💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 35
Ya dad'e a zaune yana tunanin ta inda zai fara shawo kan maimunatu ya kasa karshe tashi yayi ya zari makullan motar sa ya fita bai wuce ko ina ba sai main house.
A zaune ya sami mami a palo daya daga cikin ma'aikatan gidan tana jera mata fruits a kan darduma a hankali ya cire jacket dinsa ya ajiye kan hannun kujeran kafin yaje ya kwanta a kasa kan darduman tare da kwantar da kansa bisa kafar mami dake mike hannunta ta dora bisa kansa tana shafawa tace "Marwan sai ka karasa kafar kaji dadi ko?"
Maimakon ya tura baki yayi mata shagwabar da ya saba sai taga ya lumshe ido kawai yayi ganin hakan da tayi ta san babu lafiya,shafa kansa ta cigaba da yi a hankali kuma tana karanta mishi addua.
Fahimatan da yayi na cewan addua take mishi ya saka shi kama "Allahuma ajirni fi musibatin wa akhlifni khairan minha."A hankali yaji nutsuwa na ratsa zuciyarsa har wani bacci me dadi na dan fuzgarsa a hankali tace "maza marwan tashi kaje kayi wankan juma'a" bude idonsa yayi yana kallon fuskarta da ke dauke da kulawa murmushi ya sakar mata tare da cewa. "Thank you maminah" itama murmushin ta sakar masa tace "kul! Kar in kara jin kalmar godiya a bakinka,in uwa bata tsaya kan ya'yanta ba wa kake tunanin zai tsaya kansu."
Haka kawai ya sami kanshi da mayar da kanshi ya kwanta kan cinyarta a haka daddy ya fito ya samesu kallo daya zaka yi masa kanhango tsananin kamansa da yaransa musamman manyan idanunsa da yake dauke da su da dark skin dinsa.
Murmushi yayi yace "haba no wonder aka barni ina ta kiciniyar shiri ni kadai ashe dan gaban goshi na kusa." Tashi yayi zaune yana murmushi yace "daddy ashe kana ciki? Barka da war haka.""Ina ciki,likita,soja kuma dan kasuwa,anya na taba ganin had'amemme irinka ka kuwa marwan?" Tura baki yayi yace "daddy ai a cikin sojoji akwai likitoci ni kuma kasuwanci ba ra'ayina bane."
Daga kafad'u daddy yayi yace "oho dai ra'ayinka ko ba ra'ayinka ba babu wanda zai maka wahala,wai auta ma da kananan shekarunta ka bata gurbi me nauyi."
Tab'e fuska yayi yace "toh daddy ya zanyi? Kannena are hard working."
"Sosai kuwa dan in ba dan su ba da kamfanin tuni ta rushe." Cewar daddySai lokacin mami dake kallon draman nasu tace "ah ah fa dear marwan na kokari shima yana shiga sabgogin company din sosai duk da abubuwan da ke kanshi ga aiki ga kasuwanci ga ginin asibiti haba ai ko dan nawa na kokari sosai."
Mikewa tsaye daddy yayi yana kara saba babbab rigarsa yace "ai ke dama baya laifi a wajenki ni na shiga cikin gari sai na dawo."
A dawo lafiya suka mishi ya sa kai ya fita mayar da kallonta kan marwan tayi tace "babana kai va zaka tashi kayi shirin masallaci ba? Har ya mike ya koma ya zauna tare da kallon wrist watch dinsa ya mayar da hankalinsa kan mami yace "mami ina da matsala."
"Subhanallah me ya faru?" Numfashi ya sauke tare da tankwashe kafafunsa yace "mami ina yarinyan da nace miki ina so tun shekarun baya?" Cikin zumudi tace "eh eh na ganeta,ta gama karatun ne,ko me ya faru?"
Limshe idanunsa yayi yace "mami na ganta but taki saurarata."Cike da confusion tace "ban gane ka ganta ba kuma taki sauraranta dama ka ta bata ne ko kuma wani laifi kayi mata?"
Yace tohm mami gashi nan dai fa amm dama dama a cyprus ne,mmm"
Waro idanuwa waje mami tayi tace "ban gane dama dama a cyprus ba,marwan ba dai ka b'ata musu yarinyan mutane bane an turata karatu na san kadan daga aikinka."Kau da kai yayi gefe ransa na kuna ya san abinda ta fada gaskiya ne amma ai ya canza hali "mami ban b'ata ta ba fa ni but i almost did shine shine..." Ya sunkuyar da kai