page 44

2.2K 287 125
                                    

💖KINA RAINA💖










By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14








Page 44.

Ahhhh malam meye haka ka sakeni man, me nayi maka?  Badamasi ya fada cikin tsananin jin zafi amma bai yi kokarin kwatan kansa ba dan ya san motsi kadan zai yi yaji masa rauni.
Maimunatu ma cikin kidima da takaici ta kara matsawa kusa dasu tace "marwan meye haka? Sakar mishi hannu mana,me yayi maka ni ban son tsaban salon mugunta ka sakar mishi hannu."

Hayaniyarsa ne ya saka mama da aunty khadija fitowa ganinsu ya sa marwan sake badamasi sunkuyar da aki aka bar badamsi da yarfe hannu yana aikawa da marawan wasu uba uban harara amma ba daman karasawa kusa dashi saboda yanda yayi masa kwarjini duk wannan hararar ma bai iya kallon idanunsa.

"Me ke faruwa haka nake jin hayaniyarku,bawan Allah lafiya?" Mama ta wurgawa marwan tambayan da ya sashi rasa nutsuwarsa mai da kallonsa kan maimunatu yayi tare ds dan marairaice mata harara ta banka masa ta kawar da kai yayin da badamaai ya ke kora musu bayani "kawai fa muna tsaye da maimuna ta fara tari shine nake buga mata baya ban ankare ba kawai naji wannan mutumin yana kokarin raba min hannu biyu ban ma san daga inda ya fito ba. Maimuna ko ke kin sanshi dan naji kaman kin kira sunanshi?"

Duk suka zubo mata idanu,diri diri ta fara tana daga hannu bakinta na motsi amma ta ma rasa me zata ce,toh me ma zata ce din ta san shi ko me? Shine wanda yake sonta ko wanda suke son juna? Ita bata san irin marwan ba bakar zuciyarsa sometimes makes behave like a lunatic haba ayi mutum ba hakuri.

Dan kankantar da idanu aunty khadija tayi tace "ko kaina marwan?" Da sauri ya daga kai tare da sauke wani irin ajiyar zuciya dan shi kam kunya duk ta rufe shi gaba daya al amarin yarinyan na sashi rasa hankalinsa da nutsuwarsa bai iya controlling kansa a duk wani abu da ya shafeta ta ko wani fanni.

"Haba ko da naji wannan aikin masu kishi ne,kai kam badamasi barkanka da ba a raba ka da hannunka ba ina kai ina taba budurwar soja, malam marwan bismillah duk munyi tsaye a waje ai tun jiya yah Abdul yace min kana hanya.

Zunguro baki maimunatu tayi tsaban takaici ta koma cikin gidan kafin kowa ma ya shiga ta shige dakin mama.

Sum sum marwan yabi bayansu yana kan scolding kanshi for his behaviour sai da aka sadashi da palon alhaji sannan aka gaisa mama tace "kai kuma daga zuwa zaka balla min hannun megida tunda kai ka riga ka zabi wancan uwar kuncin ko?" Sunkuyar da kai yayi yana murmushi cike da kunya yace "ayi hakuri hajiya akasi aka samu inshaa allah hakan ba zai kuma faruwa ba,ale Badamasi dan Allah kayi hakuri." Murmushin yake Badamasi yayi yace "ba komi" amma a kasar zuciyarsa yana yiwa kanshi da sauran samarin dangin jajen rashin maimuna duk wannan hadewar tata da ilimin ashe a wani wajen ake neman auranta su basu da rabo akanta tun ranan da suka iso ya riga kowa zuwa wajenta duk da miskilancinta sai da ya san yanda ya cusa kanshi a wajenta har suka dan saba a cikin kwanki biyu rak amma ashe wani ya riga ya musu shigan sauri.

Aunty khadija ne tace "kishi kan abinda kake so yana da kyau amma dai ayi me hankali shine dai dai."

Gyada kai yayi yace "haka ne nagode sosai." A ranshi kuma yana fadin wannan dince kanwar mahaifiyarta kenan tunda mama dai da alama ita ce kakar yayi mamaki dan sai yaga gaba daya ba zata fice sa'ar mufliha ba shiru suka dan yi kafin wani yayi magana ladan ya kwada kiran sallan zuhr dole Badamasi da Marwan suka mike dan zuwa masjid.

Mama kuma tayi tsakar gidan dan inda rana ne tafi jin dadin ta'amalinta a tsakar gidan yayin da aunty khadija ta shiga uwar dakan maman inda ta tarar da maimunatu ta fito daga bathroom din cikin dakin dauke da alaula bakin nan yayi gabas saboda yanda aka turo shi ga abu dan tsut sai ya kara tsukewa.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now