page 16

1.7K 146 19
                                    

💖KINA RAINA💖

By Sawwama A.

Wattpad @sawwama

Page 16.

Haka tana ji tana gani Marwan ya kulewa ganinta jiki a sanyaye ta fito daga cikin air port din sai sheshekar kuka take yi cab ta shiga tare da kurawa wayar ta ido dan yayi mata alkawarin in har wifi din airline din is available zai kirata har suka isa gidanta bai kirata ba.

Fita tayi tare da biyan me cab din sannan ta haura zuwa apartment dinta karo na barkatai ta kara duba screen din wayanta ga mamakinta sai taga yana blinking alamun akwai sako,kunnawa wayarta ta gani sai me missed call din marwan ta gani da mesaage daya cikin rawar jiki ta bude message din da yake layi daya
_on board! Called you, you were'nt picking. I love you!_ wani irin kuka ta fashe shi da shi musamman ma da ta gwada kiran layinsa ya ki zuwa cikin kuka ta unlocking kofanta ta shiga dakin ta fada kan kujera tana kuka ya yin da take kara kiran number dinsa amma baya shiga rike cikinta tayi tana tsananta kuka she cant believe ahe missed his call,bata san ya aka yi wayarta ta shiga silent ba har ya kira bata sani ba.

A wannan halin bayan ta ci kuka ta gode Allah bacci ya dauketa sai cikin dare ta farka tayi sallah kara gwada kiran layinsa tayi still a kashe sai wani sabon kuka har garin Allah ya waye bata samu daman komawa bacci ba wanka tayi da safen tayi shirin makaranta dan bata ga amfanin zamanta a gidan ba har wannan lokacin kuma number din marwan baya zuwa.

Bakin glass ta saka ta toshe idanunta saboda yanda yayi luhu luhu sanadiyar kukan da ta sha ga wani azababen ciwon kai dake damunta haka tayi classes cikin rashin lafiya da rashin walwala ta koma gida tana kan gwada kiransa amma baya zuwa sai sabon kuka ya barke nan da nan zazzabi ya rufeta.

Kwana uku babu kiran marwan sannan layinsa baya zuwa ga ciwo ga rashin mataimaki so kusan hudu on different occation tana jin door bell dinta amma bata iya tashi taje ta bude sam maimunatu bata jin dadin rayuwarta a kwana na hudun ne a daddafe ta mike dan ta shiga school dan ta ga alama in bata yi gaske ba da alamun ba zata tsinana komi a makarantar ba hakan ya sa ta daure ta shirya zuwa makarantan tana me mamakin me ya hana marwan kiranta har lokacin wrist watch din da ya bata birthday gift ta dakko tana kallo idonta na taruwa da hawaye a hankali ta dora a hannunta tana ji kaman ta fara zuwa gidansa ta ga ni sai kuma tayi tunanin kewan zai yi mata yawa zama tayi a kan kujeran karatunta tana kara gwada kiransa daga tafiyarsa zuwa yau ta kirasa yafi karfin sao dari biyar amma sam layin baya zuwa.

Kamar kullum layinsa was switch off kifa kanta tayi a jikin table tana kuka kafin da kyar ta lallashi kanta ta mike tare da kintsawa ta fita.

School ta wuce direct tana calculation ya kamata ta je groceries shopping cos she ran out of many things tunowa tayi da kafin marwan ya tafi yayi yayi suje shopping taki saboda bata son abinda zai nesantata dashi a wannan lokutan,she cherished every second they spent together.

Bus ta bi da zai kaita sch ko da ta fito da wayanta dan ta kara duba kiran marwan babu ko daya whatsapp dinta ta shiga sai taga bata da message ko daya da yake ita ba ma gwanar chat bace haka ta zaune zuciyarta cike da tunanin ko lafiya marwan yake a haka har ta isa makaranta.

A nitse take tafiya har ta shiga cikin makaranta, da wani yaro da bata gane ba a cikin makarantan ta fara cin karo inda ya kashe mata ido tare da fadin "hey sexy" tattare giranta tayi da mamaki amma bata ce komi ba ta cigaba da tafiya abin mamaki ko ina ta wuce kowa kallonta yake yi ana magana kus kus kus tare da nunata ita dai ta san babu abin nunawa ajikinta shi yasa tayi kokarin ganin abin be dameta ba which is in possible ka ga ana nuna ka baka muzanta ba.

Balarabiyar ajinsu da suke dan magana sama sama ne ta ja ta zuwa wani lungu cike da damuwa take kallon fuskar maimunatu yayin da ita ma maimunatun take kallonta da alamun tambaya.

Hannu balarabiyar me suna jalila ta sa aljuhun rigarta ta fito da wayarta da wani flayer dan danne danne tayi sannan ta nuna mata screen din wayar dammm gaban maimunatu ya fadi ganin hotonta a tsirara ta tubke gashin kanta kadan hoton an rubuta _feeling stressed? Call me and i will relief you_ kuma an tura da number dinta kwace wayar tayi a hannun jalila tana kara kallon hoton tabbas fuskanta ne amma ba jikinta bane saboda bata mallaki wadannan kananan nonuwan ba amma babu wanda zai ce ba ita bace duk da an samo sirirriya kamanta sannan yanzu an san yan mata da iya ciko so ko wanda ya santa ne in ba wanda ya sna jikinta ba ba zai ce ba ita bace.

Nan da nan hawaye ya cika idonta ta shiga uku,ba tare da jalila ta ansa wayar ba ta fita daga cikin platform dinsu na makaranta ta shiga wajen status ta veiwing status din maimunatu inda hotuna similar to wanda maimunatun ta gani suka bayyana da write up irin wancan sannan ta presenting mata flayer ta kuma shaida mata yana nan like ta ko ina cikin campus.

Hannu maimunatu ta saka cikin jakarta ta fito da wayarta tana fadawa jalilan "this is not me i swear to you! Wallahi this is not me." Cike da tausayawa jalila ke kallonta tana gyada kai

Ga mamakinsu duk abinda suka gani a wayan jalila yana story din maimunatun,wurgi tayi glasses din da take sanye dashi jikinta na rawa tana ta faman yiwa jalila rantsuwa da hausa tana cewa ni dai bani bace ni dai bani bace ni wallahi dai bani bace i swear to you."

Rungumota jalilan tayi ganin tana shirin fita hayyacin ta duk da ko da ta ga hotunan ta san ba ita bace amma yanayin da ta kara ganin ta shiga daga ganin hotunan ya kara tabbatar mata ba ita din bace ta yaya za ta sanar da ita a wannan halin hukumar makaranta na son ganinta?.

Kafin jalila ta yanke hukuncin yanda za ta yi da ita wayarta ta fara kara alamun kira, raba jikinta tayi da na jalila dan ta duba me kiranta zaro ido tayi tare da dafe bakinta

KINA RAINAWhere stories live. Discover now