka tayi kokarin rab'awa ta gefensa ta wuce damkota yayi ya mayar da ita jikin bangon da karfi har sai da files din hannunta suka zube kokari yake su hada ido amma sam taki sai ma kiciniyar kwace jikinta da take yi.
Cikin muryan da ta san yana using in ranshi ya kai kololuwa wajen b'aci yace dan sosai maganganunta suka kona mishi rai duk da ya san rabi a kan gaskiyarta take"listen here maimunatu,ki san da wa kike magana bar ganin nonuwa sun kara cika kirjinki nine dai marwan da kika sani babu abinda ya canza na daga zafin raina sam ba zan dauki raini a wajenki ba,ke ko kunya ma baki ji kina kirawa kanki wai mazan da ke rayuwanki,maza nawa ya kamata su kasance a rayuwar diya mace da ya wuce namiji daya? And believe me ba Tahir ba,ba shi wannan da ya tafi ba,babu dan iskan da ya dace da rayuwarki a cikinsu in ba ni ba,ni ne first love dinki nine wanda jikinki ya fara sani and nine farin cikinki kaman yanda kece tawa,i fucking own you and you know damn well ki gayawa duk wani shege ya tattara tsumman rayuwarsa ya fita a sha'aninki tun ban dau mummunan mataki ba." Ya fada cikin matsanacin tsawa.Sosai maimunatu ta tsorata amma ta dake wani irin yawu me kauri ta hadiye kafin ta kwace jikinta kasancewar ya sassauta rikon da yayi mata cikin kyafkyafta ido tace "wallahi ni ba mallakinka bace,in akwai wanda ya kamata ya fita a rayuwana toh kaine dan duk tare kazo ka sameni dasu and you dont get to choose who is in my life,you dont get to decide for me ka rabu dani da su..." Ta fada muryarta na rawa.
Dan sassauta murya yayi yace "eh nazo na same su amma i was here before them ni kike so ni kika fara so..."
Cikin sauri ta tari numfashinsa tace "Ba kaine first love dina ba,ba kai na fara so ba,khalid was here before you,shi na fara so kafin kai i am not even sure if what we had was love not lust."Cikin daga murya yace "karya kike ni kika fara so dont even try to play games with me,yes we have chemestry but what we had and still have is love not lust." Ya karasa maganan cikin sanyin murya.
Dan tsaki taja tana so ta samu hanya ta wuce amma yayi baka baka sai ma mata katanga da yayi da hannayensa ta hanyan dafa bangon matso da bakinsa yayi dai dai kunnenta tana jin dumin numfashinsa nan da nan tsigar jikinta ya fara tashi cikin wani kafirin murya yace "miemie ina sonki pls ki ya hakuri koma fushin me kike yi ki ajiye shi na tuba." Ba tare da ta san shirinsa ba sai jin lips dinsa tayi a gefen wuyanta idanunta da kashin kansu suke son lumshewa saboda kasalan da ya sakar mata.
Wani kuzari ta tattaro ta hankadasa tana binsa da wani irin kallo tace wai kai me yasa babu Allah a ranka ne?" Waro idanu yayi shi fa ya kasa daina mamakin wannan sabuwar miemie din tasa "miemie nine babu Allah a raina?" Ba tare da wani shakku ba tace "yes! Cos in akwai Allah a ranka zaka ji kunyansa wajen dakumata tunda ai ba kudina ka biya da zaka dinga kai hannunka jikina anyhow."
Murmushi yayi tare da harde hannunsa a kirjinsa yace "kina so in kai kudina gidanku ne?" Wani uban harara ta watsa mishi tace "ko maza sun kare!"
Maimakon furucinta ya bata mishi rai sai ya saki yar dariya yace "ho ni marwan! Ko meye laifina a wajen wannan yarinyan sai Allah."
Tabe baki tayi tana jinjina rainin wayon marwan"Miemie da gaske meye laifina?" Ya tambayeta in a serious tune.
Idonta ne ya kawo kwallah amma bata ce komi ba sai ma fizgan kofan da tayi ta fita a hanyan hawaye ne kawai ke sintiri a idonta marwan ya mugun raina mata hankali wato ma menene laifinsa a wajenta tunda shi bai ga ya yi mata laifi ba itama ba zata taba ce mishi ga laifinsa ba dan da alama dariya zai yi mata tunda ta bashi matsayin da shi bai bata rabinsa ba.A haka ta gama aikinta na ranan ba tare da ta kara sashi a ido ba amma maimakon hankalinta ya kwanta ma sai gaba daya ta rasa nutauwarta she wished a reception yake zaune da tayi ta zirga zirga ko dan ta rinka ganin shi ita da kanta tayi Allah wadai da irin zuciyarta.
Marwan kam bayan fitan maimunatu shiru yayi yana tunanin me yayiwa maimunatu da zafi haka take nuna mishi wannan kiyayyan shi ya sani ya tafi ya bar maimunatu cikin tsananin sonshi da kewarsa amma yazo ya tarar da akasin haka yanzu in tana fushi da tafiyarsa ne kamata yayi ta tsaya ta ji uzurinsa kafin ta yanke masa hukunci. Toh ko da gaske ta daina sonshin ne? No no no yana da tabbacin har yanzu tana sonshi ko da kuwa ba kaman da ba, "na shiga uku who is this fucking of a khalid?" Ya fada a fili cikin tashin hankali a kasan office dinsa ya zauna tare dafe kansa ya rasa tunanin da zai yi he is ready to fight the world for his miemie..........
Manage this ba karamin kokari nayi ba😂