💖KINA RAINA💖
By Sawwama A.
Wattpad @sawwama14
Page 31.
"Me kike nufi da zaki aureshi in ya aiwatar da abinda kika ce?" A firgice ta juyo tana kallon mubeena dake jingine jikin kofan office dinta ta hard'e hannunta a kirjinta fuskanta sam babu annuri.
A hankali ta sauke hannayenta kafin ta fara cire kafarta ta iso table din maimunatu ta kara maimaita tambayanta kafin maimunatu ta bata amsa ta cigaba da fad'in "maimunatu dont tell me kina so khalid ya watsar da wancan maganan auran nasa da ya rage saura kwanaki ke kuma zaki aureshi ne?" Zaro idanuwa maimunatu tayi tare da bude baki amma ta kasa cewa komi ita sam wannan tunanin bai tab'a darsuwa a zuciyanta ba she is not that selfish ganin ta kasa magana yasa mubeena dafata cikin sanyin murya tace "ban taba yi miki wannan kallon ba,ban taba kallonki a matsayin mace me son kanta ba pls kar ki canza daga yanda na sanki,ka sowa dan uwanka abinda ka so wa kanka."
Murmushi maimunatu tayi tace "thank God kin shede ni sam ni ban cewa khalid ya fasa auransa ya zo ya aureni ba,mubeena khalid ya dameni sai na saurara shi bayan ya auri habiba ya aureni,ni kuma nace mishi ya sanar da habiba da iyayensa in sun amince nima na amince zan aureshi,na san ba zai taba iyawa ba shi ya sa nace mishi haka dan a zauna lafiya."
Shiru Mubeena tayi tana kallonta a hankali tace "Allah yayi zab'i,duk yanda nake sonki da khalid ban so ki zama silan bacin ran wata." Wani kallo maimunatu tayi mata can kuma ta saki murmushi indeed ciwon ya mace na ya mace ne.
"Ke yanzu in ya nemi yardansu suka yadda zaki amince ki aure shi?" Dan d'aga kafadu maimunatu tayi tana idonta kan computer da take kokarin kunnawa tace "abu ne mai wuya su amince shi yasa ma nace mishi hakan." Numfashi mubeena ta sauke tace "what IF suka amince?" ta emphasising akan if din tabe baki maimunatu tayi tace ba tare da ta kalli mubeena ba "sai in aureshi." Zaro manyan idanunta mubeena tayi tare da rufe bakinta da tafukan hannunta tace "wow! You love him!" Rolling idanunta maimunatu tayi tace "ke dai wallahi." Da dan yatsa mubeena ta nunata tace "so you love him all this while kike denying har ma da ce min kina da wanda kike so,wallahi maimunatu kinji haushin kanki."
Maimunatu bata ce mata komi ba sai da ta connecting tab dinta da system dinta sannan ta juyo tana fuskantar ta dan shagwabe fuska tayi tace "i cant believe ni boss dina ke hana ni aiki." Ta fada kaman zata yi kuka.
Kankantar da idanu mubeena tayi can ta saki wani marayan kukan shagwaba kafin ta bubbuga kafanta tare da barin wurin ta shiga office dinta har da banging kofa,murmushi mai fadi maimunatu tayi sannan ta juya ta cigaba da aikinta sam taki bawa tunani muhalli a brain dinta bata so ta tuno abinda ya wakana a yau din har sai ta je gida ta nutsu.
Ta dan aiwatar da aiki taji kanta na mugun sarawa lokacin ko la'asar ba ayi ba kifa kanta tayi a jikin table dinta tana mayar da numfashi d'ai d'ai a wannan halin mubeena da ta fito tambayanta abu ta sameta,dan is hardly kaga mubeena ta kira maimunatu office dinta sai dai in aiki yayi mata yawa amma duk abinda take so zata zo ta amsa ta koma ita dai haka kawai Allah ya saka mata soyayyar maimunatu.
"Subhanallahi! Maimuna me ya sameki?" Ta tambayeta tare da daura hannunta bisa jikinta dago da kanta maimunatu tayi tana lumlumshe ido tace "wallahi ki bari fa magrain tashi daya."
"Innalillahi sannu ina ga ki tafi gida ki samu kisha magani stress ne zuwa gobe inshaaAllah u will be alright." Gyada kai maimunatu tayi ta fara tattara kayayyakinta tana yiwa mubeena bayanin abubuwan da akwai.A daddafe maimunatu ta koma gida ko wanka bata iya yi ba taci abinci ta sha magani sannan ta kwanta bacci ne mai nauyi ya dauketa cike da mafarke mafarke!
Marwan bai samu sukuni ba saboda aiki da rincabe mishi ga na oficce dinsu ga na company dan shi sam bai cika waiwayan company din ba sai in abu yaci tura.
Zaune yake a cikin wawakeken office dinshi tuni ya cire jacket din suits dinshi daga shi sai light ash colour shirt hatta necktie din sa ya cire ya balle bottuns uku na saman rigar gaba d'aya ya rasa tunanin da zai yi ganin maimunatu ya rikita masa lissafi ya ganta a lokacin da yake da tsananin buqatarta a rayuwarsa sai dai me? Ganin nata ya zo mishi da kalubalen da bai taba tunani ba. Ya rasa fushin menene take yi dashi haka? Ya rasa menene laifinshi a wajenta.
