page 5

2.2K 146 39
                                    

💖KINA RAINA💖

By Sawwama A.

Page 5.

Murmushi yayi tare da furta abinda take kallo "happy birthday love"
Maimunatu bata iya cewa komi ba sai kallon sama da take yi inda happy birthday love ke ta fashewa cikin shape din heart a sama how on earth is that even possible tana ce a film ne kawai ake haka lallai marwan is something else.

Marwan! Yes Marwan har yanzu fa yana kan waya cikin rawar murya domin idanunta tab yake da hawaye tace "Marwan thank you! Thank you so much this means al lot for me." Shushsh shine abinda yace mata a hankali tace "amma me yasa marwan? Why?" Cikin sanyin murya yace because i love you miemie." Jan hanci tayi na kokarin hana kanta kuka tace "why me? I dont think i am upto ur standered why me ga mata nan kala kala a gari classy babes why me? I have nothing to offer Marwan."

Murmushi yayi yace "ni duk ban gansu ba ke na gani miemie and stop saying you dont have anything to offer you have a lots to offer you are unique in ur own way sannan ni ban son komi a wajenki just you."

Cikin sanyin jiki tace "but...." Katseta yayi da fadin "shuhsh dont day anything,no buts jeki samu ki kwanta ki huta tomorrow is gonna be a long day and i want you to enjoy every bit of it and zamu cigaba da maganan mu when the time is right just know that you are mine maymunatu mine alone!  Now go to sleep will see tomorrow"  daga haka ya katse kiran ya barta da waya a kunne tana mamakin tune din da ya using kaman wani yace zai kwace mishi ita murmushi tayi tare da kara kallon sama duk da abin ya watsa kulle window dinta tayi tare da yin tsalle tana juyi dan dama ita abu kadan zaka yi mata na kulawa ka siye zuciyarta bata raina kyautatawa time ta duba taga 1 saura da sauri ta hau gado tare da yin addua.

Rintse ido tayi amma bacci yaki zuwa sai ta rufe ido sai ta fara tuno kalamansa sai juyi take tana murmushi she cant believe ita ta manta yau za cika 18 years amma shi bai manta ba he is sooooo romantic she cant ask for more Allah yasa kar momy ta zuga daddy a kan marwan Allah yasa su barta ta aure shi.

Kunya taji ganin karama da ita amma ta fara tunanin aure kife kanta tayi a kan pillow kaman wani na kallonta da haka bacci barawo yayi awon gaba da ita.

Washegari da kyar ta tashi tayi sallah ta koma wajen ten door bell dinta ya tasheta bacci cike da idonta ta bude kofar ba ma tare da ta duba ko ta tambaye wanene ba.

Kyafkyafta ido yayi tayi tare da murzawa Marwan ne dai tsaye gabanta tabe baki tayi tare da turo shi,lakace mata kumatu yayi ya raba ta gefenta ya shiga dakin.

Dan juya idanu tayi ta shiga tare da rufe kofar haka kawai sai ta tsinci kanta da jin matsanancin kunyanshi ta kasa juyowa shi kam murmushi yayi ya shige kitchen dinta sai da taji burutunsa a kitchen tayi saurin shiga bathroom din zaro idanu tayi ganin yanayinta a mirror dogon wando ne a jikinta da ta saka saboda sallahriga ce mara nauyi a jikinta fara sannan kana iya ganin shatin nipples dinta saboda rashin nauyinta dafe kai tayi kaman tayi kuka tana kara karewa kanta kallo yanda gashinta yayi buya buya duk ya tashi sama tsaki taja kafin ta dau brush dinta ta bude tab ta wanke kafin ta matsa toothpaste ta fara brush bayan ta gama ne ta bude hakoranta tana kallon haskensu kara kallon kanta tayi tsaki wanka ta deciding tayi kofar bathroom din ta sakawa key kafin ta fara stripping kayan jikinta.

Wanka tayi cikin nutsuwa sannan ta goge jikinta cikin bathroom din ta mayar da kayan da ta cire a jikinta saboda dashin ruwan jikinta sai rigar ta kara lafewa a jikinta tsaki ta ja ta dakko bathrobe ta dora a kai.
Luckly tana da comb a bathroom din sai kawai ta combing kan nata tana shirin ajiye comb din taji knocking sai da ta firgita dan tsoro ta yar da comb din hannunta.

Gyaran murya tayi tace "ina zuwa" ko maganan ma sai da muryarta tayi rawa kara dan kimtsawa tayi sannan ta fito kanta a kasa ba tare da kalleshi ba tace ina zuwa tare da nufan bedroom dinta.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now