page 41

2.1K 251 75
                                    

💖KINA RAINA💖










By Sawwama A.









Wattpad @sawwama14








Page 41.








Kallon kallo suka tsaya yi jijiyoyin kansa kaman zasu ballo su rabu da kan tsaban yanda suka tashi,idanunsa sunyi jazir alaman tashin hankali ko b'acin rai hakoransa kam ba dan Allah yayi su da karfi ba da tuni sun tarwatse saboda irin yadda ya datse su hannunsa na dunkule a gefensa.
Hadiyar yawu maimunatu tayi ta kau da kai tana kame kame ta sani a halin da yake cikin nan babu abinda ba zai iya yi ba.

Abu d'aya ta sani ba zai tab'a bugunta ba marwan na da zuciya da fushi amma ba mai bugun mace  bane, ganin tsayuwar tasu tayi yawa bai iya kuma furta mata kanzil sannan ita ta amayar da nata ya sa ta juya dan ta bar shi ya digesting abubuwan
Har ta kai kofa ta juyo tace "and kar ka yi gigin zuwa ga Tahir a wannan halin and course a scene, kanka zaka tonawa asiri ba shi ba dan tonuwar asirin mubeena naka ne." Daga haka ta saka kai ta fice ta barshi a tsaye yana shirin fashewa.

A hankali a hankali ya dinga jan numfashi yana sakewa tare da kama addu'a a bakinsa a hankali ya saki dunkule hannunsa da yayi tare da jan numfashi me tsaawo ya saki. Wuri ya samu a inda yake tsaye ya zauna ya tankwashe kafarsa tare da tallafo kansa cikin hannayensa kuka yake so yayi ko zai ji dadi amma sam babu alamun kukan sai wani yaji da radadi da yaji idanunsa na yi zuciyarsa na kuna.

A hankali yake taryo maganganun maimunatu kap ya sani babu karya a cikin abinda tace shine shine silar abinda ya samu mubeena shi ya janyo komi shi ya bata komi mami ta sha gaya mishi "marwan kar abinda kake yiwa diyoyin wasu ya fada akan kannenka ka sani kanne mata gareka kar ayoyin Allah ya tabbata akansu. Ko dan su ba zaka tuba ka daina wannan mummunar d'abi'ar?"  Bude tafukan hannunsa yayi ya saka fuskarsa a ciki a wancan lokacin yana kafa hujja da shi baya bin mace sai dai ta bishi shi babu wacce ya taba yiwa dole. Cikin wata iriyar murya yace "autar mu,auta i am sorry na zalunceki na dade rabon da in kwanta da wata diya mace amma laifina na baya ya fada akanki auta dole miemie ta kyamaceni,ni din abin kyama ne ni din kazanta ne Allah na tuba Allah na tuba kar ka saukar da wannan masifan kan zuriyata da ban haifa ba kar halina ya shafi diyoyin da basu ji ba basu gani ba."

Ganin zaman da surutan ba zai mishi ba ya sa ya mike ya shiga suite dinsa na office din tare da kullowa bathroom ya fada ya dora alawla sam tunkarar Tahir a halin yanzu baya cikin lissafinsa dan ya san ana iya dauresa dan kam sai ya kaishi har lahira.

Maimunatu kam tafiya kawai take yi tana hada hanya ranan yau ta zo mata a dabaibaye tana isa office dinta ta tattara duk wani abu da ya shafeta ta kwasheshi tas dan ta kudurta a ranta ita kam daga yau ta gama service dinta dan dama ai saura kadan,tana aikinta cikin jin dadi da kwanciyar hankali har tana considering aiki a Moh enterprises amma zuwan marwan ya ruguza komi tunda ya zo take cikin tashin hankali matsalan yau daban na gobe daban.

Da wannan tunanin ta kwashe duk wani abu nata ta bar companyn kirar Tahir ne ya shigo wayarta tsaki taja tana mamakin mask din da ya sawa fuskarsa da ya iso gareta ko da wasa bai taba gigin ko taba mata hannu ba ashe kura ce da rigar akuya fuska biyu gareshi shi yasa yake bin duk wata hanya da mubeena ba zata sani ba dan gudun tonuwar asirinsa taji tsoron maza har gwara marwan bai boye mata shi wanene ba ya fito mata da halinsa Tahir kam kungurmin munafuki ne wato maza dai duk haka suke ita kam yanzu bata san wa zata trusting ba har khalid sai lokacin ma ta tunoshi dan tun ana gobe daurin auransa rabon da ya kirata dan dama ita tun da maganar auransa ya bayyana ta daina kiransa ranan auransa ma text ta mishi na tayashi murna ya aiko mata da kalmar godiya.

Duk da halin da take ciki na dacin rai bai hanata murmusawa ba ina kuwa zata ga kiran khalid yana da sabuwar amarya ai kuma sai mai ya bar kan kaza kafin ya waiwayeta.

KINA RAINAWhere stories live. Discover now