Shi ya kamata yayi fushi,shi tayiwa laifi ta tafi ta bar cyprus without a second glance in da ka san bata taba rayuwa a cyprus ba sam babu alamunta wani son ganin ta yaji tsam ya mike can kuma ya koma ya zauna ganin da yayi mata ya tabbata wannan ba maimunatun da bace wannan is a wild cat ba zai so yan uwanshi su san da maganan maimunatu ba har sai ya shawo kan abarsa he is very sur hakan ba zai yi mishi wahala ba,duk tsagerancinta ya san tana mugun shakkansa kuma ko ba komi akwai soyayyarsa a cikin zuciyanta wannan zai taimaka mishi wajen shawo kanta murmushi yayi tuno da kalmar dan iska da ta kirashi eh din yaji shi dan iska ne kuma wallahi sai taga iskanci.
Kyakyawar wayarsa ya dauka wanda ke zaune bisa table dinsa direct email dinsa ya shiga inda ya fara lalubo hotunanta na da a hankali yake kallo yana ganin bambancinta da ganin da yayi mata yau a hotunan babu komi bayan yar yarinya mai dauke da tarin yarinta a wancan lokacin ba karamin appreciating surarta yake ba amma ganinta shi da ita yau ya sare sai yaga da ba komi ma take dashi ba yanzu ne ta mallaki abubuwan da za a kira kaya.
"Damn!" Ya furta tare da mayar da kansa jikin tattausan leather seat dinsa ya limshe ido yana shafa kirjinsa da hannu daya shi kadai ya san tunanin da yake kai kawo cikin brain dinsa "he have to win her back,he have to have her!" Abinda yake ta nanatawa kenan sam Taheer is not a threat to him Taheer bai isa su had'a nema dashi ba,ya san Tahir ya san wanene Taheer kar yake kallonsa.
Maimunatu bata farka ba sai dab da magrib Allah ma ya sa ba sallah take ba,alhamdulillah ciwon kan ya sauka wanka ta fara shiga ta kintshe kanta sannan ta saka irin over size t shirt din nan sannan ta zauna tana duba missed calls dinta kiran Taheer,mubeena da khalid ta gani sai message daga wajen khalid da yake mata ya jiki dan ya bi office suka hadu da mubeena take gaya mishi ,reply tayi mishi da taji sauki ta gode.
Daga nan ta bi bayan kiran mubeena sun dan taba hira kiran Khalid ya shigo wayanta shima basu wani dade ba dan ana shirin shiga sallah time din.
Tana ajiye wayar ta tashi ta nufi kitchen ta samu an riga an gama abinci fruits salad kawai ta deba me sanyi dan sam bakinta babu appetite tana fitowa momy itama ta fito tana sanye da hijab da alama sallah tayi ko zata yi "sannu da gida momy" shine abinda tace tana kokarin wucewa
"Keh! Ke nayiwa fruits salad da zaki je ki deba baki tambayeni ba?" Dan daga gira daya maimunatu tayi da alama yau rigimar ta momy ta motsa in ba haka ba ai a cikin saura ta deba ba na cikin bowl dinsu ba.
"Ba dake nake magana ba kin mayar dani sakara? Wato ke rashin kunyanki gaba gaba yake ko saboda kinga tsawonmu ya zo daya muna gogan kafadan juna?"
"Toh fah!" Shine abinda maimunatu ta furta
Momy na shirin kara magana daddy ya shigo yana fadin "yaya ne haka nake jin hayaniya? Wai me kuma ya faru?" Cikin tsananin bacin rai da bata san a ina momyn ta aro ba tace "wai daddy ka duba yarinyan nan sam babu da'a a tattare da ita kaman maimuna da girmanta ta dinga yin abu kaman mara wayo yaya zan hada maka abu taje tana deban son ranta ba tare da ta tambayeni ba,ni boyi boyinta ne? Duk kokarin da nake yi kan baby wani sa'in sai ta nuna rashin tarbiya in ita ba zata taimaka min ba ai sai tayi nata ko?"Sam daddy bai ga abin fada ba a nan kuma sosai yaji wani iri da ta kira mishi yarinya da mara tarbiya yace "dear kiyi hakuri,ke kuma maimunatu" ya juyo kan maimuna dake kallon wannan draman baki a bude "sam baki kyauta ba in ba zaki tayata aiki ba sai ki tambayeta kafin ki debar mata abu." Ciki ciki momy tace "ai ba laifinta bane taga kanmu ya zo daya ne." Cikin dan hasala daddy yace "haba Rahina ya zaki dinga magana irin haka? Ke ba mahaifiyar maimunatu bace in tayi abu ba dai dai ba ke ba mai tsawatar mata bane? Haba! In aure kike so tayi ke ba mai zaunar da yarki kiji manemanta bane? Nifa bana son shashanci,ke maimunatu wuce kije ki fara tunanin wa zaki fitar a manemanki ai na san dai ba ki rasa masoya ba........"