page 19

1.7K 148 27
                                    

💖KINA RAINA💖

By Sawwama A.



Wattpad @sawwama14.




Page 19.








Lumshe idanunta ta bude su tar tayi lokacin da ta shaki iskan kasarta,kaman jiya ta tafi yau gashi ta dawo. A hankali take taka matattakalan tana bin bayan uncle sa'ad a haka har suka sakko suka yi abubuwan da ya kamata suka bar air port din zuciyarta na lugude tana tunanin ya zata fuskanci daddynta.

Addu'a ta kama a bakinta tana neman tsari a wajen Allah. Bayan hannunta ta saka ta goge idanunta tapping dinta   uncle sa'ad yayi tare da furta mata "ki riki Allah komi is going to be alright." A hankali ta nodding kanta.

Suna isa gate din gidan gabanta ya tsananta faduwa  a hankali ta saka kafanta ta fito daga cikin taxi din da suka renting ta fito tana kara kama duk adduar da tazo bakinta ji take yi kaman ta sa gudu,toh ta gudu taje ina? Wani gata take dashi da ya wuce daddynta? Bata da wani strong bomd da dangin mahaifiyarta saboda daddynta da momy sunyi kane kane a rayuwarta. Ko hutu bata zuwa musu sai yau kawai ta debi jiki taje lokacin da take da matsala? Will they even believe cewan bata aikata laifin da ake tuhumarta da aikatawa ba?

Dafa kafadunta da uncle sa'ad yayi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Dan tattare girarsa yayi yace "baby ba na hanaki tunanin nan ba at this tender age ki dami zuciyarki da kwalkwalwarki da tunani? Sam bana son kara ganin haka in kina so mu shirya. Ko kina in cire hannuna a lamuranki ne?" Da sauri ta girgiza kai tana kokarin mayar da hawayen da yake zuwa mata dan ta san hakan na iya kara bata mishi rai.

"Good" shine abinda yace dan waigawa tayi tana karewa tulin kayanta da taxi driver ya sauke har ya tafi bata sani ba ta tafi duniyar tunani.

Alamu uncle sa'ad yayi mata da hannu na ta fara yin gaba wani kakkauran yawu ta hadiye sannan ta fara taking steps a hankali bakinta na dauke da addua kaman wacce za a sadata da mutuwarta.

A hankali ta murda kofar da zai sadaka da babban palon gidan da daddynta ta fara cin karo yana zaune cikin daya daga cikin kujerun palon yana karanta news paper, waro idanunsa yayi a kanta kaman wanda yake mamakin ganinta ita kuma ta tsaya cak ta kasa gaba ta kasa baya bata ankara ba taji ya eurgo mata flower vase din dake kan side table din dake gefen kujeran da yake zaune da sauri ta koma baya tare da dodging wa vase din tatsatsa yayi a kasan tiles din wajen. Uncle sa'ad ne da yake bayanta ya dan ingizata gaba ta kuma shiga palon. Kau da ita gefe yayi cikin bacin rai yace" Abdul wani irin abu ne haka da ya sameta taji ciwo fa?"

Shima cikin tsananin fushi yace "ai gwara ya sameta ta ji ciwon ko zan huce haushin ni ciwon da ta saka min a zuciya,haba ace yarinya kaman maimunatu ta san shedananci toh ni ban bawa iyayena wuya ba itama ba zan nari ta wahalshe ni ba,na dauketa a Nigeria saboda kar soyayya ya rufe mata ido sai taje ta kama iskanci? Haba sa'ad haba! Wallahi ba dai dani Abdullahi za ayi danyen aikin nan ba. Ai da tayi zamanta a can da sabbin mutanen da ta zaba a matsayin abokan rayuwarta wai har ni zan kira yarinyan nan taki daukan wayana for more than 3 weeks saboda ta mayar dani sa'anta wallahi kaji na rantse maka sa'ad ni har na hakura da maimuna tunda ta zabi zaman can da rayuwa dasu da halayensu fiye dani ta nuna min fita da ita waje karatu da nayi ba gata nayi mata ba." Daga haka ya koma gefe yana ta haki kaman wanda yayi tsere maimunatu na tsaye tana ta aikin zabga kuka.

Kama shi uncle sa'ad ke kokarin yi ganin yanda yake muzurai amma sai daddy ya fizge jikinshi kaman qani yaro, da dan yatsa ya nuna uncle sa'ad  yace "sa'ad matsawar kana son tarayyar mu ta cigaba toh lallai ka fitar min da wannan annobar a gidan."

"Subhanallahi Abdul bar aibata diyarka haka mana." Cewar uncle sa'ad
Rintse idanu daddy yayi yace "wato dai ba zaka fita da ita ba sai na maka radhin mutunci ko?" Ganin yanda jikinsa ke bari dan tsananin bacin rai ya sa uncle s'ad kama hannun maimunatu dake ta faman rusan kuka ya fita da ita daga palon suna fita ya sake ta yana zarya a tsakan compound din gidan.

Maimunatu kallonsa take ta tsakankanin jikakken lashes dinta tana mamaki da tunanin ashema ba daddy bane ya sa a dawo da ita ba in ta shine kar ma ta dawo. Innalillahi me ta aikatawa rayuwarta haka? Kuka take sosai.

Tana kallo ya fito da wayarsa tare da danna kiran wani number sannan ya manna a kunnensa dayan hannunsa na rike da kugunsa yana zagaye gidan bai dau lokaci ba ya gama wayar ita dai tana rakube a gefe tana jiran taji me zai ce mata next.

Duk abinda ake yi a kan idanun momy aka yi tana kallo fuskarta dauke da kayataccen murmushi she feels this time around she has won tayi nasaran raba mijinta da diyarsa ba tare da ta bi boka ba balle malam sannan ta san babu wanda zai zargeta da rashin bawa maimunatu tarbiya she hope and pray saurayin da ya shigo cikin rayuwar maimunatu ya daidaita mata tarbiya.

Dakinta ta fada a guje tare da danna kiran wanda ta sashi aiki cikin tsananin farin ciki tace "good job! Aikinka yayi kyau,ko da yake daman bana tantama akan cewa aikin naka zai yi kyau saboda yanda ka tsara komi." Dan shiru tayi tana sauraran abinda na dayan bangaren yake cewa can ta saki murmushi tace "sosai kam ka burgeni wannan lokacin saboda haka ka saurareni nan da wani dan lokaci zaka ji alert." Daga haka suka yi sallama duk maganan da suke yi cikin halshe turanci suke yi

Ba a dau wani lokaci me tsawo ba aka yi horn me gadi yaje ya bude gate wani mota ne me kyau na yayi ya shigo cikin harabar gidan tun kafin motar ta gama parking uncle sa'ad dake tsaye gabanta yana bata baki ya rabu da ita ya karasa inda motar take.

Bude murfin motan aka yi wani kyakyawan magidanci ne ya fito daga ciki yana sanye da kaftan karamin dinki a jikinsa.

Can kasan breath dinta ta furta "uncle sufyaaaan." Da sauri sauri gudu gudu ta karasa gabansa tare da.....

KINA RAINAWhere stories live. Discover now